Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 42

Chapter 42

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da kayan leda leda. Godiya Huda tayi mata bayan ta gama, ta juya ta fita. Ita kuma ta tura k’ofar taja kayan zuwa bedroom. Tana gama ajjiyewa a closet ta fito kenan ta zauna akan gado Abba ya shigo cikin jallabiya mai k’aramin hannu rik’e da hannun Sudais wanda shima yake sanye cikin kayan bacci. Da sauri Sudais d’in yazo ya rungumeta sannan yace “Abba just told us that you are our big sister, i’m so glad that we’ve a big sister” Ya k’arashe maganar yana sake hugging d’inta. Murmushi tayi itama tayi hugging nashi back kafin tace “I’m so glad to have cute brothers too.” Da sauri ya d’ago yace “Monday idan anje school zan gayawa Ashraf da Sultan da Kareem nima nayi big sister, dariya suke yi min kullum suna tsokanata! Yanzu kema kice Abba ya kaiki school d’inmu a sakaki a ss2 dan Allah so that i can come and see you during break time just like they do, and also....” Abba ne ya dafa kanshi yana dariya, kafin yace “Sudais wai har yanzu baka san ka girma ba? Ya kamata fa ace ka daina wannan shirmen And Big sis ta gama secondary ai,,kar kayi mata adduar komawa baya mana. School d’in su Aaima zata tafi, ko?” Yayi maganar yana kallonta yana murmushi. D’an zamowa tayi ta gaidashi, a hankali ya amsa yana mai dafa kanta yana kallon idonta da tashi d’aya ya fahimci taci kuka. A kan Kujerar gefen gadon ya zauna yana kallonta kafin yace “Me ya saki kuka? Mama kike son sake gani?”. A hankali ta sunkuyar da kanta k’asa kafin tace “ina jin ba dad’i ne akan abunda nayi mata jiya, Ummu ta kirani nace mata mun dawo, inaga haushi suka ji dan I’ve been calling them since last night amman ba wanda ya amsa.” Ta k’arashe maganar tana sakin kuka. Ajiyar zuciya Abba ya sauk’e kafin yace “A kawo miki Sakina? Ku zauna tare?” Da sauri ta d’ago tana kallonshi, sai kuma ta hau d’aga kai tana share hawayenta. Murmushi yayi kafin yace “Ok, but no more crying, in ba haka ba in fasa.” Da sauri ta cigaba da goge hawayenta, da kyar kuwa ta samu suka tsaya…. Abba bai kira Baban Sakina ba sai da ya sakata tayi murmushi kala uku! Sudais yana tayashi da yi mata cakulkuli. Bayan sun gaisa ya tambayeshi akan “Dan Allah ya bar Sakina ta zo ta d’anyi kwana biyu da su tunda basu fara school ba yanzun, maybe Hudan ta d’an sake in ta ganta.” Nauyi da kunyar Abban ne suka hanashi yi masa musu dan haka yace “yanzu an sallami Mama ne suna kwashe kaya, amma zuwa anjima in shaa Allah zai kawota. Ya tura mishi adress kawai.” Godiya yayi sannan ya kashe wayar, ya tura mishi da adress d’in. Yaji dad’in yadda ta saki ranta sosai. Cikin murna ta tanbayeshi “me zata dafa?” Murmushi kawai yayi yace mata “koma me ne in ta dafa yayi” Kafin ya tambayeta adress d’in su Sakina, tayi mishi kwatance, daga nan suka fita shi da Sudais........ Wanka tayi ta sa wani silk gown, A shape, colour d’in emerald green, an d’anyi kwalliya ta k’asan k’irjin da igiya mai stones ya zagaye, daga gefe ta gaban an tufkeshi yayi kmr ribbon babba. Bai matsetaba kuma bai yi mata ruwa ba dai dai jikinta, tayi masifar yin kyau, ta gyara gashinta ta tufke a k’eyarta sannan ta d’auko d’ankwali kayan ta nad’a wanda kasancewarshi k’arami, yasa ta d’anyi normal d’aurin kai dashi ta kuma bi da edges d’in dankwalin ta kan gashin data tufke ta sake zagayewa da shi d’ankwalin. Sannan ta d’auki turare ta fesa duk a cikin kayan da tayi order jiya. Tayi kyau sosai kuwa abunta. Wayarta ta d’auko ta kira Ummu still bata d’auka ba, Sakina kuma a kashe. Jiki a mace haka ta sauk’a ta shiga kitchen. Ga mamakinta har an gama breakfast, maid d’in jiya da wani shima da uniform a jikinsa irin nata (maid d’in), Sun gama hada komai, kuloli wajen uku, kitchen d’in sai tashin k’amshi yake yi. Sai da ta k’araso tsakiyar kitchen d’in tukunna suka lura da ita, kamar zasu kifa haka suka hau gaidata cikin girmamawa.. Itakam kunya da mamaki ma da kyar suka barta ta amsa. Ta riga tayi niyyar yiwa Abba girki shiyasa ta tambayesu me suka dafa? To dai d’ayan abincin itakam ba ma ta sanshi ba kuma bata tab’a ganinshi ba ma, sai shawarma a d’ayan kulan, farfesun kayan ciki kuma a d’ayan, sai ruwan zafi a flask ga mai buk’ata. A hankali cikin nutsuwarta ta k’arasa ta bud’e inda suka nuna mata a matsayin store d’in ta shiga.. Babu abinda babu a ciki, dan haka ta d’auko, dankali kad’an da kwai da Mayonnais da su albasa sai su green beans da macaroni. Sun so su tayata aikin amman tak’i, da kanta ta had’a mishi potatoe salad mai d’ankaran dad’i da kyau! A dining d’in taje ta ajjiye bayan ta juye a cooler. Tana shirin barin wajen Auwal ya shigo… Suna had’a ido da shi ya b’ata rai! Fuskarnan tamau haka ya nufo dinning d’in. ita dai Huda ta lura kwata kwata wannan baya k’aunarta ya tsaneta! A hankali ta gaidashi amman kamar wanda take magana da dutse ko kallon inda take bai yi ba! Kujera kawai yaja ya zauna ya hau had’a tea. D’aga sagaggun k’afafunta tayi ta fara takawa don barin wajen dai dai Abba yana sauk’owa, bata ma lura dashi ba sai da ta kusan tsakiyan falon suka yi kicib’is! Murmushi yayi ya dafa kanta sannan yace “har an gama girkin?” Itama murmushin ta mayar mishi tace “Eh” “Ok, muje.” Yace sannan ya kama hannunta suka juya. Suna zuwa Auwal ya mik’e ya gaidashi, cikin kulawa Abban ya amsa mishi sannan ya cewa Huda “kun gaisa da yayan naki?” A hankali ta d’aga kai alamar ‘eh’ Harararta yayi sannan yace “Daddy ne yace kuzo muyi breakfast.” “Ok” Abban yace sannan ya cewa Huda taje taga ko su Shuraim sun gama shiryawa. Har ta juya taji yace “Ina abincin da kika dafa?” Da sauri taje ta d’auko kular ta mik’a mishi, karb’a yayi sannan ya mik’awa Auwal yace masa “fara yin gaba da wannan, gamu nan zuwa.” A k’afar bene ta had’u da Yaran dan haka suka juya tare. Suna k’arasowa parlourn suma suka wuce side d’in Daddy. Ita dai tana mamakin tou wanchan uban abincin, da aka dafa musu waye zai ci!? Kasa hak’ura tayi ta cewa Abban “Ko ta koma ta d’auko kulolin chan, masu aikin fa sun yi girki”. Murmushi yayi yace mata “Karta damu anjima da yamma idan anyi na sadaka za a had’a a kai tare da wanchan d’in.” BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 42 Yadda side d’insu yake, haka na Daddy shima yake, komai da komai iri d’aya, kawai de akwai k’ofofi da corridors d’in da suke a nasu wanda babu a na Daddyn. A parlourn suka tarar da Daddy d’in da alamun su yake jira. Abba ne ya fara gaidashi tukun su Huda. Yana jin Yarinyar a jikinshi matuk’a dan haka bayan ya amsa ya hau tambayarta “ya take? Tana jin dad’in zaman? Akwai abunda take buk’ata?” A hankali tace “komai Alhamdulillah. “Ma

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});