Chapter 69
Chapter 69
A parlour ya ga Aaima ita kad’ai tana shan tea akan dining, har zai wuce ta kawai, sai kuma duk yaji ba dad’i tausayinta ya lullub’e shi, dan haka ya koma ya ja kujerar kusa da ita ya zauna. Bata ce mishi komai ba ta ci gaba da kurb’an tea d’inta. Sai da ya zauna tukun ya fahimci ashe kuka take yi! Dafe kanshi yayi ya furzar da iska kafin yace “Ok, I’m sorry! Kin b’ata min rain ne d’azu sosai Aaima.. Ba zai yiu ki tsani Hudan haka ba! Za a samu matsala..Hudan ta zame miki dole! Ki ajjiye duk issues d’inku da ita aside, ki manta ki yafe She’s about to become my wife! Kar ki zama silar rusa zumunci da raba kan y’ay’anmu da naki in the future..” Murmushin takaici Aaima tayi ta ajjiye cup d’in hannunta kafin tace “Do you know what the funny thing Is?” Bata jira jin mai zai ce ba, tace “Ya Arshaad ban ma san za ka yi aure ba! So i think ba ni ce zan zama silar raba zumunci ba! Kai ne! Infact ka riga ma ka raba dan wallahi ba k’aramin haushi na ji ba ba zan b’oye maka ba Iya wannan banzatar dani d’in da kayi ya isa zumunci ya samu tangard’a!” Cikin son fahimtar da ita yace “Aaima, an saka date d’in a k’urarren lokaci I have a lot to discuss with you, inaso In ganar dake abubuwa da dama kafin In sanar dake shiyasa kika ga ban fad’a miki ba! Issues d’in are all tied up In na gaya miki zan yi aure dole za ki buk’aci Mammy! anan ne kuma za a samu case, na sani. But I was planning inje in d’auko ki a week b4 daga nan in miki bayani ta yanda zamu fi fahimtar juna.. Mu uku ne kawai Aaima kece mace dan Allah kar ki fara irin haka tun yanzu, please..” Ajiyar zuciya ta sauk’e, kafin ta kalleshi eye to eye, babu alamun wasa ko tsoro tace “Wallahi!! Muddin Hudan zaka aura to tsakanin mu ba zai yi kyau ba!.” Tana gama fad’in hakan ta mik’e ta bar mishi wajen a fusace… Sai da ta kai stairs tukunna ta juyo tace “Ya Aslam bashi da lafiya, Yana side d’insu ana k’ara masa ruwa. Kaje ka kula da shi pls, shi kad’ai ne, ni kuma yak’i yarda In zauna da shi, sai amai yake yi.” Har tayi gaba kuma sai ta sake juyowa tace “If Hudan permits.” Bata sake juyowa ba tayi sama abunta. Ya dade a wajen, tukun ya mik’e ya je ya watsa ruwa ya sa pyjamas ya nufi gidan su Aslam d’in: Direct d’akin sa ya wuce bayan ya bawa Gwaggo Asabe ruwan adduar. Akan gado ya ga cannula da bandage da alamun wadda aka saka mishi ce ya cire! Yana shirin fara neman shi ya jiyo shi a toilet yanata shek’a amai. Toilet d’in ya nufa ya tura k’ofar ya shiga.. Sai da gabanshi ya fad’i ganin yanda duk Aslam d’in ya fita daga haiyyacinshi cikin wuni guda tak!. Taimaka mishi yayi suka fito bayan ya yi brush ya wanke fuskarshi. Yana kwantar da shi ya d’auki waya ya kira Doc.. Bayan ya ajjiye wayar, cikin sanyin murya yaji Aslam d’in yace “Yanzu fa Doc d’in ya tafi, wanne kuma ka kira?” Banza Arshaad yayi da shi kawai yaci gaba da had’a mishi tea d’in da ya fara. After kamar 20min haka, Doc d’in suka shigo tare da Gwaggo Asabe…. Sai da ta sa baki tukunna ya yarda ya tsaya aka sake duba shi, dan shi already ya riga ya san me yake damunshi tun kafin zuwan first Doc d’in kuma baya so Arshaad d’in ya sani… Ba yadda ya iya shiyasa kawai ya kyalesu, bayan y’an gwaje gwaje Doc d’in ya tabbatar musu da ‘jininshi ne ya hau sai kuma fever mai zafi da ta ke damunshi.’ Gwaggo Asabe har da kukanta take ce mishi “Jikin Mommyn fa yanzu da sauk’i Alhamdulillah Gashi kusan satinshi biyun a gidan amman shiru bata yi komai ba! Ta warke sosai fa, ita abun har mamaki ma yake bata, amman in ta tuna yadda aka duk’ufa akan neman lafiyarta ta hanyar kad’aita Allah shi kad’ai da taimakon ayoyin shi, sai ta ga ba abun mamaki bane ba!” K’arshema cewa tayi “ya taso suje ko da ta window ne ya lek’a ya ganta, in ba fad’a maka akai ba ba zaka tab’a yarda ma ta tab’a yin rashin lafiya ba! Har waya fa suke yi da Dad”. Shiruu, kawai Aslam d’in yayi a zuciyar shi yana godewa Ubangiji, sannan yana adduar Allah ya kawo ranar da zata warke baki d’aya su zauna inuwa d’aya shi da ita….. A d’akin suka zauna bayan Doc ya tafi, shi Aslam har haushi ma suka fara bashi dan sai kace wani jariri haka suka maidashi wai duk dan Doc yace kar a barshi da damuwa ko loneliness. Sai wajajen 11 Arshaad ya k’arasa karatunshi shi da Aslam da Gwaggo Asabe tukun yayi musu sallama ya tafi bayan ya tabbatar Aslam din ya sha maganinshi. Dariya Arshaad yake bawa Aslam, shi ala dole fushi yake yi dashi wai akan yak’i fad’a mishi damuwarshi dan ko kallonsa ma baya yi amman kuma shi yayi jinyar shi yanzu. Arshaad, ya fito kenan a babban parlourn suka had’u da Jalila, yayi matuk’ar mamakin ganin yanda ta rame. Bai kula ta ba ya d’auke kai kawai ya yi wucewarshi, ga mamakinshi shi kawai yaga tasha gabanshi ta tsaya. Tamke fuska yayi kafin ya tsareta da lumsassun dogayen idanuwanshi cikin dakakkiyar murya yace “Jalila!” Jin yanda ya kirata, da yanayin data ganshi ya mugun tsoratata dan haka ta kasa magana ta kasa cewa komai chaaan! Kuma sai ta hau kame kame tana wasa da y’an yatsunta “Em, Ya Arshaad wai dagaske Gwaggo Asabe take?” “Da gaske take me?” “Maganar aurenku kai da Huda…” Sai kuma ta fashe da kuka. Da mamaki yake kallonta kafin yace “Eh” Kawai ya juya ya fita dan ya san indai ya ci gaba da tsayuwa Inuwa d’aya da ita tou tabbas za a samu matsala! Ya san babu kyau ka tsani d’an uwanka musulmi but he cant help it! Wallahi tunda yake a rayuwarshi bai tab’a jin tsantsar tsagwaron tsana kalar wacce yake yi wa Jalila ba. Da gudu tayi hanyar d’akin ta tana zuwa ta dannawa Umma kira! Ko gaisawa bata bari sun yi ba ta fara magana “Umma, Huda aure zatayi! Ya Arshaad zata aura. Umma wallahi mutuwa zan yi in ya aureta Umma dan Allah kiyi wani abun, wallahi ina sonshi.” Cikin katseta Umma tace “Dalla malama ki tsaya ki nutsu kiyi min magana yanda zan fahimceki” Cikin kukan jalilan ta hau yi mata bayani tiryan tiryan akan yadda taji Gwaggo Asabe suna maganar auren ita da wata mai aiki satin baya daya wuce data tambayeta kuma ta gasgata mata hakan sannan yanzu ma Arshaad d’in ya sake tabbatar mata. Cikin b’acin rai Umman tace “Kece ai Jalila da shegen son abunki! Nace miki ki kawo kud’i kin k’i ki bayar ya kikeso in yi? Babanku ma yanzu haka baya nan ya gudu saboda ba zai iya rayuwa ba Maryam ba! Ga Ja’afar ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96