Chapter 24
Chapter 24
juya tana kallon Arshaad kafin a hankali tace “Ya Arshaad dan Allah ka b’oye ni dan Allah.” Tayi maganar tana had’e hannuwanta waje d’aya alamun rok’o, tana kuka. Ganin sun kusan isowa ne yasa Arshaad d’in da sauri ya jata yasa a d’akin mai gadi sannan yace mata “ta shige toilet d’inshi(mai gadin) tayi shiru.” Tana rufe k’ofar toilet d’in su kuma su Abba suna shigowa gidan, dai dai Arshaad yana shirin fita shi kuma, suka yi kicib’is!. Kallon kallo aka tsaya yi, kafin Daddy yace “kunga Hudan?” Aslam yana shirin yin magana Arshaad yace “No” da sauri sannan ya d’ora da “Neman ta ake? ina tayi? Mai ya faru?” Aslam kawai Abba ya k’urawa ido..ganin yak’i had’a ido da shi yasa ya cewa Daddy wanda yake shirin yiwa Arshaad bayani “Mu koma kawai, inaga wajen Gwaggo Asabe tayi. Ma duba ta anjima, lets take care of Granpa, na tabbatr biyotan da muka yi yanzu ma case ne.” 100% Daddy ya yarda da hakan dan haka ya cewa Aslam “ya ci gaba da duba musu Hudan za suyi musu bayani anjima, shi kuma Arshaad yaje Gate yayi confirming in bata fita ba daganan ya sa curfew a estate d’in har su samu su gama meeting da Granpa su fito.” Da “to” suka amsa musu daganan su Abba suka wuce. Suna fita shima Arshaad ya fara k’ok’arin fita a gidan “Kace mata zata iya fitowa.” Shine kawai abinda ya iya cewa Aslam ba tare da ya yarda sun had’a ido ba. Har ya juya yaji Aslam d’in ya ruk’o hannunshi… Da sauri ya runtse idanunsa da k’arfi, sai da ya d’an dedeta fushinsa kafin ya juyo yana kallonshi. Aslam tunda yake bai tab’a jin nervousness irin na yau ba, dan haka ya fara kame kame “Um, I’m sooo sorry a b bout” Da sauri Arshaad ya katseshi ta hanyar cewa “It wasn’t your fault, tayi laifi, so ko baka yi abunda kayi ba dole na san wata rana gaskiya zata fito, kuma za ayi punishing nata. Kawai dai i was disappointed in you ne that’s all” Sai da ya d’anyi shiru yaji hucin da yake yi ya d’an ragu tukunna ya ci gaba da magana “Ko sabon mai aiki aka chanja a gidan nan baka nan Aslam kana Uk but sai na kiraka na fad’a maka! Ya kamata ace lissafinka ya baka ‘if Abba yana da y’a and bai san da ita ba, to dole akwai wani abu a k’asa’!. Da kayi finding out about Huda you should have talk to me first mu samu mu fara bincike first! Because that is wat i’ll definitely have done if i were in your shoes. But you just went ahead and ruin everything. Yanzu because of you Mahaifiyata is there a cell da anty Adama su da basu da laifin komai, they just help a friend.” A hankali yace “i tot we were brothers, best friends.” Cikin katseshi Aslam yace “and yes we still are, yana matsowa kusa dashi da rik’eshi”. Murmushi kawai Arshaad yayi ya zare hannunshi sannan ya zagayeshi ya fara k’ok’arin shiga d’akin mai gadi. Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin yace “Ok, I’m sorry” yana mai sake ruk’o hannunshi. Sai da Aslam d’in ya maimaita sannan Arshaad ya juyo ya kalleshi na y’an seconds kafin yace “Apology accepted.” “Thankyou “ shine abinda Aslam d’in yace kafin ya d’aura da “And about what you just saw, i’m..” Cikin katseshi Arshaad yace “Aslam we’re good fa, komai ya wuce, let me check on her, ta shiga toilet d’in mutumin nan barefoot kuma i don’t even know ko yana ciki dan ban ganshi a d’akin