Chapter 94
Chapter 94
kuma da ita had’a y’an kud’ad’en hannunta ta sake turawa Umma a san abunyi ta auri Arshaad ko ta halin yaya ne da wurwuri cikin gaggawa! Itafa wallahi yadda ta d’and’ana daular nan to kuwa batajin zata iya minti uku a cikin gidan Baba!…. Tanata sak’e sak’e a ranta a haka suka iso gida! Sai wani nonnok’ewa take yi gudun abunda Mom zata yi mata, amman suna shiga sai taji Mom d’in tace mata “ta tafi d’akinta ta huta Coook zata kawo mata abinci yanzu.” A hankali tace “Na gode Mom” Wani kalan murmushi Mom d’in tayi wanda Jalilan ta kasa ganewa.’Daganan Mom d’in ta juya ta nufi hanyar kitchen a ranta tace “Yarinya kenan! Sarai na san zaki iya yi mana bori, kice ba zaki tafi ba ki tada mana hankali Kuma ko yanzu na san idan akai test a jikinki positive za a gani.. Ki jira nan da kwana uku In sha Allah za ki san wacece Adama.” GANDUN ALBASA Tun da garin Allah ya waye Huda take kuka Idan zaka titsiyeta ka tambayeta ba zata tab’a iya gaya maka menene tak’amemen abinda ya sanya ta kukan ba! Ita dai ta san bata da nutsuwa sannan a mugun tsorace take amman tabbas ba wai shariyar Arshaad kad’ai ne dalilin tashin hankalinta ba. Sakina da Khadija sun yi lallashin sun yi har sun gaji sun rabu da ita. Hankalinta bai sake tashi ba sai da k’awayenta suka zo sannan mai makeup itama ta zo ta fara shiryata! Tayi alk’awarin ba zata sake kiran Arshaad ba amman haka ta daure ta kirashi wannan karan kam a kashe ma taji wayar tashi gaba d’aya dan haka hankalinta ya sake tashi! Ba abunda yafi d’aga mata hankali irin kar azo d’aurin aure yace ya fasa! Ita gara ya fito ya fad’a mata gaskiya akan yayi mata hakan... Nasarawa gra. A b’angaren Arshaad kuwa jiya ya gama shirya plan d’inshi amman ga mamakinshi kamar wani ya gayawa Mammy bayan Magrib nayi ta shigo d’akin nashi ta kafa ta tsare! K’arshema a d’akin a kan couch ta kwana tsabar bala’i. Tun jiyan da ta shigo har yanzu k’arfe 10 bata fita ba! Ko wanka ko brush bata yi ba, har gara ma shi yanata watsa ruwa saboda zazzab’in da yake jikinshi.. Yana lura da ita ko mik’ewa yayi ya shiga shiga toilet zai yi wanka ko alwalla sai taje bakin k’ofar ta lab’e mishi har sai ya fito sai kace wani wanda akace mata zai b’ace! Dagashi har ita ba wanda ya samu bacci jiya Idan ka gansu duk a gigice. Ko da Aaima ta kawo musu breakfast ma ba wanda ya tab’a har yanzunnan Tun jiyan da ta shigo har yanzu ba wanda ya cewa wani uffan a tsakaninsu. Amman duk wani motsinshi idanunta na akanshi. Ba abunda yafi d’aga mishi hankali kuma ya bashi mamaki irin yanda ta kasa tashi ko sallah tayi Yanzu haka yana lura da yadda ta kasa zama mai kyau sai faman mutsu mutsu take yi wanda ya tabbatar fitsari take ji amman gudun kar ta shiga ya gudu ta gwammace ta zauna a haka!. Suna a haka Dad ya shigo cikin d’akin. Yayi mamamkin ganinta a zaune amman sai ya d’auke kai kawai ya maida hankalinshi ga Arshaad, ransa a d’an b’ace yace “Ka san fa k’arfe 11:30pm ne d’aurin auren, uban me kake yi a zaune a haka?” A hankali yace “Ina kwana Dad” “Lafiya” kawai yace masa, daga nan ya nemi waje ya zauna kafin yace “Mik’e maza, yanzun nan Aslam zai kawo maka kayanka” A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yanayin k’asa k’asa yana kallon Mammy wadda ta