Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 68

Chapter 68

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

.....Sakina bata dace da Auwal ba at all, amman in haka Allah ya tsara basu da damar shiga tsakani, besides yayi mamakin changes d’in da yake gani a Auwal those days, maybe in ya samu wadda yake so ya aura a samu ya nutsu! Ko a office yanzu ya daina biye biyen matan da a daa yake yi kamar bunsuru.... Arshaad, yana wannan tunanin yaji sauk’owarta dan haka ya juyo yana kallon yanda take tafiya a hankali kamar ba Sakina ba. Cikin kulawa yace “Sai yanzu?” Murmushi tayi tace “Bacci ne ya kwashe ni” Shima murmushin kawai yayi Hudan kuwa bata ce mata uffan ba… So take sai sun keb’e tukunna dan tabbas In tunanin ta ya bata dai dai to Sakina tana k’ok’arin rufta kanta inda dai dace ba. Suna zaune Auwal ya shigo, kujerar da Sakina ke kai 2 seater yaje ya zauna ya fara yi mata magana k’asa k’asa.. Ga mamakin Hudan sai taga Sakinar ta biyeshi, suna ta k’us k’us daga baya kuma ta mik’e ta cewa Hudan “ta zo taji”, shi kuma ya mik’e ya juya ya nufi hanyar fita. Binta Hudan tayi, suna kaiwa hanyar bene ta rik’o hannun Sakinar wadda ta fara taka stairs.. Juyowa tayi tana kallon ta, k’asa k’asa Huda tace “Sakina kar fa ki biyewa Ya Auwal! Naga kamar ya fara cin galaba a kanki. Kin san Allah kuwa dan iska ne! Ranar da muka je Munjibir park baki ga y.....” Da sauri Sakina ta matsa kusa da ita ta sa hannuta ta toshe mata baki! Tun lokacin da Hudan ta fara magana taga tahowarshi, tana so ta hanata taga ya sa hannu ya d’aura akan lips d’inshi alamun tayi shiru yana d’an murmushi Bama jin Hudan take yi sosai ba saboda gaba d’aya hankalinta ya tafi wajenshi sai da taji tana neman b’aro musu aiki tukunna... Kallonta Hudan take, tana “hum um hum um” Alamun ta saki mata baki. Ganin tak’i barinta ya sa ta sa hannu ta janye hannun Sakinar akan bakinta kafin tace “Dan na fad’a miki gaskiya shine kike k’ok’arin kasheni? Har da hancina fa kika toshe. Kin san Allah, tou su Ummu zan gayawa dan ba zai yiu inaji ina gani ki kula d’a is....” Da sauri Sakina tace “Shhh, behind u.” Tsit! Hudan tayi kamar ruwa ya cinye ta, a hankali kuma ta juya… Karaff! Suka had’a ido da Auwal, yana d’an murmushi yana kallonsu. Hudan ta san gaskiya ta fad’a, amman sai ta tsinci kanta da jin mugun kunyar shi… Juyawa kawai tayi ta haye sama, Sakina kuma ta tsaya, ta fad’a mishi amsar abinda ya manta bai tambayeta ba, har ta kaishi ga dawowa. Bata dad’e da shiga ba Sakina itama ta shigo. A parlournta ta sameta, dan haka ta zauna akan hannun kujerar da take kai kafin tace “Hudan, dan Allah ki daina had’a ni da wannan mutumin, na fad’a miki ba zan tab’a sauraron sa ba, infact kin san ina da wanda zan aura ko?. Kinaso ki san maganar me muke yi?” Sai da ta d’an k’uraa mata ido, tukun tace “Eh” Murmushi Sakina tayi kafin tace “Zo muje d’aki to ki shirya, in yaso muna sauk’a k’asa zaki gani. Kamar tayi mata musu, sai kuma ta mik’e ta bita. Suna shiga taga Sakina tanata fito da kayan kwalliya, aikuwa tace bata san zance ba! Dan in akwai abinda Hudan ta tsana to a shafa mata foundation da concealer, ji takeyi kamar anyi mata suminti a fuska, sometimes har numfashin ta take ji yana d’an yin sama sama, bata tab’a jin iskar gari sai