Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 61

Chapter 61

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

har k’asa ya gaida su Mama, shima (Arshaad) d’in d’an rissinawa yayi ya gaidasu, daga nan suka d’an zauna. Kafin daga baya suka mik’e suka ajjiye musu jibga jibgan ledojin da suka shigo musu da su, suka yi musu sai da safe… Ummu ce ta cewa su Sakina “su tashi kar ayi ta jiran su” da kyar suka fita tare da su Arshaad da alk’awarin gobe da sassafe za su dawo!. Sai da suka fita tukun suka ga ashe har da Abba aka zo. Ita da Sakina ne suka shiga motar Abba, Arshaad kuma suka wuce shi da Auwal. Suna yin parking Sakina ta bud’e ta fara fita bayan ta yiwa Abban sai anjima, Hudan na shirin fita Abban yace mata “Ya jikin Maman naki?” A hankali tace “da sauk’i”. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Arshaad yace har da karaya ko?” “Eh” Ta bashi amsa. Cikin d’acin zuciya yace “na yiwa Mamanki laifi! Na saka polisawan wajen da akai kai Mijinta sun yi mishi duka bana wasa ba! Wanda shima hakan da nayi na san maybe idan taji labari zata iya jin haushina! But maza irin Usman irin haka ya kamata a dinga yi musu. Inaso in cire hannuna akan case d’in amman sam na kasa Hudan ban san mai yasa ba. Wallahi da ace ina da hali ko inda Maryam tabi Usman bai isa ya taka ba! Amman k’addara ta riga fata, kuma ance ba a shiga tsakanin Miji da mata, sam.” Shiruuu, Hudan ta d’anyi, tana son gaya mishi amman kuma sai taji ta kasa. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace mata “Good night, kije ki huta kun sha jigilar asibiti.” A hankali tace “good night Abba” ta fice. Sun dan tab’a hira kad’an a parlour da Arshaad sannan ta sallameshi ta bashi sak’on Mommy, ta nufi d’aki a ranta tana mamakin yajin da Aslam yayi musu, lokaci d’aya kawai ya d’auke k’afa!. Har ta haye bata ga shigowar Abba ba kuma ta san ba fita yayi ba. Ya dad’e a mota, kafin da kyar ya samu ya fito ya shiga ciki yana ganin dishi dishi tsabar tashin hankalin da b’acin ran da yake a ciki, ya rasa me zai yiwa Usman ya huce takaici da bak’in cikin da yake ji….. Sai da su Hudan suka zo kwanciya tukun take gaya mata yanda suka yi da Abba d’azun sannan a hankali ta d’aura da cewa “bana son had’awa Mama case biyu shiyasa na k’i ce masa komai” Murmushi Sakina tayi kafin ta kamo hannuwanta duka biyu tace “Ki yi tunani, duk abinda kika ga ya dace, kiyi musu.” Da sassafe ta tashi ta shirya, tana shirin zuwa side d’in Abba taga call d’in Arshaad, sai da ta d’anyi jimm!! Tukunna ta amsa ta gaidashi. Cikin kulawa da so ya amsata kafin yace “ta sameshi a k’asa” Tare suka sauk’a ita da su Shuraim waenda za su school. A parlourn ta tsaya tayi musu a dawo lafiya, sannan ta k’arasa inda Arshaad d’in yake zaune. “Za ki fita ne? Naga kin shirya da sassafe” Yace yana kallon ta. A hankali tace “eh, amman sai wajen 9 yanzun ina son yin magana da Abba ne” Cikin bata dukkannin attention d’inshi yace “Exactly abunda ya kawo ni kenan. Did you tell him? I’m sorry na san bai kamata in yi miki wannan maganan ba but naga kamar Abban is disturbed, na dad’e ban ganshi a wannan yanayin ba. Me kikayi deciding? Za ki fad’a masa ne?” Ya jero mata tambayoyin yana mai tsareta da ido. Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “jiya dai ban gaya mishi ba, but yau na yi deciding in fad’a mishi d’in, duk da ban san ya zai yi handling abunba, and I’m not even sure they still want each other back.” Murmushi Arshaad yayi kafin yace “Believe me they do! Amma kin tabbatar this is the right time? After all that has happened especially ma a ita Maman” A hankali Hudan ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “I’m sure. Na riga na gama deciding” Murmushi Arshaad d’in yayi sannan yace “Ok dear. Allah ya taimaka, ya sa a dace.” “Ameen” tace. Yana d’an murmushi ya mik’e yace “Anjima idan na koma gida na d’an shirya zan zo asibitin in shaa Allah.” “Allah ya kai mu” tace. Kafin daga nan suyi sallama ya wuce office ita kuma ta nufi side d’in Abba..... A bakin k’ofar parlournshi ta tsaya ta d’anyi knocking jin shiru yasa ta tura ta shiga. Ba kowa, dan haka ta nufi bedroom. Ta jima tana knocking tukun chaan, taji ance “come in” A hankali ta tura ta shiga, da alamun tun d’azun a balcony yake dan yanzun taga yake shigowa cikin d’akin. Yayi mamakin ganinta da sassafe, dan haka suka fito parlourn suka zauna kafin ya kalle ta yace “Ya aka yi dota?” Kame kame ta fara yi, dan bama ta san ta Ina zata fara ba sai yanzu ta d’anji nauyin shi da nauyin maganar da ke tafe da ita! Chaan! Dai ta dake ta d’an sunkuyar da kanta k’asa tace “Daman, Baban ma na ji Ummu tace ya yiwa Mama saki d’aya shekaran jiya, jiya kuma tayi miscarriage” Tana gama fad’an haka tayi saurin sake sunkuyar da kanta k’asa tana ci gaba da wasa da y’an yatsun ta. Ta kusan minti biyar a haka, jin shirun yayi yawa yasa ta d’ago kanta ta d’an kalleshi, yana a yanda ta barshi idanunsa a kanta amman daga gani hankalinshi baya kanta. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Hudan, are you sure?”. A hankali ta d’aga kanta kafin tace “Very sure”. Ajiyar zuciya ya sake sauk’ewa kafin yace “Thankyou! Za ki iya tafiya” A hankali ta mik’e tayi mishi sai anjima ta fita. Su kad’ai suka yi breakfast d’insu, daman a shirye suke, dan har handbags d’in su sun sauk’o dashi, Hudan ta zaro waya zata kira drivern kenan Abba ya shigo shi da Daddy…. Wani dark ash d’in yard ke jikinshi anyi masa d’inkin kaftan! Kyalli da taushin yadin kad’ai ya isa ya sanya ka gane kud’insa ba na wasa bane sannan daga ganin d’inkin ka san ba a k’asar nan ma aka yishi ba. Ya murza bak’ar hula da bak’in takalmi…. Yayinda Daddy yake sanye cikin suite maybe office yake shirin wucewa. Gaisawa suka yi. Cikin kallon agogon dake d’aure a tsintaiyar hannunshi Daddy yace “dota ku yi sauri mu wuce ko?” Mikewa suka yi Sakina tace “mun ma gama” suka gyara zaman mayafansu. Su Abba ne suka fara fita sai su. A motar Abba suka tafi Daddyn yana binsu a baya. Bayan sun shiga asibitin an yi parking, Hudan tana shirin tamabayar Abba ‘k’arfe nawa za azo a d’auke su’ taga shima ya bud’e motar yana ce mata “ta zagayo tayi leading way d’in” Bayan ta fita sun zagayo, Sakina tayi k’asa da murya tace mata “Ashe yau Abba zance zai zo shiyasa naga ya ci kwalliya” Da sauri Hudan ta mintsineta tana d’an juyawa dan taga ko attention d’in Abban yana a kansu..Magana taga suna yi shi da Daddy wanda ya fito daga mota dan haka ta d’an sauk’e ajiyar zuciya kafin ta jaa hannun Sakina suka yi gaba.. Abba na da ji sosai shiyasa sarai ya ji

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});