Chapter 71
Chapter 71
Aslam ne yace “Oh Dad, dana sani da ban fad’a mishi ba. Waye ma ya d’auko shi a airport d’in sai Allah tunda gashi bai kira ni ba.” Murmushi Gwaggo w tayi kafin tace “ai ko kaine a matsayin shi na tabbatar sai ka zo” Murmushi shima yayi kafin yace “Kuma fa hakane” Cikin minti goma ya iso cikin d’akin! Yadda ya gansu a zaune ne yasa hawayen da yake ta koma run yaga ya danne suka samu nasarar zubowa. A hankali ya k’araso ya had’asu waje guda ya rungume .. Shi kuka Mommy da kanta ya d’aure da komai kuka Gwaggo Asabe ma kuka Da kyar Aslam wanda duk ya fi su son yin kukan ma ya samu ya lallashesu, daga nan aka hau murna k’arshe dai ba wanda ya runtsa a cikinsu har asuba. Kafin gari ya gama wayewa kuwa, labari yaje kunnuwan kowa a estate d’in, har su Abba. Daga masallaci Arshaad ya biyo Aslam suka zo tare dan ya ganewa idanuwanshi, ai kuwa shima har da kukan shi na tsananinfarin ciki. Haka shima Auwal yazo da daddare tare da Daddy da Abba duk a b’oye kar e ya gansu. Sun ji dad’in ganinta kuwa, sukayi barka suka tafi . Mommy kuwa tunda aka bata labari sannan taga su Arshaad da Aaima yadda suka girma da shi kanshi Aslam d’in, ta shiga alhinin ‘shikenan tayi missing teen age d’insu, da yanda suka taso kenan har abada?’ Gaba d’aya tausayin kanta da Aslam d’in sai ya lullub’eta.. Da kyar ta iya cin abinci, in banda kuka ba abunda take yi, tun ba ma da Dad ya gaya mata irin abubuwan data dinga yiwa Aslam d’inba, da irin rayuwar da yayi, gaba daya sai ta sake birkice musu, tana kuka tana cewa Aslam do yayi hak’uri ya yafe mata. K’arshe dai barin gidan ma yayi dan ba zai iya tsayawa tana kuka haka tana neman gafarar sa ba bayan ya san ba laifinta bane ba. Dad kanshi kasa zama yayi sai gidan su Abba yaje, ya d’an zauna yana dana sanin fad’a mata d’in da yayi. Sai dare aka samu damar kaita wajen Granpa, dan Gramma ita tunda taji labari ta taho itama suna tare ranar har dare. Ba yabo ba fallasa ya amsa gaisuwarta ya yi mata ya jiki. Ba abunda yake b’ata mishi rai irin yanda Gramma take ta faman yayatawa cewa “Ai Hudan ce ta bada shawarar yi mata sauk’ar Qur’ani kullum”. Har sai da ya kwab’eta ta hanyar cewa “Ta daina cewa ‘Huda’! Kawai ta dinga cewa Allah ne ya bata lafiya ya warkar da ita.” Gramma ta so yi mishi bayani, amman ganin kamar ranshi a d’an b’ace yake kuma ta son ba ya son jayayya yasa kawai tace “In sha Allah, Granpa. Zan gyara.” Tun daga kan Gramma har Aaima ba wanda bai bada zakka da sadaka ba na ban mamaki! Sauk’a kuwa ba su daina ba ana kan yi dan Dad cewa yayi “zuwa k’arshen watan nan ma in Allah ya yarda aka kammala na Mommy to ba dainawa za ayi ba duk sati sai an yi sauk’a a cikin eatate d’in a tsakanin su, in shaa Allah”. Yau kusan sati d’aya da warkewar Mommy, har su Hudan sai da suka zo suka yi mata sannu da barka a b’oye da daddare. Mommy tayi matuk’ar murnar ganin Sudais da Shuraim ita daman tana son twins, kuma tunda taji labarin suna da twins a family d’in taketa so ta gansu da su da Huda. Tunda Mommy taga Huda Allah ya d’aura mata k’aunarta, especially ma da taji gudummawar data bayar akan rashin lafiyarta.. Tayi mata godiya yafi a k’irga! Ita kam Hudan wani tsoron