Chapter 5
Chapter 5
dan haka ba da gajiyar ba zata yi musu da sauk’i ba. Suna tsaye suna tunanin abunyi next suka hango su Ummu d’auke da mata suna nufusu, sai da suka matso su sosai sannan suka gane Mama ce. Basu samu damar tambayar su ba dan da sauri mai gadin k’ofar ya wangale suka shige kawai dukkansu… Ana ganin su aka karb’esu bayan an kawo gado an d’aurata, aka tura ta ciki don yin bincike.. Ba a jima ba sosai, Dr ya fito! Likitan dai da ya karb’eta jiya shine, magana d’aya ce ya maimaita musu “hawa da jininta yayi over ne ya janyo komai..amman this time around har eco za suyi” Nan yake ce musu “ba yadda bai yi da ita jiya akan ta zauna ta shanye drip d’inta ba amma tak’i, ta biyewa wasu suka dinga hayaniya suna fad’a! Yayi yayi akan suyi shiru suka k’i, shiyasa shi kuma ya sallameta, so suma in sun san hayaniyar za suyi gara karma su shiga inda take, dan zai sake korar su ne!”. Yana gama fad’in haka ya nuna musu inda take sannan ya wuce........ Bayan kamar awa d’aya, Kaka da su Baba suka wuce aka bar Sakina da Ummu. Su Kaka na fita Hudan wadda take kiran Sakina a kai a kai ta kira, nan Sakina ta gaya mata “sun ganta suna tare ma yanzu haka” Sai a lokacin hankalinta yad’an kwanta. Nan itama Sakinan take tambayarta “tana Ina?” Hudan tace mata “tana wajen Gwaggon su Aslam, amman still Abba bai san tana gidan ba, dan a b’oye ma Arshaad ya kawo mata wayarta data bari a gidan Gramma, so in shaa Allah gobe da sassafe za ta san dabarar da zata yi ta gudo.” shiruu, Sakina tayi chan tace “ki bari mu yi magana da Ummu tukunna, kar ki yi komai, kinji?” Ummun ce tasa hannu ta karb’i wayar suka yi magana da Hudan ta d’an kwantar mata da hankali, kafin suka yi sallama. Da kyar suka samu bacci ya kwashesu wajen k’arfe 3 na dare. Da sassafe su Madu da Baaba Talatu suka zo kawo musu breakfast, har lokacin Mama bata farfad’o ba. Sama sama take jin hayaniyar su dan haka ta fara k’ok’arin bud’e idanunta. Sakina wadda take a kusa da ita ce ta lura dan haka ta maida gaba d’ayan hankalinta gareta, ganin Sakina ta k’ura mata ido ne ya sanya suma duk suka taso suka zagaye gadon suna tambayar “mai ya faru?” Basu ida tambaya ba Mama ta k’arasa bud’e idanunta… Tsantsar farin ciki ne ya baiyyana a fuskokinsu gaba d’ayansu, cikin murna suka hau furta “Alhamdulillah” suna tambayarta “ya jiki?”. Da kyar Baaba Talatu ta taimaka mata ta mik’e ta zauna.. Tana zama suka had’a ido da Ummu! Kawai sai ta fashe da kuka abun tausayi…… Duk shiru suka yi. Da kyar Madu ya samu ya k’araso inda take ya dafa ta sannan ya d’an fara bubbuga bayanta alamun lallashi. Farin ciki ne ya mamaye zuciyoyinsu gaba d’aya, duk sai suka hau murmushi Kaka har da y’a kwallarshi, ya sa hannu share ba tare daya bari kowa ya lura ba. Ita kanta Mama duk da yanayin da take ciki hakan sai da ya sanyata zubar da kwallar farin ciki, dan rabonta da Madu ya nuna kulawarshi a kanta kaman haka, yau yau shekaru ashirin da bakwai kenan!. Share hawayenta tayi sannan ta d’ago ta kalleshi, shima itan yake kallo, ba abinda ta hango a idanuwanshi sai tsantsar tausayinta, bakinta na rawa cikin kuka tace “Abba, ya raba ni da Huda! Dan Allah ku karb’o min ita, wallahi mutuwa zan yi in ba y’ata, na shak’u