Chapter 62
Chapter 62
abunda Sakinan tace, murmushi kawai yayi ya girgiza kai suka bi bayan su… Ba kowa a d’akin sai Mama ita kad’ai tana zaune a kan gadon jinyar tata da littafin addu’o’i rik’e a hannun ta, tana karantawa tana d’an tofawa k’afar da akayiwa d’auri! Tsananin azaba takes sha, shiyasa gaba d’aya jikinta ma rawa yake yi…. Raunukan jikinta sun d’an sab’e, fuskarta ma ta d’an sab’e amman still har yanzu akwai bandej a goshinta wanda aka zagaye kan nata da shi aka d’aure a k’eyarta, ta d’an yafa k’aramin mayafi akan doguwar rigar jikinta saboda masu shige da fice but still kana iya hango dogon gashinta da Ummu ta gama tufke mata shi yanzu ta dunk’ule a k’asan bandej d’in kafin ta fita. Hudan ce ta fara shigowa sai Sakina sai Daddy.. Bata ganeshi sosai ba dan haka ta d’an tsaya tana d’an satar kallonshi A hankali yayi sallama ya shigo, suna had’a ido tayi saurin sunkuyar da kanta sannan ta rintse idanuwanta. Bata gama dawowa dai dai ba taji Daddyn yana yi mata ya jiki, kamar ba zata amsa ba sai kuma ta daure, “Alhamdulillah” kawai ta iya cewa. A hankali su Hudan suka je suka yi hugging d’inta suma suka yi mata ya jiki, da kyar ta iya amsawa. Sannan duk suka nema waje suka zazzauna. Tana jira taga Abba ya fita sai taga shima ya nemi waje ya zauna kafin a hankali muryarshi ta daki dodon kunnenta “Maryam ya jiki?!” Banza tayi da shi! Ya sake maimaitawa Nan ma tayi mishi banza!. Murmushi Daddy yayi kafin yace “Allah yasa kaffara ne, ni bara ni In wuce. Dota sai kun dawo” Allah kiyaye suka yi masa. Sai da yazo fita tukun Mama ta samu k’arfin halin cewa “An gode” Da murmushi yad’an kalleta yace “Allah ya sauwwak’e” daga haka ya fice ya bar Abba a nan zaune wanda bashi da niyya ko ranar tashi dan gyara zama ma suka ga yayi...... Kowa da abunda yake sak’awa a cikin zuciyarshi…..d’akin yayi shiruuu! A haka Ummu ta shigo ta samesu. Da murna suka hau gaisheta bayan sun je sun yi hugging d’inta. Cikin mutantawa suka gaisa ita da Abba Daga nan itama ta nemi waje ta zauna aka ci gaba da zaman kuramen da ita. A haka Baaba Talatu ta shigo ta same su, wadda ta zo tare da jikanta Autan Anty Zainab tsaran Sumayya da Sumayyar. Sumayya tana ganin Sakina taje ta fad’a kanta tana cewa “I miss you” Sai da Hudan ta dungure mata kai tukun ta juyo ta rungume ta tana cewa “Sorry, i miss you more” Dariya duk aka yi, Yaron Anty Zainab kuwa yana gaida Mama da Ummu ya koma gefe ya zauna, daman kaf a y’ay’an nata wadda aka yiwa aure kwanaki (Khadija) ita ce kawai suke shiri amman da babbar da autan duk uwar su sukayo. Tunda Baaba Talatu ta shigo taga Abba ta had’e rai! Hankalinta ba k’aramin tashi yayi ba har sai da su Maman suka lura da hakan. Wani abun mamaki ko gaisuwarshi k’in amsawa ta yi, haka ya yi mata har sau uku a tunaninsa ma shi ko bata ji bane, ganewa da yayi amsawarne ba zata yi ba yasa ya kyaleta. Hudan kuwa abun da taga ana yiwa Abban nata ya k’ular da ita sosai, dan haka ta had’e rai tana gaida Baaba Talatu ta d’auke wuta a d’akin. Su Baaba Talatu basu wani dad’e ba suka tafi. Sai da Abba yayi 3 hours tukunna ya mik’e ya yiwa Mama Allah k’ara sauk’i Ummu ce ta amsa Hudan kuma ta tafi yi mishi rakiya. Har suka je motar ba wanda yace komai. Sai da ya shiga ya zauna, tukun ya d’auko kud’i a cikin motar ya bata yace “ta rik’e, ko suna son siyan wani abun” Godiya tayi ta karb’a. Ganin ta rik’e murfin motar yasa yace “Akwai wani abu ne?”