Chapter 75
Chapter 75
Sakina wadda itama ya lura bata da sukuni ga Ashraff a gefenta wanda yake ji kamar yaje ya rufe da duka, sai wani shishshige mata yake yi. Su y’an matan wajen a tunanin su tsabar kyau da had’uwar sa ne yasa yake shan k’amshi yak’i shiga mutane basu san shi kuwa zuciyarshi ce take shirin tarwatsewa ba! Gashi ank’i a tashi daga wajen....... Sai after kamar 2 hours tukunna aka ce Amarya da Ango su yanka cake! Bayan sun yanka Huda na k’ok’arin durk’usawa ta bashi yayi saurin tarota ya karb’a shi ya durk’usa ya bata! Ai kuwa aka hau tafi ana ta videos da pictures. Daga nan masu bada gifts suka bada aka yi addua aka tashi a lokacin already Auwal ya dad’e da komawa cikin mota su kawai yake jira. Suna fitowa kowa ya fara kama gabanshi…. Bai yi tunanin Sakina zata shigo motar ba! Dan haka ya fara k’ok’arin tada motar bayan su Hudan sun shigo Arshaad ne yace “Wait Auwal, bara mu d’an jira Sakina” Yana juyawa yaga sun yi sallama da k’awarta da wanda ya gansu tare sun tafi.. Sai da taga wucewarsu, tukunna ta zo ta shiga a lokacin ita kad’ai ce ma ta rage a harabar wajen. Har suka isa gidan su Mama bai ko kalli inda take ba Motar shiruuu sai hirar su Arshaad da suke yi k’asa k’asa ba wanda yake jin me suke cewa.. Sallama Sakina tayi da Arshaad Hudan kuma ta cewa Auwal sun gode, daga nan Arshaad ya dawo gaba su kuma suka wuce cikin gida....... Dad, Mommy, Gramma, Aslam Arshaad sai Aaima kawai Granpa ya buk’aci gani tunda a ganinshi ya riga ya cire Dad da Abba da su Hudan acikin zuriarshi….. Mammy da Mom kawai suka tarar a parlourn dan Ummi kusan a sume ma aka kawota, shiyasa Granpa ya kira Doc akai d’akin Gramma ma da ita domin bata taimakon gaggawa. Aaima tana shigowa da suka had’a ido da Mammy sai tayi kanta ta gudu ta rungume kawai tasa kuka. A hankali Aslam yaje ya gaida Granpa tukunna ya dawo wajensu ya gaidasu yana mai shafa kan Aaima alamun lallashi, haka itama Mommy bayan ta je ta gaida Granpa d’in ta dawo wajensu…. Gaba d’aya hankalinsu yana ga Aaima, wani abun mamaki kwata kwata basu lura da Mommy ba har sai da muryarta ta yiwa dodon kunnuwansu dirar mikiya! A firgice duk su biyun suka d’ago suna kallon ta! Itanma su d’in take kallo da murmushi akan fuskarta especially ma Mammy wadda bakinta yake rawa ta kasa furta uffan! Mom na shirin yin magana Granpa yayi gyaran murya. Duk nutsuwa suka yi suka maida hankalin su a kanshi bayan sun d’an gyaygyara zama.. Kallonsu yayi d’aya bayan d’aya, kafin yace “Ina Muhammad?” A hankali cikin girmamawa Aslam yace “Yana wajen event d’insu an fara yau” Da mamaki Mom da Mammy suka kalleshi, suna shirin yin magana suka ji Aslam d’in ya sake cewa “Ni da Aaima ma da yanzu zamu wuce to kuma sai kiranka ya riskemu”. “Call him! Kace ya bar duk abunda yake ya zo yanzun nan!” Cewar Granpa. A hankali Aslam yace “Granpa plss..” Cikin d’an fad’a fad’a abunda bai tab’a yi mishi ba yace “Call him now!!” Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Ok, Granpa.” Sannan ya zaro wayar shi ya hau kiran Arshaad… Har ta tsinke ba a d’auka ba, ya sake kira nan ma ba a d’auka ba, zai kira a karo na uku Granpa ya d’aga mishi hannu, yace “Leave him” Daga nan ya fara magana “2 months ago! Adama, Rukayya da Zainab Sun yi wa wannan family d’in babban laifi wanda hakan ya kai ni ga yanke hukunci a garesu mai tsauri! Dalilin tara ku a nan da nayi shine Inaso In jaa muku kunne akan ‘magana ta riga ta wuce!’