Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 56

Chapter 56

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kafin ya fara magana “Shikenan zamu gwada mu gani, amman idan mun yi nasara kin dawo wajen Maman naki to inaso kisan cewa Ba a inda take zaki zauna ba sai dai ki zauna a gidana! Saboda Usman ba zai tab’a bari ki ci gaba da zama nasa a gida ba sannan na san ba zai dinga barin itama Maman naki tana zuwa inda kike ba kwata kwata kinga kenan baki zauna da Abba ba kuma baki zauna da Mama ba!” Cikin kuka Mama tace “Abba dan Allah ka dai na, za ka karya mata guiwa” Murmushi ya sake yi kafin yace “Maryam hakan shine gaskiya! Kuyi hak’uri, for the first time nayi miki alk’awari ban cika ba! In dai zan fad’a miki ki ji, tou inaso dan Allah ki bar Yarinyar nan ta koma wajen Mahaifinta kamar yadda ya buk’ata, ko munje kotu ya fimu gaskiya, kuma rashin hankalin da Usman ya sake yi yau d’innan ma wata shaida da point ne Abba ya sake samu. Ki barta ta tafi, za ku dinga waya sannan yace anytime kike son ganinta kije ki ganta, idan ma bakya son zuwa gidan nasa to zai saka ko driver ne ya kaita ko wani park ko restaurant, ku had’u achan amman yace ba zai sake barinta tazo inda kike ba! Har ga Allah Maryam, Abba is trying to be just here.” Da sauri ta d’ago tana kallonshi da jajayen idanunta. D’aga mata kai yayi alamar gasgata mganar shi, kafin Baba Bashir ya d’aura da cewa “Maryam har yanzu zuciyar ki a k’ulle take da zafin abunda Abbas ya aikata miki, shiyasa ba za kiga abinda mu muka ganiba, wanda muma a da bamu ganshiba sai bayan da muka yi k’ok’ari muka goge takaicin shi daga idanuwanmu.” “Mune muka haifeki, baki da masu fad’a miki gaskiya sama da mu, ki tashi ku tafi suyi miki kwatance ki kaisu ki dawo, dama haka rayuwar take, ba komai kake kwallafawa rai kuma ka samu ba, ki bari ko nan da wata biyu ne haka, sai a san abun yi kinji? Yanzu kuje kawai.” Hudan ke kuma idan kin koma, ki san yanda za kiyi mishi magana a samu ya saki Babanku Usman kinji?” Cewar Shuwa. A hankali Mama ta rintse idanuwanta wasu zafafan hawaye suna zubo mata! Ta manta rabon da Shuwa tayi mata magana mai tsayi haka. Bata dawo daga duniyar tunanin da ta tafi ba, taji Sakina ta furta wasu maganganu da suka girgizata matuk’a! Wai “An saka ranar Huda nan da wata biyu da Arshaad!!” Ba Mama kad’ai ba, gaba d’aya parlourn shiru ya d’auka! Chaaan! Shuwa tace “Allah ya sanya albarka” Da sauri Mama ta kalle ta da idanunta hawaye shab’e shab’e! Kasa jurewa Shuwan tayi kawai ta mik’e ta kama hanya ta fice… Baba Bashir ne yace “ku tashi kuje Maryam, za muyi wannan maganar wata rana!” Cikin kuka Mama tace “Kaka, Abba Naji zan barta ta koma amman dan Allah kar ku saka na maida ita, ba zan...” Kukan da ya kufce mata ne yasa ta kasa ci gaba da magana ta mik’e ta fice tayi cikin gidan… Baaba Talatu ce ta bita domin lallashin ta. Wannan shi ake kira isa da mallaka!!! Tayaya zaka sa ranar Yarinya ba tare da tuntub’ar Mahaifiyarta ba? Saboda Allah fa!. Shiruuu, parlourn ya d’auka, chaan Kaka yace “su mik’e su kai su” Ita Sakina tausayi ma y’an tsofaffin suke bata, sun tsufa amman har yau basu huta ba, bayan jigilar case d’in y’an unguwa ga na family…ta tabbatar yanzu suna maida su, police station zasu wuce, akan case d’in Baba……….. A k’ofar tafkeken mansion d’in da suka