ba.” Yana gama fad’in haka ya zare hannunshi sannan yayi cikin d’akin ya isa bak’in k’ofar toilet d’in yana cewa “Hudan open the door, it’s me, su Abba sun tafi.” A hankali take bud’e k’ofar tana d’an lek’owa.. Sai da ta tabbatar da shi d’inne tukunna ta k’arasa bud’ewa. Murmushi ya d’anyi mata.. Gaba d’aya ta had’a gumi tayi zuru zuru! A hankali yace “matsoraciya kawai” A hankali tayi k’asa da kanta sannan ta fito, Allah ya taimaketa ba kowa a toilet d’in kuma mutumin yanada tsafta dan band’akin tass yake gashi tiles ko ina kuma a bushe. Amman dukda haka sai da Arshaad yayi amfani da ruwan butan da ya gani bayan sun fito ya zuba mata akan k’afafunta. Suna fitowa ya cire takalminshi ya bata ta saka sannan yace “ta zo ta rakashi ya saka takalmi.” A hankali ta fara kuka kafin tace masa “Ita wajen Mama zata je” Gaba d’aya sai yaji wani matsanancin tausayinta ya kama shi. Shiruuu, yai yana tunanin ta yadda zai fita da ita bayan shi aka d’orawa alhakin curfew. Dole ya lallab’ata ta d’an hak’ura ko zuwa gobe ne sai su je. Matsowa yayi yana shirin lallashinta wayarshi ta hau k’ara, ganin sunan Sakina ya sanaya shi ce mata su k’arasa ciki akwai maganar da yake ai suyi da ita, dama. Tukunna sai ya kaita gurin Maman. Ba tare da musu ba ta bishi suka yi hanyar shiga parlourn gidan, Aslam har zai bisu dan still ya lura Arshaad d’in is still mad, saboda da suka fito ko inda yake bai yarda ya kalla ba.. Sai kuma kawai ya chanja shawara ya juya kawai, duba da yayi ba shi kad’ai bane kuma ya lura soyayyar Mahaifiya ta rufe mishi ido, if not tayaya zai ce “ita da Mom basu da laifil!” ko kuma may be bai san story d’in gaba d’aya ba, dai. Da wannan tunanin ya fita a gidan bayan ya yanke shawarar sai nan da 4 to 5 days haka zai nemeshi ya sake bashi hak’uri, by then ya san ya sak’k’o..... Suna shiga parlour ya umarceta da “ta zauna akan kujera” Bayan ta zauna shi kuma ya nufi fridge ya d’auko mata ruwa da glass cup a kan dining ya kawo. Dama kuwa tana buk’ata hakan yasa yana zuba mata ta k’arb’a ta hau sha. Sai da ta shanye tass sannan ta ajjiye tana sauk’e ajjiyar zuciya a jejjere. Kallonta yayi da idanuwanshi da har yanzun basu gama dawowa dede ba sannan a hankali yace “In kara?” Girgiza mishi kai tayi tana y’ar mitsitsiyar gyatsa kafin tace “Alhamdulillah” Sai kuma anhankali ta mik’e tace “Bara inje wajen Aaima” Mik’ewa shima yayi yace “bata nan, bata dawo daga school ba tukun! Mammy kuma tana cell! It’s just me.” Ya fad’i hakan yana tsareta da ido. Saurin yin k’asa tayi da kanta, kafin a hankali tace “Kayi hak’uri dan Allah.” Murmushi ya d’an yi yana kallonta kawai ba tare da yace komai ba. A hankali tace “bara in tafi, nayi tunanin Aaima tana nan ma.” Bata jira jin me zai ce ba ta fara k’ok’arin fita tana cewa “ka d’auko takalmin naka muje mu duba Mama da wuri, ko?”. Dede nan wayarshi ta sake ringing, ganin me kiran ne yasa shi kai mata wayar har bakin k’ofa sannan yace “Na so muyi magana but it’s like kamar tsorona ma kikeji! Gashi ungo, Sakina ta gaya miki, bara in d’auko takalmin nawa” Yana gama fad’an haka ya kara mata a kunne bayan ya amsa kiran daga nan yayi hanyar part d’in nashi. Da sallama ta amsa wayar.. Ajiyar zuciya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96