Chapter 22
Chapter 22
suka k’arasa cika ita da Mommy shi kuma ya shiga masallacin ana idarwa Granpa yace “su wuce side d’inshi, ko gidanshi bai bari ya lek’a ba................ BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 38 Sai da Arshaad ya dawo daga masallaci ‘sallar isha’ tukunna ya lura babu Mammy a gidan. A bakin cook d’insu ya ji komai bayan ya tambayeta. Da kyar ya iya controlling kanshi dan ya san idan yace zai samu Abba ko Daddy a wannan lokacin a yanayin da yake ciki to tabbas za a samu matsala…. Dafe kanshi kawai yayi ya sallami cook d’in. Ya dad’e a tsaye! Bai ma san ta ina zai fara ba! Dan haka kawai ya sake komawa d’aki ya kwanta…. Da kyar kuwa ya samu ya iya rintsawa a daren ranar. WASHEGARI. Sai bayan sallar isha, tukunna Granpa ya nemi ganin Huda Abba Gramma Daddy da Dad, wanda dawowarshi kenan ya tarar ana sallah dan haka ya kira Gwaggo suka k’arasa cika ita da Mommy shi kuma ya shiga masallacin.. ana idarwa Granpa yace “su wuce side d’inshi”, ko gidanshi be bari ya lek’a ba............. A tare su duka hud’un suka iso parlourn Granpa. Ba tare da b’ata lokaci ba ya d’au waya yayi kiran Gramma yace “su zo ita da Huda!” Hijabin Gramma na salla mai hannu Hudan ta zumbula a kan abayar jikinta. Bayan sun fito Hudan ta bisu duk ta gaidasu..cike da kulawa duk suka amsa mata apart from Granpa wanda ya kauda kai gefe! Tana k’ok’arin zama a k’asa Abba yayi saurin jawota ya zaunar da ita a kan kujera kusa da shi sannan ya hau tamabayarta “how is she?” Tana shirin yin magana Granpa yayi gyaran murya! Sai da ya lura hankalin kowa ya dawo kanshi, sannan cikin serious voice d’inshi na tsoffi ya fara magana “Na san kowa a nan ya san abunda ya faru! Da kuma wannan Yarinya da Abba ya kawo yace ‘y’arsa ce’! Although ga kamanni nan na gani kuma su Ummi suma sun tabbatar da hakan, but dukda haka i need proof! Saboda ko dan abinda akace su Ummi sun yi jiya ya sa na saka jin ba zan iya trusting family members d’ina ba ma akan komai talkless of Maryam! Na lura ba zata iya hak’ura da Abba ba so she can do anything, zata iya tricking su kansu su Ummi d’in ta jira for years tukunna ta aiwatar da plan d’inta. Wannan dalili yasa jiya aka d’au sample d’inta da kuma na Abban wanda ya nemi yayi mini rashin kunya bayan na kirashi za a d’auki jinin nashi! He looked at me yana cemin ‘ko da ace The girl is not his, shi already ya riga yayi accepting nata, so tests d’ina babu abunda zasu saka ko su chanja!’.” Shiru Granpa yayi ya d’an sauk’e ajiyan zuciya sannan yaci gaba “Idan nace muku na tsani Maryam!!! Sai ku dinga ganin laifina….. jiya kawai ya ganta suka had’u amman har ya zama mara kunya mara mutunci!!! I’m pretty sure inda ace bai ganta ba to da ba zai iya gayamin maganar da ya gaya mini ba!! He even hit his wife! Saboda kawai giyar ganin wannan matar yana yawo a jikinshi…. Anyways duk ba wannan ne ya zaunar da mu anan ba!. Abba, inaso ka sani ko da ace zan yi disowing d’inka kamar farko, i’ll make sure Maryam bata lik’a maka y’ar da ba taka ba! Shiyasa na saka aka yi DNA and results d’in sun fito positive, so she’s your daughter, although na san you don’t need it!. Magana ta anan itace …. 