. Mazajen su Adama da ita Ummi basa kusa dan haka kai Yahaya kai ne zaka sanar da sak’ona garesu! Banaso ko da wasa inji makamanciyar maganar nan ta sake tasowa! Sun yi laifi an hukuntasu magana ta mutu!! Duk kuma wanda ya k’etare umarnina ko a fuska ya nuna musu wani abun yi zai gamu da fushina tabbas. Su Yusuf kar suga wai basa tare da ni, muddin suka yi wani abun da bai kamata ba a matayensu to tabbas zan yanke musu hukunci mai tsanani! Ka gaya musu hakan. Ku kuma” Ya juya kan su Mammy “Wannan hukuncin da na yanke muku kuka yi going through for the past 2 months ba komai bane! Ku k’irga azabar sau ashirin tou tabbas ita zaku fuskanta muddin kuka bari naji wata matsala daga gareku. Sai magana ta biyu! Duk da Muhammad ya b’ata min rai a yanzu, hakan ba zai saka In chanja abunda na shirya ba… A kwanaki yayi laifi wanda ya kai ni ga rage mishi matsayi Auwal ma haka. Tou yanzu Alhamdulillah naga progress da ci gaba a tare da su, dan haka ranar Monday Auwal ba dan halin ubansa ba sai dan kwazon shi zai koma assistant md tunda Aslam ne md yanzu shi kuma Muhammad ya koma matsayinshi, treasurer. In shaa Allah Nan da shekara d’aya za a fidda wanda ya chanchanci a malllakawa MT gaba d’aya na uk da na Abuja da na nan Kano, a tsakanin su uku. Yahaya In Zainab ta warke ka mik’a ta gidan Mijinta inda ya k’aura ya koma, amman yanzu ka fara kai Adama tukunna ta samu ta huta, Mammy kema ki wuce d’akinki. Allah ya bamu alheri.” Yana gama fad’in haka ya mik’e, ya shige d’akin shi. Shiruu, d’akin ya d’auka. Da kyar Mammmy ta iya mik’ewa dan jikinta ba energy ta isa inda Mommy take tana zuwa kawai ta fad’a jikinta ta fashe da kuka tana cewa “Alhamdulillah!! Na ji dad’in ganinki a haka y’ar uwa ta, Alhamdulillah Alhamdulillah” Mom ita ma rarrafawa tayi inda suke, ba yabo ba fallasa ta d’an rungume Mommy kafin tace “Alhamdulillah, Allah ya k’ara mike lafiya” Ba wadda Dad ya k’urawa ido irin Mammy! A hankali yace musu “ku taso mu tafi” kawai, ya mike. Aaima ce taje ta kansu ta tayasu mik’ewa, dan ko kuzarin kirki babu a jikinsu! Duk sun yi bak’i sun rame sun kod’e sun k’anjame! Banda kuka ba abunda take yi. Aslam tare suka tafi da Mommy kamar yanda suka zo tare. Dad kuwa sai da ya fara kai Mammy gida ita da Aaima tukunna ya wuce da Mom dan kaita sabon gidan da su Abba suka koma. Side d’in Daddy ya shiga tana biye da shi a baya.. A zaune suka samu Daddyn a parlourn k’asa yana shan coffee da suit d’inshi a jikinshi ko takalmi bai cire ba da alama yanzu ma ya dawo daga aiki dan ga suitcase d’inshi a gefe. Sallamar Dad ce ta jawo hankalinshi gare su, mik’ewa yayi yana d’an murmushi da muryarshi dake nuni da a matuk’ar gajiye yake yace “Yaya ina wuni, ai da ka kirani na zo..” Muryarshi ce ta mak’ale sakamokon ganin Mom wadda ta fito yanzu daga bayan Yayan nashi. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya, yana kallanta.. Rabonshi da ita wata d’aya kenan, tun last zuwanshi da yaje tayi ta kuka ya yanke shawarar sai dai ya kira police d’in
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96