Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 88

Chapter 88

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Anty Zainab da Umma suka samu suka iya zama…Umma so take yi ta sake mik’ewa tsaye tace “To Ina y’an unwan Ango!?” ta sake creating scene amman sam ta kaasa dan in banda dishi dishi babu abunda take gani! A ranta ta shiga aiyyana …..Tabbas sai taci uwar malan ado! Wallahi sai ta saka an yi mishi yasin mai walk’iya! Ba Malami ba ko uban waye shi. Kuma sai ya bata kud’inta. Jiya jiyan nan fa ta sake komawa wajenshi dan ta sake nanata mishi, shi kuma ya tabbatar mata da “babu aure tsakanin Hudan da Arshaad ya riga ya gama aiki kuma ya buga k’asa ya tabbatar ba Mijin ta bane ba sannan ya ingiza zuciyar iyayen shi (Arshaad) ya rura wutar k’iyayyar Hudan a cikinta ta yanda ba zasu tab’a bari ayi auren ba musamman ma Mahaifiyarshi (Arshaad)…” Amman kalli yadda Maman nasa taketa jan Hudan a jiki, anyi musu hoto yafi kala nawa tare sai faman fara’a take yi tana washe baki kana ganinta ka san tana cikin tsantsar farin ciki….Inaaaaa!!!!! Taya ma zata tsaya ta yarda Hudan ta auri wannan No1 kyakkyawan da ita tunda take a rayuwarta ko a telebijin bata tab’a ganin mai kyawunsa ba! Ga uban kud’i ga kyau kamar aljani Allah sarki Jalilan ta dole ta mutu akan soyayyar Arshaad, ai kuwa idan zata yi yawo tsirara wallahi sai ta raba auren Huda da Arshaad ko sama da k’asa zasu had’e Wallahi sai dai in rabo ya kasheta akan dai ta zauna ta nad’i wannan abun takaicin da ta san k’arshe in dai bata d’auki mataki ba to shine ajalinta! Kuma ko yana so ko baya so sai ya auri Jalila! Wannan alkawari ne ta d’aukarwa Jalila da ita kanta! D’an halal ka fasa…….. Anty Zainab ce ta tab’o ta wanda hakan ne ya katse mata tunani. Da kyar ta iya motsa wuyanta dan ji take kamar ba jini da rai a dukkannin ilahirin jikinta Suna had’a ido taga itama Anty Zainab d’in idanuwanta sun kad’a sun yi jazir! Kafin Umman tace wani abu taji tace “Sadiya taso mu tafi, kai na ciwo yake yi min” Suna shirin mik’ewa suka fara jiyo gud’a daga parlourn Madu sai a sannan ma suka lura Shuwa da Baaba Talatu da wasu y’an tsirrun mutane basa wajen A bakin matan wajen sukaji an fara k’us k’us d’in “Ashe tun d’azu mazan gidan Ango suka zo sun kawo lefe yanzu suka wuce da yake falon Madu yana da k’ofar shiga da fita ta waje, shiyasa har suka zo suka tafi ba wanda ya sani Sai da suka tafi yanzu akace aje a fito da shi” Sunaji anata k’usk’us d’in “ai motocin da suka zo da su ma kansu abun kallo ne! Gasu kana ganinsu kaga manyan mutanen da kud’i ya zaunamawa” Da kyar Umma take iya jan numfashi, dan ji take yi gaba d’aya iskar wajen bata isarta!. Ummu ce ta d’an matsosu kafin tace “Umma kuzo muje a fito da lefen nan kowa ya gani ko?” Anty Zainab ce ta iya ce mata “eh” Itanma da kyar, daga haka ta mik’e ta d’an dafa Umma kana tace “Muje Sadiya” Da kyar ta iya mik’ewa k’afafun ta suna rawa suka jera ita da Anty Zainab suka bi bayan Ummu suka yi parlourn b’aki. Mutane kam wasu basu ma samu damar shiga ba dan akwatunan sun cike parlourn tap! Ganin kowa cirko cirko a tsaye iya y’an k’alilan kuma na a ciki suna mik’owa ana fitowa da shi ne yasa suma suka ja suka tsaya a gefe kai kana ganinsu ka san basa cikin hayyacin su.. Ta gabansu aka fara wucewa