Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 74

Chapter 74

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

nufi motar da ita. Suna zuwa bakin motar Arshaad yasa hannu ya bud’e seat d’in baya inda yake zaune ta gefe… Wata zazzafar suite ce a jikinshi white, hatta neck tie d’in shi white ne da takalmi, sai wani d’an kyalle da ya d’an d’aura a jikin aljihunshi na suite d’in nasa d’an mitsitsi peach..... Lokacin da yace mata kar su damu ya gama order da had’a komai kayan da za ayi using, aranta ta gama aiyyanawa ‘ba wani kyau za suyi ba’ dan tayi tunanin maza ba su iya zab’e ba amman yau kam ta tabbatar Ya Arshaad k’arshe ne wajen zab’a, had’a kaya da colours. Murmushi Sakina tayi kafin tace “Ango irin wannan kyau haka?” Dariya ya d’anyi sannan yace “Ai ban kaiki ba. K’anwar Amarya” Yana mata magana idanunshi na kan Hudan! Da kyar ma ya amsa gaisuwarta ita da k’awarta. Lura da Sakina tayi hankalinshi baya kansu yasa ta saka mishi Hudan a motar ta rufe a ranta tace “Gata nan ai sai ka cinyeta da kallo” Tana d’an murmushi. Ba dan hancinta ya jiyo mata k’amshin turaren Auwal ba da ba abunda zai hanata afkawa kanshi In ta tashi juyowa domin barin wajen. A hankali ta d’an juyo jin k’amshi da mutum a bayanta daff! Suna had’a ido kuwa ta zabga masa wata uwar harara.. A wajen k’anwar Ashraff kawai ya samu gaisuwa, bai damu ba ya amsa ta kafin ya juya ga Sakina yace “Kin yi kyau over!” Yad’an yi mata alamar perfect da hannunshi yana murmushi.. White suite ce shima a jikinshi da d’an ratsin black, yayi masifar yin kyau sai dai askin sa da yayi yau d’in ne ya b’ata mata rai. Hannu yasa ya bud’e gaban motar, kafin yace “Bismillah” yana kallonta still da murmushi akan kyakkyawar fuskarshi. A hankali ta d’auke idanunta daga kanshi, daman tun d’azu da ta sunkuya suna magana da Arshaad ta ganshi zaune a mazaunin driver! A tunaninshi zata yarda ta zauna kusa dashi kenan, tab! Ai ko hauka take ba zata yarda ta zauna kusa da shi ba ita da take k’ok’arin ganin ta kauce mishi ta kowacce hanya, besides Ashraff ma yana jiranta tare za su tafi..’ Da wannan tunanin ta kamo hannun k’anwar Ashraff ta saka ta a cikin gaban motar ta rufe, ta yi gaba abunta. Guiwa a sace Auwal ya bita da kallo har ta isa inda motar Ashraff d’in take a chan gefe bama a cikin convoy d’in nasu ba, ta shiga. Da kyar ya iya dedeta kanshi ya juya yaje ya shiga ya kunna motar dan har an fara yin gaba... Suna isa inda za ayi event d’in ya bud’e motar shi ya fito. Sai hotuna ake d’auka amman shi bai damu ba, neman ta kawai yake yi.. Ganin ba ita ba dalilin ta yasa ya zaro waya ya hau kiranta! Kowacce mota ta k’araso, har ta masu d’aukar hoto amman tasu bata iso ba.. Arshaad ne ya d’an kira sunan shi dan haka ya juya, da hannu Arshaad d’in ya yafito shi, yana zuwa yace “Ana ta hoto babu kai, me kake nema?” D’an murmushi kawai yayi ya tsaya aka yi musu, daga nan aka fara k’ok’arin shiga hall d’in. K’awayen Amarya, a baya Abokan Ango a gaba Auwal da Jamil su ne daf da Ango da Amarya dan sune suka saka suit kamar Angon ragowar mazan kowa kayan shi ya saka. Shi dai Auwal har aka shiga bashi da nutsuwa dan haka Amarya tana zama ya juya ya fita yana mai cewa Jamil yayi jawabin da da shine zai