ta wanke.” Ba kalar rok’on da Sakina bata yi mata ba, amman furr tace “wallahi ba da itaba, ko me za ai sai dai ayi a haka” ita a tunanin ta ma ko wani get together su Sakinar suka had’a, dan tace mata surprise ne suka had’a musu ita da Auwal. Abunda kawai ta tsaya Sakina tai mata shine, eye lining..da kyar ta yadda ta ja mata liner black a saman ido d’an kad’an, sannan tasa mata brown kwalli. Ko dan bata saba yin kwalliyar ba ga kuma gyaran jiki da ta sha! Ya sanya Inka kalleta ba lalle ka iya d’auke idonka lokaci d’aya ba. Ita kanta Sakina ta kasa yin shiru da ce mata ‘kin yi kyau’. Akwai wani sirrin da idanun Hudan yake dashi wanda bata tab’a gani a idon kowa ba, gashi kuma yau yasha liner da brown kwalli. Wata zazzafar gown ta d’auko mata black, da ta ji silver stones, sai kyalli take yi. Tun daga k’irjinta zuwa k’asan mararta a tsuke ne daga nan kuma yayi wani irin bajewa har k’asa. Wani fitinennan tauban Sakina tayi mata wanda ya yi mata mugun kyau, sannan ta sak’ala mata wasu arnen silver sark’a da y’an kunne masu shek’i da abun hannunsu da zoben sai silver takalmi ta bata ta saka. Sannan ta d’auki set d’in kaya kala biyu suma duk English Wears kasancewar bata da wasu native masu kyau. Kafin tace “muje suna jira.” Har ta kai k’ofa taji shiru, juyowa tayi tana kallonta tace “Me ne kuma?” Hararar ta tayi tukun tace “A haka kikeson in fita da wannan matsarsen rigar?” Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e kafin tace “Hudan ana jiranmu, ga vail d’in nan a jakar nan na had’a In muka sauk’a sai in baki” Ba don taso ba tabi bayanta suka wuce, dan ta san tunda ta nace tou ba zata bata ba sai sun sauk’an. Ita kuwa Sakina batayi niyyar batan bane, ta gama rayawa a ranta ‘ko hoto d’aya ne sai anyi musu da wannan shigar’ ita tayi tauban d’in amman ba k’aramin tafiya yayi da imanin ta ba, dan haka bata ga dalilin da zai sa ta bata mayafi ta d’aura akai ba. Suna sauk’a suka tarar da mai hoton har ya k’araso da yaranshi dan haka suka fara…… Da kyar Hudan ta yarda ta tsaya aka yi kala uku da d’aurin daga su ta ware tayi rolling abunta. Styles Sakina ta dinga d’aukowa a insta tana nunawa.. Auwal ne yaje har gida ya d’aukowa Arshaad kaya shima kala biyu! Suite kalar kwanduwar kwai dark da kuma black d’in jamfa na yadi Suite d’in yayi using a last pics d’in da suka yi Ita kuma riga da skirt kalan suite d’in nashi tayi roling da black vail Sunyi masifar yin kyau!. Sai bayan Magrib aka kammala. Sun yi hoton har da su Sudais sannan aka yi da Auwal da su Sudais Abun sai ya zama kamar event a tsakaninsu su shidda dan har drinks da snacks suka d’auko suka d’an cicci suka yi videos a wayoyinsu........... Masu hoto suna tafiya Abba yana dawowa..A parlourn ya samesu har Auwal suna zaune suna kallo. Dai da mazan suka yi isha tukun suka zagaya gidan Daddy dukkansu aka yi dinner daganan kowa ya kama gaban shi bayan Arshaad ya karb’a ruwan adduar su...... Akwai maganar da yake so suyi da Aslam amman takaicinshi yake ji shiyasa kawai ya rabu da shi ya nufi gida.. D’azu babu yadda bai yi da shi akan ya kawo mishi kaya kala biyu ba za ai pre wedding amman k’iri k’iri Aslam d’in ya k’i! K’arshema da yayi ta kiranshi k’in d’aukar wayar yayi.

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});