Chapter 39
Chapter 39
addu’ar a shafa mata . Suna fita Abba ma yace mata “ta d’auko hijabinta ya kaita ta duba Mama” Murna a wajen Hudan ba a magana dan da gudu ta haye benayen, bata yi minti uku a saman ba ta sauk’o sanye da hijab har k’asa wanda ta gani a cikin kayan da aka bata. Ya lura da yadda jikinta har karkarwa yake yi, shiyasa bai b’ata mata lokaci ba yace “suje”. Da sassarfa ta shige motar. Shi dai Abba kallonta kawai yake yi, tabbas Hudan da shi take kama komai da komai amma idan tana wani abun sai ya dinga ganinta kamar Maryam!!! Wani d’an murmushi ne ya sub’uce mishi, a hankali cikin sanyin jiki ya murza key ya tada motar ya nufi gate. Masu gadin gidanjensu na chan estate su suka d’auko suka taho dasu.. Suna Isa gate d’ayan ya ajjiye rediyonshi a kan dogon bencin da suke zaune su wajen biyar harda driver da mai wankinsu da gyaran fulawar, yaje ya bud’e musu makeken gate d’in, suka fice. Tunda suka fita Huda ta kasa sukuni, tsabar zumud’i, gani takeyi kamar Abba baya gudu, har d’an tasowa take yi ta d’an lek’a gaban titin ta gaban glass d’in motar.. Dariya ta bashi sosai dan haka yace “Gani kike kamar bana gudu ko?” Ya fad’a yana dariya sannan ya k’arawa motar wuta… Itama murmurshin tayi ta koma ta zauna da kyau a mazaunin ta. Tafiyar minti ashirin ce ta kaisu AKTH emergency, dan ma sun d’an tarar da go slow a hanya. Tana shirin fita taji yace “You promised Hudan, right?” A hankali ta d’aga mishi kai, sannan tace “Na gode sosai Abba” sannan ta fita. Da kyar security suka barta ta shiga bayan tayi ta nacin ce mishi Mamanta ne a kwance, Allah ya taimaketa, wanda yake gadi ne a wajen ranar da suka kawota ita da Aslam, kuma d’azu tabbas yaga Maman nata an fito da ita tana d’an zagaye, shiyasa ma ya barta ta shiga, don ya tunata tun ranar da suka zo ita tana kuka shi kuma yanata mamakin had’uwar Yarinyar, hakanan yaketa ganin hoton fuskarta a zuciyarshi amman ya san ko hauka yake ba zai ma yi tunanin tunkarar ta ba. Dube dube ta hau yi bayan ta shiga, da kyar da sid’in goshi ta hango su… Mama da Ummu a kan gadon a zaune suna magana da alamun mai matuk’ar mahimmanci ce sai Sakina ita kuma a gefe kan kujerar mai jinya da waya a hannunta. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 41 Basu ga tahowarta ba, kawai suka ga an afka kan Mama da gudu an rungumeta! Kukan da ta fashe dashi ne yasa suka gane itance, da sauri Sakina ta d’ago ta, ai kuwa tana ganinta tayi hugging d’inta tana dariya. Ummu itama murna kamar tayi me, Mama kuwa ba a magana. Ummu ce ta zare Hudan daga jikin Sakina sannan ta d’an muskuta ta ajjiyeta a tsakiyar su ita da Mama. A hankali Mama tasa hannu ta shafa fuskarta tana hawaye, da sauri itama Hudan ta goge mata hawayen tace “ki bar kuka Mama, i missed you so much, kwana biyun nan ji nayi kamar shekara wallahi” Ta fad’a tana sakin wani kukan, sannan ta kwanta jikin Mama. Sakina ce ta d’aka mata duka a cinya kafin tace “dalla Malama d’agata, kin wani zo sai kuka kike yiwa mutane salon ki karya mana zuciya muma mu biye ki! To Mama dai ance a daina sakata a damuwa dan haka sai kiyi k’ok’arin tashi ki ware garau ki bar wannan tab’arar.” Da sauri ta d’ago tana goge hawayen da suka k’i tsayawa, da