da ita sosai, ba zan iya yarda in bar mishi ita ba.” Da sauri Ummu ta k’araso ta rungumeta, sannan cikin tsananin tausayinta tace “Ki yi hak’uri ki huta, munji komai, in kika warke sai a san abun yi, ki kwantar da hankalin ki dan Allah.” Cikin jujjuya kai Mama ta zare Ummu a jikinta kafin tace “Bilkisu ba zan iya yin hak’urin nan ba!! Abba ya zama wani irin mutum! Mugun mutun.. Shi ne fa ya turo Arshaad wajen Huda, Arshaad cousin d’inta ne! Suka dinga yaudarar mu, idanunsa akan mu yake all this time amman bai baiyyana kanshi ba sai yanzu? Saboda ko nace ba zata koma wajenshi ba ya san ai Arshaad zata aura, kenan ko? Wanne irin ubane zai yiwa y’arsa haka? Bilkisu gaba d’aya kaina ya kulle, a baya yace ‘baya buk’atar ta’, yanzu kuma yazo ya raba ni da ita a lokacin da nafi buk’atar ta, mai yasa zai yi haka? Laifin me na yiwa Abba da zafi haka??”. Ta k’arashe maganar tana mai fashewa da kuka. Lallashinta Kaka Baaba Talatu da Ummu suka hau yi, amman furr!! Tace “ba zata hak’ura ba! Ba zata iya yin hak’urin da suke so tayi ba, yanzu zata je ta taho da y’arta, barinta a hannun Abba danger ne! Tunda har ya iya turo wani wajenta saboda son zuciyarshi bai damu da yana sonta tsakani da Allah ba ko akasin hakan ba Tou tabbas zai iya yin komai. Ko bayaga haka ma idan duk duniya zata taru a kanta tofa ba zata d’auki y’arta wadda Abban yace ‘bayaso ta fad’a mata ko da sunan shi ne’ ba, ta bayar a shi yanzu! Sai dai duk abinda zai faru ya faru. Suyi mata kwatancen gidan ko kar suyi mata zata tafi ta nema, tunda Allah yasa taji kwarin jikinta yanzu, daman jiya ma jiri ne ya hanata motsawa daga inda take.” Gaba d’aya Mama ta hargitse musu, data ga ma ba zasu bata goyon baya ba, Sai ta fara k’ok’arin sauk’a daga kan gadon sannan tasa hannu zata cisge cannular hannunta. Madu ne ya rik’e hannun nata, kafin cikin lallashi yace “Maryam koma ki zauna muyi magana.” Cikin sheshshek’ar kuka ta koma ta zauna tana share hawayenta. Sai da yaga ta d’an sassauta kukan nata, sannan ya fara magana “Ki kwanta ki huta, baki da lafiya. Koda kin fita za ki sake fad’uwa ne, saboda baki gama dawowa normal ba! Ki zauna ki shanye allurai da magungunan ki, da ni da Babanku Bashir za muje mu samu Abba, in shaa Allah, kinji ko??” Da sauri Kaka yace “Za muje a yau! Ki kwantar da hankalin ki kinji?” A hankali taji kad’an daga cikin nauyin da zuciyarta tayi ya d’an sauk’a, dan haka ta d’aga musu kai alamar ‘to’ kawai, tana sharar hawaye. Ajiyar zuciya Baaba Talatu ta sauk’e, sannan ta nufi wajen kulolin da suka kawo ta zubowa Mama abinci ta kawo mata. Sakina ce ta karb’a ta fara k’ok’arin bata, amma sai ta kauda kai gefe tace “ta k’oshi” Cikin turo baki Sakina tace “haba Mama ki ce mana, kin ganki kuwa yadda kika koma? Gashi duk kin yi wata zuru zuru kamar…” Dukan da Maman ta kawo mata tayi saurin kaucewa, duk kuwa sai suka hau murmushi…. Da naci da komai hakanan sai da Sakina ta d’urawa Mama abincin nan, ta kuwa ci sosai, dan sai da su Madu suka sa baki tukun Sakina ta hak’ura. Sai wajen 11 na safe su Sakina suka fara shirin tafiya don suke suyi wanka suyi girki, ita da Ummu. Baban su Sakina ne yazo d’aukar su! Ya d’auka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96