. D’an b’ata fuska tayi kafin tace “Abba In kayi musu magana sau d’aya suka yi shiru kawai ka dinga kyalesu”. Bai san lokacin da murmushi ya sub’uce mishi ba, ya ji matuk’ar dad’i da Hudan ta damu da mutuncinshi haka..dan haka yayi murmushi yace “To shikenan princess, na ji, in shaa Allah. Shikenan? Ko akwai wani abun?” D’an guntun murmushi tayi tace “babu” daganan ta rufe mishi murfin motar, yayi waving d’inta itama haka, ya wuce. Sai da taga fitar motarshi tukun ta koma ciki............ Satin Mama biyu a asibiti aka sallameta. A cikin sati biyun nan ba ranar da zata zo ta wuce Abba bai je ya duba ta ba. Kamar yadda Hudan ta gaya mishi kuwa sau d’aya yake yi mata magana in ta k’i amsawa ya kyaleta Baaba Talatu itama haka! K’arshema idan ya shiga jimla yake yi yace “Ummu sannun ku, ya mai jiki?” Daga nan shikenan… Sau biyu suka had’u da su Madu, dan su Ummu sun rok’esu akan su daina yawan zirga zirga shiyasa ba sosai suke yawan zuwaba! Yayi mamaki dan bai yi tunani idan ya gaishesun za su amsa ba, amman ga mamakinsa sai yaga sun amsa ba yabo ba fallasa! Yadda Baaba Talatu taga sun yi mishi hakan ya sake d’aga mata hankali dan haka suna isa gida ta d’agawa Kaka hankali akan su fito da Usman yazo a maida auren su da Maryam, ko kuma su fad’a mata inda yake taje ta sameshi dan ya kamata ya san halin da ake ciki! Dan ta ga take taken Abba so gara a maida auren su k’arasa rayuwarsu tare tun kafin Abba ya b’ullo da wani abun…. Da farko Kaka a hankali ya fara binta, ganin da yayi ba fahimta za tayi ba sannan kanta ya soma birkicewa ya sanya shima ya birkice mata ya fito mata a mai gidan sa! Yayi mata fata fata!! Tukun ya samu ta sarara mishi dan tayi mugun tsorata da shi. Auwal ma zuwanshi biyar, tun su Ummu basu fahimta ba har Sakina ta tonawa kanta asiri, dan yana shigowa zata had’e rai, ko kulashi ba tayi Hudan kad’ai ke gaidashi. Su su Maman ma dariya take basu, ganin basu ce musu komaiba yasa suka zuba ido kawai dan sun lura Sakinar bata ra’ayin shi kuma sun san da maganar yayan k’awarta Ashraff. Har da Abba aka rakata gida. Tunda aka bud’e gate d’in gidansu gabanta yake fad’uwa, dukda yanzu Shuwa har waya tana yi mata tana jin ya take amman ta san ba lalle ta huce gaba d’aya ba, tunda gashi ko asibiti bata zo ba..tana murnar mutuwar auren Baba a kanta matuk’a amma tana tunanin zaman da za suyi da Shuwa kuma ko ita ta kawo rashin kunya duniya ba zata je tace zata zauna a gidan Kaka ba….. Tana wannan tunanin motocin suka yi parking a harabar gidan, wani sanyi da iska take ji yana shigarta ta koina “gida mai dad’i” Ta fad’i hakan a k’asan ranta wani hawaye yana zubo mata. Abba bai tsaya ba, ana gama kwashe kayan dake motarshi yayi reverse ya fita. Ummu ce ta taimaka mata ta hau kujerar ta, daganan ta tura ta tayi ciki da ita, su kuma su Sakina suka mara musu baya. A parlourn suka tarar da Shuwa, ga mamakin kowa tana gani an shigo da Maryam sai ta fashe da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96