29 years ago!!! Na fad’a maka na fad’awa Maryam cewa ‘I’ll never accept her and her children!!’ Dan haka wannan Yarinyar”yayi maganan yana nuna Huda, sannan yace “Kasancewarta y’a ga Maryam hakan ya sa she cannot live with us in this estate!!!!. Kana da two options Either ka mayar da ita wajen Maryam Or You are free to leave this estate and family, with her Forever!!!.” Yana gama fad’in haka ya koma yayi lamooo, a kan luntsumemiyar sofar da yake kai. Shiruuuu, parlourn ya d’auka, baka jin komai sai sheshshekar kukan Huda. A hankali Abba ya mik’e rik’e da hannunta har yanzun.. Gaban Granpa suka je suka durk’usa sannan ya fara magana “Granpa bani da bakin da zan yi maka godiya akan irin abubuwan da kayi mini tun haihuwata har kawo yanzu, ba zan tab’a iya biyanka ba sai dai In kamanta! Ko da ace kai ka cire Ni a cikin y’ay’anka Ni ba zan tab’a iya chanja uba ba! You’ll forever remain my Dad that same Dad that loves me so much! Wanda son zuciyata ya sanya a yanzu bana jin akwai 10% out of 100 na son da yake yi mini. Na san ba lalle ka iya finding place a heart naka kayi forgiven d’ina ba, but i’ll keep on apologizing till the end of time, I’m sorry, so sorry, very sorry! Dan Allah kayi hak’uri ka yafe min.” Yana gama fad’in haka ya mik’e ya mik’ar da Huda itama sannan yace “Hudan and I are leaving!! Good bye.” Da sauri Huda tace “Dan Allah kayi hak’uri, ka zauna da su, ni zan koma wajen Mamana, na ma fi son wajen ta akan nan, kar kuyi fad’a saboda ni dan Allah!”. Abba bai saurareta ba sai ma k’ok’arin janta da yake yi, dan so yake yayi sauri ya bar parlourn baya so su had’a ido da Gramma. Ya juya kenan yaga Daddy a tsaye! Bai gama tunanin me ya mik’ar da shi ba yaga ya k’araso inda yake ya rik’e free hand d’inshi! D’agowa yayi yana kallonshi da jajayen idanuwanshi, ganin Daddyn shima shi yake kallo ya sanya shi cewa “Don Allah kar ka ce komai, ka san ba zai tab’a chanja decision d’inshi ba, ni kuma ba zan iya barin y’ata taci gaba da zama a gidan wani ba! Please don’t stop me.” Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e, kafin yace “I’m not trying to stop you Abba. I’m coming wit you!!.” Da sauri ya kalleshi sannan ya juya ya kalli Granpa wanda ya lumshe idanunsa yana nan kishingid’e kamar mai bacci. Shima Daddy juyawa yayi still rik’e da hannun Abba yana kallon setin Granpa sannan ya fara magana “Granpa! Laifin Maryam da Abba bai kamata ace ya shafi Yarinyar nan ba! Bafa mu ma santa ba, bamu san ma tana existing ba, ta taso ba tare da kulawar d’aya daga ciki mu ba. I think yanzu lokacine da ya kamata ace mun yi welcoming d’inta warmly + mu nuna mata gatan da bamu nuna mata ba a baya! Bawai a hukuntata a kan laifin da iyayenta suka aikata ba wanda yaci ace yanzu ka yafe tunda Abban da Maryam d’in sun dad’e da rabuwa!!. To be honest Granpa What you have been doing is not right!! Kawai muna yi maka biyayya ne because we respect and love you as a father! But it’s like abun yana neman yin yawa! Tunda gashi kana k’ok’arin kai Abba wuta! Ko baka tunanin Allah zai tambayeshi hakkin y’arsa akanshi ranar gobe k’iyama?? What you are about to do is wrong! Very wrong!! Dan haka i think it’s about time da ya kamata mu fara fad’a maka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96