kyar kuwa ta tsaidasu, ta d’an harari Sakina tana murmushi sannan juya tace “ina wuni Mama, ya jikin ki?” Da murmushi Maman tace “Alhamdulillah” Sannan Huda ta juya ta gaida Ummu, wadda itama ta amsa mata cikin kulawa sannan tace “ya mutanen gidan naku?” A hankali Huda tayi k’asa da kanta tace “Alhamdulillah” Sakina ce tace “a estate d’in kike? Family house d’in nasu kamar estate ne kowa da kowa ko?” Numfashi Hudan ta fesar tukun tace “Eh, nan aka kaini da farko, amman yanzu dani da Abba da Daddy da Ya Auwal mun tashi mun koma wani gida a baya. Saboda Granpa yace ‘Abba sai dai ya zab’a, ko ni ko su!’.” Cikin mutuwar jiki Sakina tace “Shine ya zab’e ki kuka tashi?” Da “eh” ta amsa, kafin tace “Har da d’an uwanshi ‘Daddy’ shima muka tashi, sun yi fad’a sosai jiya da Granpa d’in.” Tana shirin sake yin magana Mama tace “Kuka tashi as in how?? To ai yayi ta banza ne, dan ke kam kin zo kenan!! Ya aka yi kika fito? D’azu su Kaka suke gaya mana kalar rashin kunyar da yayi musu ai! Yanzu haka takardun shiga kotu ake had’awa!…” Cikin rashin jin dad’i Ummu tace “Mama dan Allah ki daina biyewa su Abba Modu kina k’ara tunzurasu! Kina ji fa bawan Allahn nan har gidansu ya bari, saboda ita!. Ko fa anje kotun nan na fad’a miki bamu da nasara saboda kamar yadda Abba Madun yace d’an uwanshi( Daddy) ya fad’a musu d’azu ‘ko a iya case d’in Baba aka tsaya dole a bashi Hudan!!’ Ballantana kuma idan aka duba yanayin standard of living! Shi (Abba) yana da aikin da zai iya kula da ita ke kuma.....” Shiru Ummu tayi ta kasa k’arasawa ganin yanda Maman ta kafeta da idanuwa. Cikin jan numfashi Maman tace “Ki k’arasa mana! Ni kuma bani da aikin yi, bani da komai ko?.” Sai kuma tace “Bari kiji idan su sun yi amfani da Baba to ni kuma zan yi musu amfani da Granpa! Ai har gara Baba shi bai tab’a korar Huda a gidanshiba, Granpa fa?” Cikin katseta Ummu tace “Amman ai yanzu ko me Granpa yake ji dashi bai isa yayi mata ba! Saboda Abban ma ya d’auketa a kusan shi gaba d’aya! Dan haka Kotu ba zata duba wannan bama a matsayin reliable.” Cikin d’an fad’a Mama tace “Wai Ummu kina nufin in barta kenan a wajenshi ko me kike son gaya min?” Cikin kwantar da murya Ummu tace “ba nufi na kenan ba, ki fahimceni Dan Allah… Maganar shiga kotun ne bana so saboda idan anje mune za muji kunya! Kuma In dai Abba yaga anbashi custody d’inta gaba d’aya to fa ba lalle ya dinga barinta tana zuwa mana ba! Mama, Hudan y’a mace ce! Makaranta ma zata shiga yanzu university wanda idan kika kwantar da hankalinki ma wata rana a wajenki za tayi Hutun ta! A hankali a hanakali zakiga zata iya dawowa wajenki gaba d’aya wata rana. Abunda nake so dake shine yanzu ki barshi (Abba) Zafin zuciya ne kawai yake damunshi.. Ni a nawa ganin banga amfanin a shiga kotu anata kace nace ba k’arshe kuma na san mu ne da kunya!. Kuma Hudan aure zata yi nan ba da dad’ewa ba, daga k’arshe fa dole ta bar gabanku gaba d’aya daga ke har shi. Dan Allah Mama ki fahimceni ki tayani fahimtar da su Kaka.” Cikin tsananin b’acin rai Maman tace “Eh!! Ai shiyasa ya turo mata da Arshaad, kuma abunda basu saniba na riga na gama yanke hukunci ‘In shi kad’ai ne Namiji a duniya to
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96