Chapter 47
Chapter 47
tace “gaskiya wajen nan ya burgeni Huda, over!! Ina tunanin had’uwar parlourn ashe bedroom d’in har ya fishi? “ Murmushi Hudan tayi tace “Ni kuma duk toilet d’in yafi burgeni” da sauri Sakina tace “muje In gani” ta fad’a tana cire hijab d’in jikinta dake nan har k’asa. Suna shiga nan itama tace “gaskiya kam toilet d’in duk yafi had’uwa” Haka nan suka taru suka dinga hauka, daga su kunna wannan sai su kashe wannan, wani abun ma ba iyawa suka yi ba da karambani suka koya. Babu abunda yafi burge Sakina irin closet dan haka ta fito wajen tana kuma setawa Hudan zaman kayanta kafin ta fito a wanka. Bata wani dad’e ba ta fito a wankan tana fitowa tace “itama ta shiga tayi wanka sai ta chanja kayan jikinta, lace d’in zai yi mata nauyi dan garin ana zafi sosai” Murmushi Sakina tayi kafin tace “Ni fa daga ni sai hand bag d’ina nazo, Ummu daa hanani zuwa tayi fa, sai da Baba ya bud’e mata wuta!Amman tace wai gobe da safe in dawo, har na d’auko kaya set uku tace wai In na tafi da kaya ba zan dawo da wuri ba! Shi kuma Baba yace tunda Abba ne da kansa ya rok’esa to sai lokacin da kika saba da nan d’in tukunna zan koma!. Wallahi tun d’azu jikina a sanyaye yake, Mama ma bata san na taho ba, dan Ummu tace bata san da wanne ido zata kalle ta ta fad’a mata ba! Shinema dalilinta na hanani zuwa tun farko daman.” Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e kafin tace “Ranar dana tafi ya aka yi? Ina ta kiran Ummu bata d’auka.” “Hmm.. Mama ce ta rikita kowa wai Abba ya aiko an sace ki! Amman har yanzu a haka su Ummu suka barta basu gaya mata ke kika tafi da kannki ba saboda kar taji haushinmu, kawai dai ance mata kina nan d’in so ta kwantar da hankalinta tunda kina wajen Mahaifinki ne ba wani mugun hannu ba.” Hawaye Hudan ta goge kafin tace “Sakina wallahi ni ban san ya zan yi ba” ta fad’a tana fashewa da kuka, rungumeta Sakina tayi kafin tace “wallahi Huda ni kaina abun nan yana daure min kai, sai ka rasa ina zaka tsaya, gaba d’aya ni kaina i’m confused, ballantana kuma ke. Muyi ta addua kawai ki kwantar da hankalinki, kinji?Please”. Hawayenta ta goge jikinta duk yayi sanyi, sannan ta d’an d’aga kanta a hankali kafin ta cewa Sakinan “kije kiyi wanka sai ki sa kayana Inner wears kuma ina da sababbi suma, muyi sauri dan na san yanzu Abba zai fara kira, lokacin dinner yayi.” Hijab d’inta wanda ta ajjiye a bedroom Hudan ta fita ta d’auko ta wuce ta sa a washing machine ta fito ta bata towel, Ita ta tayata wankin dan sai da ta tayata ma shanya kayan data cire suka wanke d’in tukun ta fito ta barta dan tayi wankan. Sallah ta tarar Hudan tanayi lokacin da ta fito dan haka itama ta nemi hijab ta tayar da sallar. Sauranta izu d’aya a izu goman daya kamata tayi, dan haka ta hau karatu bayan ta idar…. Tana idarwa tayi addua ta tofa ta had’e ruwan d’azu data shigo dashi dana d’akin waje d’aya!. Da mamaki Sakina ta kalle ta kafin ta tambayeta Bayani ta hau yi mata a kan ‘na maman Aslam ne wanda ta basu labarinta….’ “Allah sarki Allah ya bata lafiya, abun tausayi wallahi” Sakinan tace. Kayan bacci dukkansu suka sanya, sai suka d’aura hijabai a sama, sannan suka sauk’a dan Abba har ya kirata kamar yanda tayi tsammani. Sai da ta lek’a d’akin su Sudais, ganin basa nan yasa suka nufi k’asan. Har Aslam suka tarar a dining d’in da Arshaad amman yanzu ya chanja kaya wanda hakan ke nuni da wanka yaje yayo. Yaji tahowa amman bai d’ago ba, dan babu abunda yake sosa mishi zuciya irin yadda ko kallon inda yake bata yi. Sai da suka k’araso tukun Abba yace “a’a inyee! Yau ga annuri a fuskar princess, duk a dalilin Sakina, irin wannan murmushi haka?!” Ya fad’a yana murmushi kafin yace “bismillah ku zauna mana” A hankali suka fara k’ok’arin jan kujera… Yana shirin d’agowa ya ga da gaske Sakinan ce jin abunda Abba yace, yaji tace “Ya Arshaad Ina wuni.” Da sauri ya d’ago, ya d’an zaro ido alamun mamaki, sai kuma ya fara murmushi yace “Lafiya, Alhamdulillah. Ashe kece da kanki! Welcome, ya gida?” “Alhamdulillah” tace kafin ta d’an turo baki tace “Ai gani nayi da farko ka wani had’e rai ko kallon inda muke ma bakayi ba” Dariya yayi kafin yace “Hankalina baya wajen ne, sorry” Itama murmushi tayi ta sake gaida Abba da Aslam wanda ya amsa ko kallonta bai yi ba! Tunda suka sauk’o ma ta lura bai ko kallesu ba… Tana ganinshi tashi d’aya ta fahimci shine Aslam. Lokacin da Hudan take zuzuta mata kyawun Aslam d’in bata yarda ba, dan har ta fara tunanin wani abun a tare da Hudan na daban, but yanzu kam tagani itama! “Tubarakallah!” Ta fad’a a k’asan ranta. Cikin nutsuwa taji Hudan suna gaisawa da Abba wanda yake zaune a opposite d’insu shi da Aslam. Da kulawa yake tambayanta hope taji dad’in ganin Sakina? Is she happy now? Taji dad’in zuwa munjibir park d’in? Ba wata damuwa ko?…… Murmushi Hudan tayi duk tana ta binshi da “Alhamdulillah komai Alhamdulillah..” Abun yayi matuk’ar burge Sakina a ranta tace “yau ina Baba da Umma suzo suga gatan da akewa Huda, suga yanda Abbanta yake janta a jiki yana lallab’a ta” Wani farin ciki ne taji ya lullub’eta, tabbas tana yiwa Hudan murna da baiyyanar Mahaifinta! Itafa sometimes ji take a ranta kamar ma tafi Hudan farin ciki. A hankali taji sun gaisa da Aslam, taga ita Hudan ta d’an samu darajar kallo a wajenshi tukunna yace “lafiya” da d’an mitsitsin bakinshi. Har an fara serving ta mintsili Huda da k’arfi ta k’asa k’asa inda ba za a gani ba. “Ouch” tace, a hankali sannan ta juyo tana kallon ta, harara Sakina ta zabga mata k’asa k’asa tace “shi ba zaki gaidashi ba???” Itama Hudan hararar ta maida mata ta cigaba da zuba abincinta! Mintsilinta Sakina ta sake yi, kafin tace “Wallahi ko ki gaisheshi ko kiyi ta karb’ar ruwan mintsili kala kala!” Dai dai nan wayar Abba tayi k’ara … Excusing kanshi yayi ya mik’e ya d’an koma gefe yana amsa wayar dan it’s a very important call ba zai yiu yayi ignoring ba. Kamar jira Sakina take, nan ta sake sakar mata wani sabon mintsinin da sai da tayi k’ara mai sauti sosai this time around har su Aslam sai da sukaji suka juyo suna kallonsu… Sudais kuma ya fara kyalkyala dariya dan shine a kusa da Sakina yana kallonta tun d’azu! Ganin da Huda tayi Sakina ba zata hak’ura ba yasa ta juya, kujera biyu ne tsakaninta da Arshaad d’in dan haka ta d’an kalleshi tace “ina wuni” Sai da ya sake tamke fuska tukun yace “Lafiya” Yanajin haushi a ranshi, wato gaisuwar ma sai ta ga dama zata yi, kuma shine na k’arshe! Har su Sudais sai da ta gama kulawa tukunna shine last! Tashi Sakina tayi daga kan kujerarta ta dawo ta gefen Hudan side
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96