Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

duk sai taji jikinta yayi sanyi, ashe ita kad’ai take ta shirmen ta. A hankali ta k’arasa wajen, kanta a k’asa. Har k’asa ta durk’usa ta gaida Dad, wanda cikin tsananin son yake yiwa y’ar d’anuwan nasa yayi saurin kamo ta ya zaunar da ita a kan d’an stool d’in da yake facing d’inshi, cikin kulawa ya amsa kafin ya hau tambayarta “ya kwanan bak’unta?” “Alhamdulillah” kawai ta iya cewa kafin ta juya ta hau gaida matar gefen shi har sau biyu amman ba alamun zata amsa kuma ta kafeta da idanuwa! Tana shirin sake gaidata a karo na uku ne Dad ya sauk’e ajiyar zuciya ya d’an dafa Huda tukun yace “Karki damu ba zata iya amsawa bane, amman ta fahimceki, tunda gashi tanata kallonki.” Yana gama fad’in haka ya juya ga Gwaggo Asabe jin tana cewa “ga breakfast, watak’il taci tunda naga yanzu jikin da d’an sauk’i, ko?” Shiru ya d’anyi kafin ya sauk’e wata ajiyar zuciya tukunna yace “Sai addua fa, amman Alhamdulillah, ni fa da Granpa zai yarda wallahi da an hak’ura da wannan theraphy d’in, saboda duk lokacin da akaje aka yi aka dawo ni sai inga kamar abun k’aruwa ma yake yi, kwanaki fa har hira tana yi, amman yanzu kiga gaba d’aya sai a hankali, danfa baki ganta last two weeks ba (Tym d’in da suka dawo. A Abuja), shiyasa ai na hanata dawowa nan, da kyar fa da addu’o’i tukunna abun yayi sauk’i ta dawo hakan.” Ajiyar zuciya Gwaggo ta sauk’e kafin tace “nima dai gaskiya na dad’e da lura, magana ce kawai banaso.” Cikin d’an fad’a Dad yace “Ai kuwa ta gama theraphy! Dan a gaskiya, ko ance za aje, sai dai In kaita Abuja kawai muyi sati mu dawo, abu ba fad’ar Allah ba amman an maidashi kamar dole!?” Kwalla Gwaggo Asabe ta share sannan tace “Ai shima Granpa d’in naji yana cewa ‘daga wannan an gama’.”Cikin katseta Dad yace “ai tun last year yake cewa ‘daga wannan an gama daga wannan an gama’! Amman an kasa gamawa da gasken.” Ajiyar zuciya Gwaggo ta sauk’e ranta duk ba dad’i da yanayin y’ar uwarta ta…. A hankali ta durk’usa ta fara serving abincin cikin mutuwar jiki. Hudan itama duk jikinta yayi sanyi dan haka tace “Allah ya bata lafiya”. A hankali Dad ya d’an juya ya kalle ta sai kuma yace “Ameen” cike da jin dad’in adduar tata. Juyawa yayi ya kalli Mommy, gani yayi har yanzu Hudan take kallo, kamar tanaso ta tuna wani abun.. Bai gama fahimtar yanayin ta ba yaga ta d’aga hannunta sannan tayi amfani da yatsar ta manuniya wajen sai da Huda! Gaba d’aya hankulansu kanta ya koma, cikin rawar murya kamar ta mai koyan magana sukaji tace “Aaa-sllam, ttanna kama ddda Aasllm d’Ina” Ba Dad ba hatta Gwaggo Asabe sai da gabanta yayi wani irin mahaukacin fad’uwa!!! Rabon da Mommy ta kira sunan Aslam, tun kafin ta fad’o daga bene! Gaba d’aya rawa jikin Dad ya d’auka, a hankali ya sa hannu ya juyo da fuskarta, ya kalli cikin idanunta sannan yace “Kina so kiga Aslam d’in naki?” Da sauri ta hau d’aga mishi kai, sai kuma hawaye, shaaarrrr suka zubo mata. “Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!” Shine abunda Dad ya dinga maimaitawa, cikin kid’ima ya mik’e ya fita yana cewa “su Gwaggwon su tsaya gashi nan zuwa, kar kowa yaje koina.” Ba ayi minti goma ba sai gashi ya turo k’ofa, rik’e da hannun Aslam Abba yana binsu a baya! Cikin zumud’i yace “Ga Aslam d’in naki” ya fad’a yana tunkarar ta, yana cewa su Abba “komai yazo k’arshe in shaa Allah, Aslam yau da kanta ta kira sunank.........” Razananniyar k’arar da ta fasa ce ta hanashi k’arasa maganar tashi, ta kuma rud’a duk wani wanda ke a cikin d’akin!! Basu ida dawowa haiyyacinsu ba ta kuma sakin wata k’arar! Wadda kusan rabin estate d’in sai da aka ji!. Cikin tsananin tashin hankali firgici kid’ima da tsoron da ya baiyyana k’arara a kwayar idanunta take nuna Aslam d’in tana kururuwa! A kid’ime Dad wanda duk ya rud’e ya sake nufota still yana rik’e da hannun Aslam wanda ya sake shiga tsananin tashin hankali da rud’ani don shi Dad ce mishi yayi “yazo Mahaifiyarsa tana nemanshi yau da kanta!” Gashi yanzu kuma ya tarar da haka!…. K’arar da ta sake saki ne ya kid’ima su dan tafi ta ko yaushe! Sai kuma ta saki jiki rigif ta fad’i sumammiya akan gadon….. Da sauri Aslam wanda idanuwanshi suka kad’a sukai jaa over, ya k’arasa inda take ya hau jijjigata yana kiranta amman bata motsi…….d’ago jajayen idanuwanshi yayi yana kallon Dad. Gaba d’aya sai Dad d’in yaji tausayin su, su duka ukun ya lullub’e shi.. Abba ne yayi k’arfin halin zuwa inda suke, yad’an kura mata ido kafin ya cewa Gwaggo Asabe “ta mik’o mishi ruwa!” A hankali yake yayyafa mata ruwan, har sun cire ran zata farka sai kuma sukaga tana motsi da idanunta alamun zata farfad’o…. A hankali Abba yad’an kalli Aslam wanda ke zaune a gefenta ya rankwafa kanta sannan ya kama hannunta gam!! Yana kallon idon da take k’ok’arin bud’ewa, alamun a kag’e yake yaga ta bud’e idanun nata! Da kyar Abba ya tattaro courage d’in da ya iya cewa Aslam “Aslam, ko zaka d’an je waje ko? Kar ta farka kuma ya zamana kai d’in zata fara gani.” Da sauri yace “No Abba, I think bata gane ni bane ba.” Sai kuma ya kalli Dad yace “Dad da kanta ai kace ta kirani ko?” Ganin da Dad yayi Aslam d’in na neman koma musu wani firgitachche ne ya sanya shi kawai cewa “Kaje wajen tukunna mu gani.” Jikinshi har wani karkarwa yake yi, sai da Dad ya sake cewa “I’m so sorry Aslam, ita tace a kiraka but ban san me ya sake faruwa ba kuma, for now just, ka d’an jira a waje ko?” A hankali ya cika hannun ya mik’e ba tare da ya yarda ya had’a ido da kowa ba ya fice, Dede nan Dad ya fashe da kuka, gaba d’aya sai hankalin su Abba ya sake tashi, saboda abune wanda basu saba gani ba! Don haka duk sai suka hau bashi hak’uri suna tausar shi, tare da adduar in shaa Allah Allah zai bata lafiya soon… A b’angaren Dad shi kuma Aslam yake ji, da ya sani da bai yi saurin kiranshiba, gaba d’aya duk sai yaji ya tsani kanshi….. Da kyar suka samu ya tsaida kukan ya k’arasa gurin Mommy wadda ta farka yanzun tanata faman dube dube a mugun tsorace alamun neman tsari take daga sake ganin Aslam d’in. Sai da komai ya lafa sannan Gwaggo Asabe suka fito ita da Hudan daga d’akin…. Ita dai Huda gaba d’aya kanta ya kulle, hakan yasa ta kasa hak’uri ta hau tambayar Gwaggo “meke faruwa? Mai ya sameta take haka? Tun yaushe? An yi mata sauka?” Dan ita Huda har ga Allah kawai ta fi jirkita akan lamarin na iska ne, tunda gashi dai ita da kanta ta tambayeshi but yana shigowa gaba d’aya ta firgice! Tayaya uwa zata dinga gudun d’anta haka?? Don ko ba a gaya mata ba ta gane itace Mahaifiyar Aslam ko dan yanayin kamar da suke yi da juna! But why him? Him alone?” Ajiyar

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});