da akwatuna nan kuwa suka maida hankali suka hau k’irgawa! Ana wucewa da goma Umma ta nemi d’an dakalin slop ta zauna dan jiri ne taji yaana d’ibarta ba na wasaba! A tunaninta su kenan amman ga mamakinta sai taga ana ta sake fito da wasu! Ganin ta k’irga ashirin da d’aya basu k’are ba ya sanya ta janyo Anty Zainab wadda itama tayi mutuwar tsaye kafin tace “Zainab zo mu bar wajen nan, tabbas kwakwalwa ta ta d’an samu matsala sannan bana gani sosai! Gani nake yi anata wucewa da akwatuna fa har yanzu basu k’are ba.” Da sauri Anty Zainab d’in tad’an dafa ta dan yanda take magana da sauri kuma da k’arfi kamar wata zararra ya sanya mutane har sun fara d’an juyowa ana kallonsu. A hankali tace mata “Ba idonki bane! Ashirin da hud’u ne cass! Gasu chan ragowar ukun Sai kuma waenchan baskets d’in da ban san na menene ba” Bata ida rufe bakinta ba aka fara fito da na Gwaggo da Kawu. Ai kuwa Umma bata san lokacin da ta mik’e tsaye ba tace “Amman dai Maryam sayar da y’ar nan tata tayi ko!? Haba mana wannan abu kuma ai ya zama hauka! Meye hakan? Me sukeso su nuna?” Cikin takaici Anty Zainab tace “Wallahi Sadiya za kiyi hanyarki nima inyi tawa har a tashi daga bikin nan gaskiya! Maganar Allah kenan, haba mana! So kika mu zama abun kwatance? Sai wasu abubuwa kike yi kamar tab’abb’iya? Kiyi controlling kanki mana Haba?” Ta fad’i hakan tana mai wucewa ta barta a tsaye nan dan a yanda take jin zuciyarta yanzu, tsaf zata iya sauk’e ruwan bala’i da fushinta akan matan dake k’ok’arin maidasu telebijin…. Sai da Umma taga an gama fito da kayan an watse daga wajen sannan ta samu da kyar taja y’an k’afafuwanta ta isa harabar tsakar gidan. Banda gud’a da hayaniyar mata ba abunda yake tashi A lokacin har an bud’e akwatunan farko an fara dubawa…. Sai a sannan ne Aslam ya samu ya tatttaro nutsuwar shi da d’an ragowar kuzarinsa ya mik’e tsaye! Yana mik’ewa Ummu da Mommy suka k’arasa wajensu.. D’an b’ata rai yayi kafin yace “Mommy zan wuce wannan bidi’ar bada ni ba gaskiya” Murmushi Mommy tayi ta shafa kanshi kafin ta juyo ta cewa Ummu “Zai iya tafiya?” Murmushi Ummun tayi kafin tace “eh, zai iya ai an gama komai” A hankali yace mata “Sai anjima” Cikin kulawa tace “Mun gode kwarai Aslam, mun gode.” Ajiyar zuciya kawai ya sauk’e daga nan ya ajjiye sandar hannunshi a gefe ya juya dai dai nan su Sudais suma suka mik’e Shuraim yana ta b’ata rai shi ala dole ya gaji.. Ummu da Mommy ne suka yi musu rakiya har waje, shi da Sudais da Shuraim bayan ya kira drivern da zai maida Mommy gida yace masa ya taho yanzun… Mutane in banda kallonsu ba abunda suke yi sunata yaba kyawun Angon Gashi bai wani zak’e ba irin yanda Angwayen yanzu suke yi! Instead shi ya kama kanshi matuk’a, hakan kuwa ba k’aramin burge jamaar wajen yayi ba. Su Mommy suna komawa suka tarar anata ware lefe an yi filla filla ana gani… Tun daga kan atamfofi Umma ta raina kanta… Zata iya cewa tunda Laraba ta kawota duniya bata taba shiga tashin hankali irin na wannan lokacin ba! Hankalinta bai gama tashi ba sai da aka zo kan akwatunan jewelry’s kit kit waenda aka ware guda biyu aka shak’e taff da sark’a da y’an kunne Na farkon fashion ne Na biyun kuwa gold ne zalla! Matar dake gefen ta ce taji tana cewa “Ai dama su

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});