Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 54

Chapter 54

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Mommy. Auwal ma ganin yanata zama shi d’aya yasa ya yiwa Abban sai da safe ya tafi, bayan yaga sauk’owar Sakina. A tare suka fito shi( Auwal ) yayi part d’insu su kuma suka wuce mota Sakina na baya Hudan na gaba a haka har suka isa bakin k’ofar gidan Baba. Ba Hudan ba hatta Sakina zumud’i take yi.. Cikin rawar k’afa suka fita a tare suka shige gidan. Basu tarar da mashin d’in Baba a soro ba, da alamun bai kai ga dawowa ba. Gidan shiruuuu, sai d’an hasken fitulu da suke hangowa ta d’akin Umma da Mama. A hankali Huda tasa hannu ta d’an tura k’ofar kafin su shiga a tare da sallama… Kendir d’in dake kan dressing mirrow ne ya taimaka wajen haskaka d’akin! Tana zaune a k’asa gaban gado kan sallayarta, da charbi a hannunta, da alama bata tashi daga wuridin bayan Isha ba dan ga hijabinta ma a jikinta, a gefe guda kuma ta kunna maganin sauro yana d’an tashi da kad’an da kad’an. D’ago fuskarta tayi ta kallesu, kafin ta maida idonta k’asa kamar bata ga kowa ba!. Gaba d’aya jikinsu sai yayi sanyi, amman suka aro jarumta suka k’arasa inda take! Sakina ce tayi k’arfin halin hugging d’inta kafin tace “Mama Ina wuni ya jiki?” “Alhamdulillah” kawai tace Maman tace mata. Itama Hudan ta gaisheta ta bita da “Alhamdulillah” Sannan ta mik’e ta cire hijabin jikinta ta ninke da sallayar, ta mik’e ta haye gado ta kwanta abunta. Duk kasa cewa komai suka yi, d’akin ya d’auki shiruuuu. Wajen minti goma ta tashi taje ta kashe kendir d’in ta dawo ta tofa addua ta kwanta, harda d’an jan abun rufuwa. Sheshshek’ar kukan Huda ne ya sa Sakina kunna flash d’in wayarta! Itama Mama jin kuka yasa ta mik’e ta zauna daga kan gadon tana kallonsu a inda suke. A hankali Sakina ta cewa Mama “Mama dan Allah ki yi hak’uri mana.” Cikin katseta Maman tace “Hak’urin me?” Dibi dibi Sakina ta hau yi kafin ta samu damar cewa “Naga kamar kina fushi da mu ne” Murmushi Maman tayi kafin tace “ba fushi nake yi ba Sakina, ko kad’an bana fushi daku Kawai kun zab’i abunda kuka ga ya dace ne Nima kuma na zab’i wanda naga ya dace!” Ajiyar zuciya ta (Mama) sauk’e kafin ta juya kan Huda tace “Na san abunda kika yi ranar da kika zo duba ni a asibiti! Dukda Ummu taso b’oyewa amman naji kuma na fahimta! Na gode Hudan, Mahaifin ki ya fini ko? Ba komai.. Amman abunda nake so ki fahimta shine Tunda shi kika zab’a, to ki zauna a iya shi kad’ai kar in sake ganin k’afar ki a inda nake! In ba hakaba wallahi sai ranki ya b’aci! Na bar masa ke! Tunda naga a ganin ki yanzu ban dace ki zauna da ni ba, kin girma ko? Kin mallaki hankalin kanki, so bani da wani amfani a wajen ki, tunda ba abunda zan iya miki ko zan iya baki..” Wani irin kuka Hudan ta rushe da shi, tana shirin yin magana Mama ta katseta ta hanyar cewa “Haka ne mana, kar ki min kuka gaskiya na fad’a! Kinyi girma ai yanzu tunda har kika iya yankewa kanki decision..” Sakina ce tace “Mama dan girman Allah kiyi hak’uri, wallahi kin yi misunderstanding d’in mu ne Please Mama ki tsaya ki fahimcemu” “Hmmmm” Maman tace, kafin tace “Nima kun kasa fahimta ta Sakina ba wai haushi naji ba fa, kawai ina baku space d’in da kuke buk’ata ne, tunda gashi ta nuna min k’iri k’iri abubda