Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 92

Chapter 92

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kanta ta furta cewar bata son y’ata a matsayin suruka To Wallahi ko ta dawo tace tana so, Ina so ka san cewa ‘maganar aure babu ita!!’ Sak’o ne wannan na baka, ka gaya mata ka gayawa Arshaad da wakilin shi! Dan ba zan tab’a yarda in kai Huda gidan da ba’a k’aunarta ba wallahi. Saboda na san zafin k’iyayyar surukai” Ta fad’i haka tana fashewa da wani matsanancin kuka. Da sauri Abba wanda yakejin zuciyarshi tana wani mahaukacin racing yace “Maryam listen to me dan Allah ki bar wannan kukan” Cikin tsananin b’acin rai tace “Abba kuka yanzu na fara! Na san zan yi kuka especially idan Allah ya kaimu gobe aka yi calling off auren y’ata na ganta a cikin tashin hankali dole zan yi kuka.....” Kasa cigaba ta yi da maganar dan haka ta yi jifa da wayar akan gadon ta durk’ushe a k’asa tana kuka. Sakina na shirin yin magana Ummu da Mommy suka shigo. Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e tanaji itama kamar ta fashe da kukan, a hankali ta d’an matso Maman sannan tace “Wannan dalilin fa shiyasa nak’i gaya miki tun farko, kin yi min alk’awarin ba zaki d’aga hankalinki ba yanzu menene haka? Ki kwantar da hankalinki ni na san Mammy bata isa ta hana komai ba! Dad ba zai barta ba.” Cikin katseta Mama tace “Wallahi ko Dad ya barta ko bai barta ba babu maganar aure tsakanin Huda da Arshaad Idan ita ta hak’ura to gobe ni zan hana! Ta yaya kuke tunanin zan bar y’ata ta rayu da surukar da bata sonta? Mommy na san mecece k’iyayyar surukai! Kullum addua ta Allah ya had’a Huda da surukan da zasu k’aunaceta. Taya za ki yi tunanin yanzu zan amince ta auri Arshaad??” Cikin katseta Mommy tace “Kar kiyi haka dan Allah, kawai mu zuba ido amman kar kice zaki shiga tsakanin kaddara! Idan kika yi hakan ai kun zama d’aya ke da Mammy kenan.” Cikin katseta tace “In zuba ido y’ata ta tafi inda ba a k’aunarta kome kike nufi? In zuba ido rayuwar Huda ta lalace kamar yadda tawa ta lalace?” Cikin rashin jin dad’i Mommy tace “Haba Maryam, rayuwarki bata lalace ba, da ni da ke fa kusan mataki d’aya muka taka a rayuwar aure. Tabbas mun jigatu kuma mun sha wahala amman a ko da yaushe idan na kalli Aslam wallahi ji nake gaba d’aya wahalar it’s worth it! Dan Allah yayi mana kyauta. Kuma dama a rayuwa dole akwai jarabta da kuma gwajin imani. Ni dai shawarar da zan Baki itace Dan Allah kar kiyi interfering ki zuba ido ki barwa mazan komai, su sun san me za suyi.” Cikin sharar kwallah Ummu tace “hakane tabbas! Mama dan Allah ki gwada yin hak’urin da kika saba wata rana sai labari.” Da sauri Baaba Talatu wadda bama su san ta biyo su ba ta k’araso tace “Taya zaku ce mata haka? In dai uwar Yaro tace batayi to muma ba zamu kai jikarmu mai tsada inda ba’a k’aunarta ba wallahi! Allah na tuba maza da yawa a gari.. Ga mai sunan kakan ta nan, d’an wajen Jamilu, idan Arshaad d’in zai kawo matsala ana iya d’aura musu aure gobe in sha Allah. Na san ba zai tab’a cewa a’a ba, saboda daman ni na d’an so in fahimci take takenshi tun ba yau ba.” Gyaran murya Shuwa wadda ta shigo yanzu tayi, dan haka duk suka juya suna kallonta. A hankali ta k’araso cikin tafiyar ta wadda ke