Chapter 84
Chapter 84
yi’ Amman ta kasa nutsuwa kuma zuciyarta ta k’i ta daina tafarfasa…… Sannan zata fita daga estate d’in nan, da Auwal ya maida mata shi kamar kurkuku. Murmushi tayi aranta tace “Zan jefi tsintsu biyu da dutse d’aya!” Driver ne ya jasu su duk biyun a baya, kamar yadda tayi zato kuwa masu gadin da kyar suka bari aka fita da ita.... Sai da Mom ta nuna mata d’akin da zata zauna a sama, daganan ta wuce nata d’akin. Sai da Ummi ta tabbatar kowa ya watse tukun tabi bayan Mammy Sisters d’inta( Mammyn) kuwa ko sallama basu yi mata ba suka wuce suka rabu da ita. A d’aki ta sameta sai faman safa da marwa take yi ta hana zuciyarta sukuni sam!. Ta ganta sarai taga shigowarta amman sai tayi banza da ita taci gaba da kai kawon da yake yi. A hankali Ummi ta nemi waje ta zauna tukunna tace Mammy Da sauri Mammy tace “Zainab tashi ki fita! In dai shawararki kika san zaki sake bani to tashi ki fita tun kafin raina ya b’aci!”. Murmushi Ummin tayi sannan ta fara magana “Dama ai in dai kinga mutun yana farin ciki idan ana bashi shawara in yayi ba daidai ba to ki tabbata ba gaskiya ake fad’a mishi ba! Nazo in baki shawara ne Mammy kuma zan yi matuk’ar farin ciki idan naga kina jin haushin shawarar tawa dan na san gaskiya ce nake fad’a. Bari kiji in fad’a miki abunda na San Baki sani ba.. idanuwanki ne suka kulle ba kya ganin komai ba kya ganin kowa sai k’iyayyar Huda da Aisha wadda kika gani abkan k’afafuwanta!” Da sauri Mammyn ta kalleta kafin tace “Magana zaki fad’amin? Me kike nufi? Use your words! Ta fad’i hakan tana me k’arasowa daff da ita. Mik’ewa Ummin itama tayi sannan tace “Ba zan yi using words d’ina ba Mammy dan na san kin san me nake nufi! So yanzu ba lokacin tashin tashina bane ba, yanzun lokaci ne wanda ya kamata ace kin farka idanuwanki sun bud’e sannan kin kalli rayuwa da idon gaskiya da basira. Bari in baki wani d’an misali , watak’il ki gane abunda kowa yake son fahimtar da ke wanda kika kasa nutsuwa ki fahimta.. For instance ace, ki samu kare ki kulle shi yayi kwanaki baki bashi abinci ba! Rana d’aya ki samu dogon lungu, a k’arshen lungun ki ajiiye nama da k’asusuwa da ruwan sha sannan ki kawo zarto k’usoshi da wuk’a ki ajjiye a daidai ta saman lungun a saman wannan naman sannan ki d’ana mishi tarkon da in dai yabi ta kai ya taka to wannan wuk’a da zarton zasu sauk’o su chakeshi su kasheshi murus har lahira ba tare da ya ci wannan naman ba.” Ajiyar zuciya Ummi ta sauk’e kafin tace “Ki gaya min in akwai mahaluk’in da ya isa ya hana wannan karen cin naman nan? Ko kuwa shin wannan karen zai iya hankalta da wannan tarkon da yake a gaban naman? Amsar anan itace ‘a’a’, sai dai In d’auke shi za ayi ta k’arfin tsiya a sama mishi sabon nama a bashi yaci. Sannan ne za a samu sauk’i. Wannan karen ba kowa bace face, ke. Naman nan kuwa, Hudan ce da Aisha waenda k’iyayyarsu haushi da takaicinsu ya sanya kika kasa ganin komai da kowa hatta tarkon dake gabansu wanda in dai kika taka to tabbas wuka zata fad’o kanki ta kashe ki har lahira ba tare da kin tab’a su ba! Waennan tarkon da wuka’ak’e ba komai bane Mammy face Dad da Arshaad da auren ki da mutuncinki da k’imarki, da kike k’ok’arin lalatawa ki kashe rayuwarki jin dad’in ki