Chapter 37
Chapter 37
yayi sai ya kulle Usman kuma yayi shariah da su!” Daga k’arshe yace musu “Dan haka, ko kotun da Madu yake ik’irarin zai je sai dai ya kulle kanshi da kanshi dan wannan dalili kad’ai ya isa a barma Abba custody d’in Huda!.” Yana gama fadin haka shima yayi musu sallama cikin girmamawa ya wuce ya koma mota Auwal ya ja suka yi gaba suka barsu a wajen, daman su su Abba sun dad’e da wucewa. Tunda suka shigo gidan Huda take bin had’add’en mansion d’in mai hawa biyu da kallo! Har Aslam ya gama parking bata sani ba, sai da yace “Na bud’e lock d’in, ki fita sai kin fi jin dad’in kallon!” Tukunna ta dawo hankalinta, gaba d’aya kuma sai kunya ta lullub’eta. A hankali tasa hannu ta bud’e ta fito, still mutane waenda suka kwashe kaya daga chan gidan sunata kai kawo, da alamun basu gama jeran ba, dan gashi har sets d’in kujeru wasu ba a shishshigar ba. K’ofar shiga gidan biyu ne manya manya! Kamar yadda Dad ya fad’a gidan wajen zaman mutum uku ne ma amma k’ofar farko ta gefen dama yafi girma dan wajen d’akuna sha biyar ne da faluka bakwai (shine mutum biyu zasu iya using dan hatta kitchen biyu ne) Sai d’ayar k’ofar gefen hagu ta d’an gefe kad’an na d’auke da 7 bedrooms da 4 parlourns. Mai girman Abba ya d’auka Daddy kuma ya nufi d’ayar k’ofar (side d’in mutum d’aya wanda bai kai na Abba ba). Suna shiga Hudan ta kusan daskarewa… Dukda gidan chan estate d’in shima yana da double height ceiling amman ko rabin wannan bai kai ba, ga wata mahaukaciyar chandelier da tunda take bata tab’a tunanin akwai irinta ba, wasu irin kwayayene da suke k’ok’arin makantar da ita tsabar haske a gidan! Waiting parlour yana a ta gefe a cikin wani d’an glass door kafin ka k’arasa shigowa makeken main parlourn k’asa wanda girman parlourn zai iya cin set d’in manya manyan kujeru 6 ko bakwai! Gefen dining daban, sai wata had’add’iyar matattakalar bene doguwa da zata kaika sama. K’aramin Kitchen d’in na ata gefen waiting parlour kana iya hango cikin shi dan bangon half ne bai kai har chan sama ba Main kitchen d’in kuma yana ta gefen dining Amman shi rufaffiyar k’ofa babba gareshi. Akwai wasu k’ofofin still a cikin parlourn wanda take da tabbacin d’akuna ne. Sama suka yi gaba d’ayan su, Parlour ne nan ma biyu d’aya a gefen dama d’aya a hagu masu masifar kyau, dukda basu kai na k’asan girma ba saboda double height ceiling d’in da aka yanka ya cinye kusan 1/3 d’in saman amman suma sun had’u sosai ba a magana! pop kam kamar ka kirashi ya amsa ta jikin bango ta ceiling hatta k’afar bene shima ba a barshi ya huta ba. Wata matattakalar suka sake bi suka hau chaan sama. Suna hawa suka nufi side d’in su Sudais, d’akunan su da parlourn su yayi matuk’ar burgeta. Sudais yanata murna Shuraim kuwa miskili bai ce komai ba Sudais shi a shirmen shi ya d’auka har da Huda, dan haka ya hau tsarawa ‘Za su d’auki d’aki daya ita kuma ta d’auki d’aya, sannan ya cewa Abba “ai da anyi mata nata gadon pink ba kalar blue ba”…’ Dariya dukkansu suka yiwa shirmen shi, kafin Abba yace “a’a ita nata d’akin daban ne bara in kaita in dawo ko?” Yana shirin fita yaji Shuraim yace “Abba yaushe Ummin zata dawo? Gramma tace za kaje ka d’auko ta” A lokaci d’aya duk suka d’auke wuta.. Gaba d’aya duk sai Hudan taji ba dad’i, yadda taga Abba