d’auke kai tana kallon gefe. Mik’ewa yayi jikinshi ba kwari ya fad’a band’aki! Ya kai kusan 20 minutes tukunna ya fito sanye da bathrobe a d’akin ya tarar da Aslam sanye cikin sky blue d’in rantsattsiyar shadda aikin gaban rigar white da d’an ratsin blue ya murza farar hula mai asalin kyau da tsada sai kyalli take yi da farin takalmi hatta agogon hannunshi white ne. Yana rik’e da babbar rigarshi a hannu wadda take a ninke, k’amshinsa gaba d’aya ya cika ilahirin d’akin…. Suna had’a ido ya sakar mishi murmushi a hankali yace “Ango” Murmushi shima Arshaad d’in yayi sannan ya wuce jikin wardrobe d’inshi ya na mamakin ta yanda zai shirya a gaban waennnan body guards d’in! Inner wears d’inshi ya kwasa ya d’auki jakar kayan da yaga an ajjiye akan gadon ya juya ya wuce toilet. Bai yi minti biyar cikakku ba ya fito! Murmushi Dad yayi yana kallon shi yana mai jin wani sanyi a ranshi! Kana ganinshi kaga Ango.. A hankali jikinshi a mugun sanyaye ya k’arasa gaban mirror ya d’an shafa mai sama sama a hannu da fuskar shi sannan da k’afa, ya fesa perfumes ya d’auko takalmin da ya fito da shi a jakar kayan nashi ya sanya… Farar shadda ce k’all! Mai babbar riga sai bak’in takalmi hula da agogo.. Yana gyara d’aurin agogon suka ji knocking Aslam ne ya juya ya d’an bud’e k’ofar dake a kusanta yake. Da mamaki yake kallon Abba da Daddy da Auwal a bayansu. Dad Abba da Daddy duk ankon shadda ruwan goro light suka yi, aikin rigar ciki da babbar rigarsu kuma na kalar kayan amman dark sosai Sai hulunansu zannah bukar d’in da suka amsa sunansu ZANNAH bukar! Amman kowa da design d’inshi, takalmansu kuma na fata kalar ruwan goro masu mugun kyau da tsada iri d’aya. Yayinda Auwal ke sanye da maroon shadda shima ya murza zannah bukar d’inshi mai asalin kyau da tsada. Cikin girmamawa Aslam ya gaida su Abba Daddy ne yayi dariya yace “Kaga yau har da mu a y’an sneaking a shigo estate ko?” Murmushi kawai Aslam d’in yayi. Kallonshi kawai Abba yake yi… Ya manta when last da ya ganshi da manya kaya, ba k’aramin kyau yayi ba, har ga Allah Aslam ba wai favorite d’in Granpa bane kad’ai Har da shima Aslam ne favorite d’inshi! Kawai dai shi d’in baya nunawa ne Yaron akwai hankali da nutsuwa da sanin ya kamata “Ina ma inama! How i wish......” Ya fad’i hakan a ranshi sai kuma yayi saurin kawar da tunanin ya juya suka fara gaisawa da Dad. Daga shi har Daddy ba wanda ya kalli ko inda Mammy take Kuma sarai sun ganta dan har had’a ido suka yi da Abba! Hakan kuwa ba k’aramin sake ingizata yayi ba Tabbas yau sai ta nuna musu ta isa wallahi! Chap!! Arshaad ya shirya dan haka suma duk suka mik’e dan har an fara jera musu kira Abokanan su sun fara zxuwa venue d’in.. Ba tare da Mammy ta motsa ba tace “Arshaad!” Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna ya juyo yace “Na’am Mammy” Mik’ewa tayi tsaye tace “Koma ka zauna” Sannan ta dubi su Dad waenda suke kallonta gaba d’ayansu tace “Kuna iya wucewa ku tafi! D’a dai ni na haifa ko? To wallahi tallahi ba wanda ya isa ya yi mini iko da shi! Da kuka shigo kuka wani banzatar dani kamar baku ga mutum ba saboda ban kai ba har kai Abba! Kalla Auwal shima Aslam ne kawai ya gaidani ya kulani a kaff d’inku saboda ka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96