isa da taimakon kwatancen Sakina suka yi parking, daganan suka yi musu sallama, da d’an Guntun maganganu tukunna suka wuce, su kuma suka shige ciki. A parlourn suka tarar da Abba, Daddy har Dad da Arshaad! Da alamun maganganu suke yi masu mahimmanci. Yadda Hudan ta baro Mama tana kuka yasa ta d’an ji zafin Abba! A hankali suka gaidasu, bayan sun amsa bata tsaya ba kawai ta haye sama! Har sai da Sakina ta d’an yi mata magana bayan sun hau, dan taga kamar basu ji dad’in yadda tayi musu d’in ba. Ko lunch k’in sauk’a tayi, ba yanda Sakina batayi da ita ba amman tak’i sauk’a, gashi Abba sai kira yake a waya tana amsawa tana cewa “Huda sallah take” Kamar minti ashirin haka, suka ji knocking. Sakina ce tace “Come in” A tunanin ta ko maid aka turo ta kawo musu abincin. Turo k’ofar yayi ya shigo, Sakina bata san lokacin da ta fara dariya ba ganin Abba ya shigo har da hular kuku a kanshi da basket d’in abinci a hannunshi. Harararta yayi, ya d’aura yatsanshi akan lips d’inshi alamun tayi shiru! D’aga hannuwanta sama tayi tana gimtse dariyar tata, sannan ta mik’e ta fice da sauri. Sai da ya ajjiye kular, sannan yace “princess” Shiru tayi still tana kwance ta bawa k’ofar baya. Chan taji yace “Hudan” A hankali ta mik’e ta zauna ta juyo tana goge hawayenta, fuskarta tayi jaaa alamun taci kuka, over!! Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya zauna a bakin gadon, yayi hugging d’inta ya fara lallashinta ai kuwa kamar jira take ta saki kukan babu control. Bai hana ta ba, sai da ta gaji dan kanta tayi shiru tukunna a hankali yace “sorry dota, i’m really sorry, ok?” Cikin sheshshek’a tace “Abba Mama na da bp, yanda na baro ta tana kuka, Allah zai iya tashi?” Murmushi yayi yana sakinta kafin ya gyara zamanshi yana kallon k’ofar fita tukun yace “Hudan, na fiki jin zafin kukan da Maman ki take, please don’t question my decision, it’s the right thing.” Ahankali tace “Amman Abba pls...” “Shhhhhhh” Yace ba tare daya kalleta ba, kafin ya juyo ya fara k’ok’arin zuba mata abinci. Omelet d’in da ya soya mata ya saka a gefe, da pizza slice uku da ya d’auko. Da farko k’in ci tayi sai da yayi dagaske, tukun ta d’an karb’a. Bayan ta gama ta sha ruwa, ya d’an dunga janta da magana yana ta faman lallashinta. Hudan bata iya dogon fushi da mutum ba, don haka ta d’an sauk’o, hakan kuwa yayi matuk’ar ragewa Abba kusan 20% na damuwar da yake ciki shiyasa da ta rok’esa akan ya saki Baba ba don halinsa ba sai dam kakanninta da hankalin su yake a tashe! Abban ya amince, a take ma a gabanta yayi waya yace a sake shi. Ta ji dad’i sosai kuwa. Daganan suka d’an ci gaba da maganarsu. Hammar da yaga tanayi ne ya sanya ya fahimci bacci take ji, dan haka yace mata “ta kwanta” Bata yi 10 minutes da kwanciyar ba ta fara bacci…. Ahankali yake kallonta yana tunani kala kala… Sai bayan kusan 1 hour tukun ya rage mata k’arfin ac ya lullub’eta da bargo, sannan ya fita da kayan abincin............... A chan parlourn k’asa kuwa, sam Sakina bata lura da Auwal wanda ya daya dawo break ba, sai da ta kusan k’arasawa dining d’in! Tun kusan sauk’owarta yaji a jikinshi! Addua yake Allah yasa itance, don haka ya k’urawa stairs d’in ido… Ba a hankali take tafiyarta ba ba kuma da sauri ba! Da d’an murmushi a kan fuskarta. Gaba d’aya

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});