nuna tsufan da ya rufar mata. Sai da tazo gaban Maryam tukunna ta kama hannuwanta duka biyu ta fara magana “Dan Allah dan annabi kar ki yi komai kar ki yi kuka kar ki d’agawa y’ar ki hankali. Ki bar komai a hannun Ubangiji, tun kafin ki haifi Huda already an riga an gama rubuta k’addararta da komai nata. Kar ki yi interfering wai dan kina tunanin zaki iya kub’utar da ita! ki zuba ido ki yi mata addua komai zai tafi bisa yanda Ubangiji ya riga ya tsara. Bamu isa mu saka ko mu hana komai ba. Kin ji y’ar albarka?” Ta k’arashe maganar tana mai sa hannu ta share mata hawayenta duka biyu. Kuka Mama ta sake fashewa da shi ta fad’a jikin Shuwa suka rungume juna. Ita kanta Shuwan k’arfin hali ne kawai da dauriya suka hanata kukan Ta rasa gane wachche iriyar k’addara ce A rayuwar Maryam da Huda, Astaghfirullah..... Shigowar ta tare da matan da suka ruk’o ta ne ya sanya d’akin yin shiru. Har yanzu fuskarta a rufe take amman kana gani ka san kuka take yi. Sakina na ganinta taji kuka na shirin kufce mata dan haka da sauri ta fita a d’akin. Suna zaunar da ita a bakin gado Mama ma ta saki Shuwa ta fice. Shuwan ce tayi k’arfin halin cewa “Mommy da Ummu da kuma mata biyun da suka shigo da ita “Su je akwai motoci a fara kwasar kayan Amarya ana kaiwa gidanta, dan ba zata yarda da ajjiye wannan dukiyar a gidanta ba, tunda kowa ya gani kawai su kai mata abunta gidanta.” Murmushi Mommy tayi kafin tace “Ni kam gida zan wuce.. Ina a matsayin uwar Ango ina ni ina ziryar gidansu Ai nayi jere sai kuma in ta haihu nan da wata tara in sha Allah ni da in koma.” Da sauri cikin raha ragowar matan suka ce “In shaa Allah” Ba a wani dad’e ba suka fito dukkansu a tare Mommy ta d’anso ta sake ganin Mama amman kuma kawai sai ta rabu da ita, a cewarta ‘in ta d’an sauk’o zuwa anjima zata kira ta a waya’….. A tare suka fito da Ummu, su suka fara yin gaba da akwatuna ita kuma ta shiga mota ta nufi MT estate dan already drivern ya zo tun d’azu. NASARAWA g r a. Daddy da Dad na zaune sai zazzagawa Abba fad’a suke yi akan ‘ya mayar da Ummi tun kafin zance ya isa kunnen Granpa’ shi kuma ya tubure ya k’i!. Suna a haka wayar Mama ta shigo… Tsaf! Duk sun ji abubuwan da ta fad’a, dan wayar a high volume take kuma suna kurkusa da juna. Yana gama wayar Dad yace “Abba ka mayar da Ummi yanzunnan in dai na isa da kai.” Haka shima Daddy same thing ya fad’a mishi. Ba yadda ya iya haka ya maida ita yana ji kamar yayi ta kurma uban ihu!. Daganan Dad ya mik’e! Kamar Daddy ya san meye a ranshi yayi saurin mik’ewa shima ya tsaya a gabanshi sannan yace “Dan Allah kar ka yi haka. Ka tsaya zan yiwa Adama magana, na san kafin zuwa gobe in sha Allah zata nutsu.” Cikin fad’a fad’a Dad yace “Ba zata nutsu ba! Sam ba zata nutsu ba. Da ace zata nutsu da tun tuni ta nutsu, ku bar ni kawai!!” Ya fad’i haka yana k’ok’arin zagaye Daddy ya wuce. Da sauri Daddy ya kuma tareshi sannan yace “Ya abunda muka gama gyarawa yanzu! Da girman ka kake k’ok’arin aikatawa?” Cikin tsananin b’acin rai Dad yace “This is a different case..” Cikin katseshi Daddy yace “Ba wani different case anan duk abu d’aya ne! Idan kayi mata haka ma ai ka ji haushi kenan, wato ta ci riba ma

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});