kwanciyar hankalinki da farincikinki da aurenki, duk akan rashin hak’uri. Second option kuma da na baki na ‘sai dai a d’auke karen a bashi sabon nama’ Shine wanda ni, y’an uwanki da Aaima muke ta k’ok’arin fahimtar da ke!. Idan kika yi hak’uri kika sawa kanki da zuciyarki salama, zaki samu peace of mind za ki samu farin ciki amman fa sai kin yi tunani irin na mutane bawai irin na karnuka da basa ji basa gani idan suna jin yunwa ba. Ki daure ki kwantar da hankalinki, wata rana sai labari. Kar kije maybe akwai babban rabo a tsakanin Hudan da Arshaad ki kashe kanki ba tare da kin hankalta ba...” “Attakhbir! Allahu akhbar! Mai k’aramar kwakwalwa da zuciya. Naji na gode reformed Zainab! Na lura tunda kika ji azabar cell shikenan zuciyar ta mutu. To bari kiji in gaya miki Wallahi! Kin ji dai na rantse gara rabon dake tsakaninsu ya kashe ni! Akan in zauna a gaban idona a d’aura musu aure inaji ina gani dan na tabbatar bak’in ciki ne zai k’arasa ni muddin Arshaad ya auri wannan Yarinyar!. Kinji dai kankat! Kenan, ko?. Oya jeki na gode duk ranar da fargabar cell ta bar jikinki, kya iya zuwa mu yi magana.” Cewar Mammy. Bak’in ciki ne ya hana Ummi sake ce mata komai, dan haka kawai ta juya ta fita cike da takaici da tsananin mamakin Mammy. Da harara Mammyn ta rakata, sannan tayi tsaki ta koma kan gadonta ta zauna. Ummi na fita suka had’u da Daddy da alama d’akin shi zai yi amman yana ganinta yace “ta zo suje ya kaita kawai ya gama tukun ya huta.” Ba ta san taya zata fuskanci Abba ba, bata san taya zata fara bashi hak’uri ba! Hakan yasa tunda taje ta yiwa su Granpa sallama suka d’au hanya zuciyarta take ta faman tsitstsinkewa..... Ba kowa a parlourn dan su Shuraim tun safe suka tafi gandun albasa. Basu dad’e da gama waya da Dad ba yace mishi yana gida don haka suna zama ya kirashi yace “ya sauk’o gashi ya kawo Ummi” Wallahi Abba har ga Allah har cikin zuciyarshi shi mantawa ma yake yi da wata Ummi. Mike’wa yayi kawai ya je jikin drawer inda yake ajjiye important documents d’inshi ya d’auko takardar da ya dad’e ajjiye da ita, ya fice yayi k’asa. Da kyar ya iya daurewa suka yi cikakkiyar gaisuwa shi da Dad. Ummi na shirin gaidashi da fara sake bashi hak’uri har da d’am zamowarta daga kan kujera taji yace “Ke! Zo ki karb’a nan” Ganin ya mik’a mata farar takarda ya sanya gabanta ya hau dukan uku uku! Ba ita ba hatta Dad sai da ya shiga rud’ani. Bata gama gigicewa ba sai da ya daka mata wata uwar tsawa! A take jikinta ya d’au rawa. Gudun kar ta b’ata mishi rai ya sa ta mik’e da kyar ta k’arasa inda yake tasa hannu biyu ta karb’a…. Dad ne yace “Abba meye wannan ka bata?” Yana mai tsareshi da idanu. Cikin nuna halin ko in kula yace “Ta karanta za ta gani” Da kyar Ummi ta iya bud’e takardar, jikinta na karkarwa tana adduar Allah yasa ba abunda take tunani bane… Zuwa yanzu ran Dad ya soma b’aci da attitude d’in Abba dan haka cikin b’acin rai ya yunk’uro da niyyyar fara zazzzage mishi ta cikinshi dan yaga alamun da renin wayo ya sauk’o k’asan shi kuwa yadda Mammy ta gama chaza mishi kai wallahi ba Abba ba ko waye ya shigo gonarshi yau sai ya ci ubansa! Ya bud’e baki kenan, yaji k’arar fad’uwa! Da sauri
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96