ya had’e rai ne yasa ta kasa cewa komai “Bana son yawan tambaya!” shine abunda yace daga nan ya fice daga d’akin. Ganin haka yasa itama Hudan tayi musu sai anjima ta fice.. Tanata kallon parlourn nasu har ta fita, ta jaa musu k’ofa ta rufe. Sai a sannan Abba yace “tazo suje ya kaita d’akinta” yana mai kama hannunta. A gefen parlourn da suke a ciki suka shiga wani dogon corridor, k’ofar tana achan k’arshe suna isa ya sa hannu ya zura key ya murza k’ofar ta bud’u! Sanna ya jaa hannunta suka shige ciki. Set d’in kujeru biyu ne Peach da black, sai wani d’an k’aramin dining mai mugun kayau mai d’auke da kujeru biyu a gefe, da wata had’add’iyar tv babba mai curve. Wucewa sukayi suka shiga bedroom a nan ta sake shiga mamaki, gadon nata pink ne mai rumfa da net a jiki (princess tent) ga wasu had’add’un resting da coffee chairs guda bibbbiyu a kusa da tvn bedroom d’in, fad’ar had’uwar d’akin kawai sai wanda ya gani! Kawai. Still toilet d’inta ya nufa da ita don ya nuna mata… Ta closet suka bi kafin su isa cikin toilet d’in A nan kuwa ta saki baki, wajen wanka har uku shower da wani had’add’en jacuzzi, sai kuma wani makeken bathtub da mutum hud’u ma za su iya shiga su kwanta kamar gado da Showers a jikinshi ta ko ina. Ba abunda yafi bata mamaki irin wutan pop da take gani na sama, da taga yana ratsowa ta k’asan toilet d’in toilet d’in ta ko wanne angle. Bata gana dawowa dede ba , taji Abba yana cewa “Duk abunda bai yi miki ba ki fad’a sai a chanja! Munata sauri ba a samu anyi komai a nutse ba, so if you need anything just say it sai a chanja miki ko a siyo, an d’an zab’a miki kad’an jiya kayan suna mota mostly abaya ne da shoes da sauran y’an abubuwa, zan kawo miki tab zuwa anjima, sai kiyi shopping duk abunda kike buk’ata, in kuma a furnishing akwai abunda kikeso ki fad’a shima sai a kawo.” Ita dai mamakine ma ya hanata yin magana, wai A nan d’in amman still ana tambayanta ko akwai wani abun da takeso a kawo! Girgiza kai kawai tayi, kafin tace “Abba na gode komai yayi Allah ya k’ara Arzik’i. “ A hankali ya dafa kanta yana mai jin tsananin kaunar y’ar tashi tana ratsa ko Ina na jikinshi sannan ga tsananin tausayinta da ya hanashi sukuni! Ji yake kamar yaje ya kama Usman yayita dukanshi har sai yaga baya numfashi tukunna ya kyaleshi! Jiya yanda yaga rana haka yaga dare tsabar bak’in ciki… Jin yadda zuciyarshi ta fara tafarfasa ne yasa ya kawar da tunanin yace “Ki huta bara a kawo miki tab d’in da kayan, anyi order abinci shima na san kafin ki gama freshining up ya zama ready sai ki sauk’o muci ko?” D’aga mishi kai kawai tayi ta kasa d’ago kanta, saboda kwallar da ta tarar mata! Dan tana ganin inda aka kawota a matsayin mallakinta Mama ce kawai ta fad’o mata…… A tare suka fito daga toilet d’in suka shigo d’aki. Ganin Abba yana shirin fita yasa tunanin ta ya katse tayi saurin cewa “Abba” Juyowa yayi yana kallon ta. A hankali ta k’arasa wajen da yake sanna tace “Dan Allah Mama, mun yi waya da Sakina tace min Maman tana asibiti tun shekaran jiya”ta k’are maganan hawaye na zubowa daga idanunta. A hankali ya kama hannunta suka k’arasa bakin gadon suka zauna sannan yace “Zan kaiki wajenta anjima da daddare. Ki daina kuka” Da sauri tasa tafin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96