Allah da girman zatin shine ya sake shigarta, tana tunawa ko 2 month ba ai ba ta ganta a hargitse amman kalleta yanzu garau! Tabbas a rayuwa, in dai mutum yana neman sauk’i! Waraka! Taimako! To kuwa ya nema a wajen Ubangijin Talikai wanda bashi da kishiya. Da kyar ranar ta barsu suka tafi, ita Huda mamakin ma yanda matar take mata take yi, kamar ta santa tun daa chan amman da ta tuna yanda Mommyn ta bata labarin shak’uwarsu ita da Mama sai tayi tunanin ko saboda Maman ne yasa take yi mata haka.... Sannan itama a lokaci d’aya taji girma da k’aunar matar ya shige ta. A b’angaren Mommy kuwa, kawai tsintar kanta tayi da tsananin k’aunar Huda, dan koda bata kasance y’a ga Maryam ba tabbas Ubangiji ya d’aura mata k’aunar Yarinyar a ranta. Ba abunda yafi sosa mata rai irin da taji cewa ‘an sa ranar ta da Arshaad!’ Saboda ita har ga Allah tun da ta d’aura idonta akan Yarinyar ta fara kwad’ayin ganinta da Aslam d’inta a matsayin maaurata! Amman kuma da ta duba taga abunda yayi Aslam shi yayi Arshaad sai ta hak’ura ta barwa Allah komai sannan ta bisu da fatan alkhairi......................... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 50. Yau saura sati biyu auren su Hudan, sai shirye shirye ake yi. Yayinda jikin Mama yayi sauk’i sosai abun har mamaki yake bawa jamaa kamar ba wadda ta karye ba, follow up kawai take zuwa abunta. Abba da kanshi yaje ya siyowa y’arsa kayan d’aki na gani na fad’a, hatta cokali bai bari ba sai da ya siyo mata komai bayab ya tambayeta taste d’inta, wasu kuma yana daga chan d’in yake turo mata Sakina ta tayata zab’a. Sannan ya had’a mata gara nan ma na gani na fad’a. Lokacin da bikin ya rage saura sati d’aya already kayan gara da kayan d’akin amarya suna gidanta. Duk da ba wai zama za suyi anan d’in ba, kai ta kawai zaayi gidan daganan su wuce karatunsu amman hakan bai sanya an k’i yi mata kayan d’aki ba saboda time to time za su ke zuwa hutu. Shima Arshaad a nasa b’angaren hakan bai hana sa siyan gida ba! Daa a cikin estate d’in zai zauna amman da yake Granpa ya san Hudan zai aura haka nan k’iri k’iri sai ya hana sa gida! Da farko Granpa d’in cewa ma yayi ya bar mishi estate d’inshi, tun kafin auren! Da kyar Aslam ya lallab’ashi ya hak’ura amman dukda haka sai faman neman fad’a yake yi kuma fa sai da Dad ya tambayeshi tun farko lokacin kafin ma a saka rana amma sai ya nuna irin shi ba ruwanshi d’innan su yi abunda sukeso.. Yanzu kuma da bikin ya taho sai neman rigima yake yi yana neman abokin fad’a! Shiyasa kowa ya sha jinin jikinshi dan duk wanda yayi rashin sa’a ya yarda ya samu matsala da Granpa a wannan yanayin da yake, tou tabbas kashin shi ya bushe! Wannan dalili yasa Arshaad ya sayi gidanshi da kanshi daman kuma shi har ga Allah ya ma fi son ya yi komai da kanshi, dan da kyar ma ya yarda ya bari Daddy ya bawa Mommy mak’udan kud’ad’e take had’a mishi zazzafan lefe.. Gida kuwa da Abba yace zai siya mishi yi yayi kamar zai yi kuka, shi kuma Abban ya dage! Sai da Mommy ta saka baki tukunna Abban ya hak’ura ya bar Arshaad d’in ya sayi gidanshi mai hawa biyu d’aki bakwai da parlour hud’u har da d’an k’aramin bq a gefe a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96