ranta yake so ai kinga sai in barta in daina kutsa kaina cikin rayuwarta ko?? Ku tashi kuje dare yayi, na san yau ma yana waje yana jiranki! And maganar zuwa kotu itama na daina yi! Tunda gashi k’iri k’iri kin riga kin zab’i abunda kikeso, so ba amfanin zuwa kotun tunda babu amfanin inje inata yak’i ni kad’ai. Sai kuje ku yi ta rayuwarku mai dad’i cikin daula ke da Mahaifinki.” Tana gama fad’in haka ta koma ta kwanta abunta. Kusan 20 minutes suna bata hak’uri, amman tak’i kulasu Sai da suka kaita bango ta tashi ta balbalesu da fad’a tace “wallahi In basu fita ba zata dake su! Su bar ganin wai sun girma.” Mik’ewa Hudan tayi kamar zata fita, sai kuma ta koma da gudu ta je ta kanainaye Maman tace “Ni ba inda zan je, dan Allah ki daina fushi dani haka, ba zan sake komawa ba, anan zan zauna.” Kasa cewa komai Mama tayi.. Suna a haka wayar Hudan ta fara ringing, har ta tsinke ba wanda yayi yunk’urin d’aukar wayar… Sai da aka sake kira, tukunna Sakina tayi k’arfin halin d’auka ta d’an fita waje, ta fad’awa Abban halin da ake ciki “Sai da safe” kawai yace mata, daga nan ya kashe wayar! A chan d’aki kuwa, da kyar Mama ta d’an kulasu.. Sai da Hudan tayi mata alk’awarin ta bar zuwa gidan Abba har abada sannan ta d’an sauk’o…. Daga Hudan har Sakina, gabansu fad’uwa yake yi dan basu san ta inda zasu fara yi mata bayanin baikon Hudan da sa ranar da aka yi ba! Chaan dare! Kowa ya kasa bacci sai juyi suke yi, Mama ta hango kendir d’in d’akin Umma a kunne, ita tama yi tunanin ko tana d’akin Baba ne tunda ita ke da girki, gudun kar ya k’are ya kama wani abun yasa ta cewa Sakina “taje ta kashe mata kendir d’in, in k’ofar a bud’e take.” Tun daga bakin k’ofar d’akin Sakina fara jiyo gwarti! Tsaki tayi ta d’anyi sallama kusan sau uku, jin shiru yasa ta d’an tura k’ofar ta shiga… Kendir d’in saura kad’an ya k’are, dan ba don ta je ba ma to da babu abunda zai hanashi kama kan mudubin katakon d’akin, dan Umman bata d’aurashi akan komai ba kamar yadda taga Mama tayi ba. Kallonta tayi dariya taso kufce mata, da sauri ta hure kendir d’in ta fito ta maida k’ofar ta rufe ta wuce a ranta tana mamakin rashin hankali jahilci da rashin sanin ciwon kai irin na Umma! Ace y’arki tana nan da ciki a chan wani gidan da baki san ko su waye ba! Amman kalli yanda ta barrarraje tana shek’a uban bacci kamar wata jaka! Da wannan tunanin Sakina ta k’arasa d’aki ta tarar bacci yayi nasarar d’auke Hudan, daman ita bata da wuyar bacci. Itama Sakinan bata wani dad’e ba baccin ya d’auketa cike da tunanin rashin man kai irin na Umma…inda ace su Ummu ne akace d’aya a cikin ita ko Huda bata gida ta tabbatar ko gigin yin bacci ba zasu yi ba!….. Abunda Sakina bata sani ba shine Umma magani mai k’arfin tsiya ta sha, dan yau kusan kwananta uku bata iya bacci tun lokacin da Jalila ta gaya mata Huda cousin d’in Arshaad ce! Ga kuma Mahaifinta yana son ta harma sun bar gidan kakan da shi da yayanshi duk akan Huda! Yau kuwa da Jalila ta kirata take shaida mata irin daular da Hudan take ciki sai da ta kusa hauka! K’arshema dishi dishi ta fara gani! Ga zuciyarta tana ta bugawa da mugun k’arfi ga zazzab’i. Don haka ta lallab’a taje wani Chemist a chan bakin titi babba da aka bud’e

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});