Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 40

Chapter 40

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,209 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Hudan ba zata auresaba!’ Wai wanne irin rainin wayo ne ma wannan Abba yake yi wanda kika kasa fahimta??? Kina ganifa yadda muka taso muka sha wahalar rayuwa tare, bai tab’a ko da lek’en ta ba, sai yanzu data zama mutum tukunna shine zai nuna ya santa? Inace daa cewa yayi ‘kar ma in fad’a mata sunanshi?’.” Dafe kai Ummu tayi tana shirin yin magana Huda tace “Mama da gaske yake tun ranar anan ya fad’a miki ‘bai san da ni ba!’ Kuma dagaske yake.” Cikin jin haushi Mama tace “k’arya yakeyi!! Na fad’a na sake maimaitawa ‘k’arya yake yi!’ Kinji mai uba! To nuna min shine ya haifeki kinji Huda, hakan yayi kyau! Wato d’an kwana biyun da kika yi tare dasu har an juya miki tunani akaina ko? Bilkisu kinga irinta ko? Ina kuma ga in na barta ta zauna dasu gaba d’aya? Hudan fa ita kad’ai Allah ya bani, amman kalli mugu Abba abinda yayi a cikin kwana biyu kawai!!.” Ta k’arashe maganar tana fashewa da kuka. Da sauri Hudan ta hau lallashinta sannan ta fara basu labarin yadda akayi da Mom da su Ummi da Mammy, har cell d’in da suke ciki a yanzu…. Ummu wani sanyi da proud na Abba take ji, kuma ta sake amincewa zai kula da Huda iya iyawarshi kuma zai yi duk iyakar bakin k’ok’arin shi wajen bata kariya. Amman wani abun mamaki furr!! Mama tak’i amincewa da zancen tace “Makirci ne suka k’ulla da shi da y’an uwan sa, aka yi komai a gaban Huda dan ta yarda dashi asa ta juya mata baya!” Ba Ummu ba hatta Sakina da Huda da basu da shekaru sosai, sai da suka tsorata da lamarin Mama, ga gaskiya nan ana nuna mata amman ta kafe! Tak’i ji taki gani.. Ummu har ce mata tayi “zata je suyi maganar fahimta ita da Abba, ba sai anje kotu ba! Kawai Huda za ta dinga sati sati a hannunsu, har Allah ya kawo mata miji tayi aure Ma’aana taje Gandu tayi sati d’aya sai ta koma Nasarawa tayi sati daganan ta sake dawowa Gandu….haka dai.” Amman nan ma furr!! Mama nace akan ‘attakafur!! Ita sai dai a bata Huda gaba d’aya!’ K’arshema cewa tayi “idan Ummun ba zata tsaya mata ba ta daina yi mata kwana kwana kawai ta fito fili ta fad’a! Ta samu ta fara neman wani lawyer d’in, tun kafin lokaci ya k’ure mata.” Da jin hakan ne yasa Ummu taja bakinta tayi shiru bata sake cewa komai ba! Daganan shiru ya wanzu a wajen…. Hudan ce ta kawo k’arshen shirun ta hanyar cewa “Ya Jalila ma tana gidan” Da sauri duk suka zuba mata idanu… Cikin In Ina tace “Ciki ne ma da ita” A firgice Sakina ta rafka salati haka ma Ummu Mama kuwa daman ta riga ta Sani, amman abunda ya bata mamaki shine ‘me take yi a gidan su Abba’. Ummu ce tace “Me take yi kuma a gidan?” Shiruuu, Hudan tayi, bata san daliliba amman sai ta kasa ce musu cikin na Arshaad ne kawai tace “itama bata sani ba” Tana goge wani hawaye mai zafi daya zubo mata ba tare data bari sun gani ba, kafin ta k’ara da cewa “A gidansu Ya Auwal dai ta ganta, kuma yanzu da suka tashi, Ya Auwal d’in ya kaita wajen Gwaggo Asabe.” Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e kafin tace “Sadiya ta cuci Yarinyar nan har abada wallahi…” Cikin sanyin murya Huda tace “Ummu nace mata ta kwantar da hankalinta zan nema mata mafita, ya za ayi yanzu? Dan wallahi naji tausayinta..” Da sauri Mama tace “Wacce mafitar za ki nema mata?? Meye naki a cikin lamarin ciki, iye?” Ta k’arashe maganar cikin fad’a! Sannan taci gaba “Kin san Allah Huda babu ruwan ki a cikin lamarin nan, mafita Sadiya ta nema mata, wannan maganar tafi k’arfin ki kar inji kar in gani! Ballanta a tsunduma ki a cikin lamarin a yi miki bak’in fenti ke daman mai bak’in jini a idonsu…” Hawayen Hudan ne ya k’aru, ta sa hannu ta shiga gogewa.. Ita kad’ai ta san kalar tuk’uk’in da zuciyarta take yi mata, kawai tunowa da lamarin cikin da tayi And Tana mamakin masifar da Maman nata ta koya.” Ummu ce tace mata “kin dai ji ko Huda? Ki bita da addua kawai, Sadiya ta fiki sanin kalar taimakon da zata yi mata, ba ruwan ki! Dan yanzu za a goga miki fenti taki sai tafi ta kowa tsami!” Cikin katseta Mama tace “Ai gashi irin tarbiyyar Abban da kuke magana akai!! Yanzu kamar Hudan har tana shiga lamarin ciki tana alk’awarin zata nemawa mutum mafita sai kace wata nurse??!” Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e sannan tace “Ki kwantar da hankalinki, ai taji abunda muka ce mata ko Huda? Besides ai basa tare ma yanzu, naji tace tana wajen Gwaggo Asabe ko? Wacece Gwaggo Asaben?” Nan Hudan tace “k’anwar Mommy ce” Sannan ta basu labarin halin da Mommyn take ciki. Kaf a labaran da Huda tazo da su na Mommy ne kawai ya girgiza Mama. Ta ji ba dad’i sosai, gashi ta san matar sun d’an saba dan haka tayi ta jimami…ga shima Aslam wanda dukda kalar rashin kirkin da yayi mata ranar amman har yanzu tana jinsa har cikin ranta….. Kamar ance ta kalli wayar Sakina da message ya shigo yanzu ta d’anyi haske! Wayar na nan akan cinyarta don haka ta samu damar ganin time… Mamakine ya kamata dan har ta shafe wajen awa d’aya da minti ashirin a wajen. Cikin k’arfin hali ta d’an kwanta a jikin Maman, bayan kamar minti uku ta mik’e ta cewa Sakina “tazk ta rakata taje tayi fitsari.” Kamar kuwa Mama ta sani dan tashi d’aya ta fara k’ok’arin mik’ewa tace “bari ta rakata da kanta!” Da kyar Ummu ta lallab’ata, ta hak’ura ta koma ta zauna. Daganan Sakina ta gyara mayafinta suka rik’e hannu suka yi gaba…. Har suka fita daga wajen tana d’an juyowa tana satar kallon inda su Maman suke…..tun kafin suje waje ta fashe da kuka mara sauti suna fita harabar asibitin ta sakeshi mai sauti ya fito, da sauri Sakina wadda tun d’azu taketa ce mata “bafa nan bane hanyar toilet d’in” amman tayi mata shiru sai janta kawai take yi tace “Lafiya Huda mai ya faru kuma?” Waige waige ta hau yi, chaan ta hango motar Abba da suka yi parking d’azu! Daman bata yi tunanin zai tafi ba. Bata b’oyewa Sakina ba, nan ta fad’a mata komai akan yadda suka shirya da Abban nata. D’an k’ura mata ido Sakina tayi….Chaan! Tace “Yanzu sai yaushe kuma? Anyways kinga dai 30 minutes ya baki yanzu kuwa kin kusan awa d’aya ma. Ki kunna wayarki kawai za muyi magana. Mai yasa kika kashe ko kwacewa akayi?” A hankali tace “Charger ne babu. Amman d’azu na siya a online an kawo har na ma jona Ina so ya cika ne kafin In kunna.” “Ok za muyi waya muje in rakaki” Hannun ta Hudan ta ruk’o kafin tace “Sakina kina ganin Mama ba zata ji haushina ba? Me za kice mata idan kin koma ciki?” Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e sannan tace “Haushin ki kam za taji, ba d’aya bama kuwa! Kuma yau Allah yasa ta bar Ummu ta

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});