yi, yana da uzuri. Arshaad bai yi mamakin rashin ganin Aaima da Aslam a wajen ba! Amman tabbas ranshi ya sosu, baya son b’ata wannan ranar ta musannan dan haka ya kawai sai ya basar ya ci gaba da huld’ar gabanshi. Tsarin wajen ba k’aramin had’uwa yayi ba Tebur da kujeru uku a zagaye wajen guda ashirin! Sai chan wajen sit d’in Amarya da Ango gefen dama da hagun su kuma akwai kujeru goma goma da dogon tebur a lamun nan ne wajen zaman best friends dan har ma sunje sun zazzauna matan masu anko mazan kuma waenda suka zo tare. Kwata kwata friends d’insu da suka tarar a wajen ba sufi ashirin ba! Cool music ke tashi ba wani hayaniya.. Cocktail ne da cake da sweet da hot chocolate da kuma menu mai d’auke da abubuwa daban daban akan tebur d’in, sai waiters a gefen tebles d’in a tsattsaye su wajen 30 da uniform, duk abinda kake buk’ata sai ka kira ka gaya musu a menu d’in aje a kawo maka In ka gama su d’auke. After kamar 20 minutes da fitar Auwal, motar su Sakina ta shigo wajen.. Ranshi a mugun b’ace ya k’arasa inda motar take! Bai yi wata wata ba yasa hannu ya bud’e side d’inta ya kamo hannunta ya fito da ita. Da kyar ta iya tsayawa ta gyara mayafinta wanda yake k’ok’arin zamewa… Ko lura da guy d’in da ya fito shima ya zagayo inda suke Auwal d’in bai yi ba ya fara magana “Ina kuka tsaya?? Kin san mintunku nawa kuwa? Almost 30 minutes kowa ya k’araso banda ku, Ina kuka biya haka?” Ya k’arashe maganar cikin tsananin b’acin rai, kamar wani ubanta… Kallon shi take yi kawai. Sai da ta barshi ya kai aya tukun ta fara k’ok’arin wuceshi ba tare da tace uffan ba!. Tafarfasar da zuciyarshi keyi ba kad’an bane dan haka cikin zafin nama ya sake sa hannu ya fincikota ya dawo da ita unintentionally ta bugu da jikin motar. Da sauri Ashraff ya k’araso inda suke ya juyo da shi ya cukumi wuyan rigar shi! Cikin tsananin b’acin rai yace “Meye ne matsalar ka? Who the hell are you? A iya sani na bata da yaya! Ka fito kawai ka fara yiwa mutane hauka.. Ka godewa Allah ni ba mahaukaci bane Irin ka dan wallahi da sai na gyara maka zama a wajen nan!” Ya k’arashe maganar yana sakin mishi kwala da k’arfi. Auwal ya taso kenan yana shirin yin magana a zafafe Idanuwansa suka sauk’a kan Sakina wadda ta fara hawaye. A take yaji duk jikinshi yayi sanyi… Tun lokacin da ya tura ta jikin mota har yanzu bata motsa ba tana a yanda take sai dai hawayen da ita kanta ta rasa na menene waenda suke zuba akan k’uncinta. Kamar an tsoma shi a ruwan sanyi haka yaji, ya kasa motsawa zuciyarsa na dukan uku uku, gashi tak’i yarda ta kalli inda yake. A hankali Ashraff ya k’arasa inda take ya fara yi mata maganar da Auwal d’in baya jin me yake cewa. Goge hawayenta tayi ta gyara tsayuwarta. Sannan Ashraff d’in ya bud’e bayan motar ya d’auko k’aton cake d’in da suka tsaya karb’a. Daganan suka zo suka wuce shi ba tare da sun ce mishi komai ba!. Sam ya kasa motsi ya kasa yin komai. Kawai iya hawayen da ya gani daga idonta ne ya kashe mishi guiwa ya sanyaya mishi jiki. Yafi 10 minutes a wajen kafin da kyar ya samu ya wuce ciki, yana zuwa ya nemi waje ya zauna.. Ba abunda ya iya ci a wajen yana nan zaune a wajen shi kad’ai amman dukkannin hankalinshi na a kan

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});