Chapter 91
Chapter 91
masu goge gogen gidan! Tace musu “su tafi part d’insu In akwai wani abun zata neme su!” Har ta shiga ta d’auko abunda zata d’auka ta fito hankalin Jalila yana kan kallo. A dai dai stairs na bakwai ta tsaya ta zuba abunda zata zuba tayi sama abunta da cup d’in cikin sand’a. Kamar minti biyu ta dawo bayan ta ajjiye abun hannunta a d’an gefe kad’an a nan saman ta tsaya a saman bata sauk’o ba kafin ta d’an fara sauk’owa sai kuma ta tsaya tana lek’en parlourn k’asan kafin tace “Jalila ga Ummanki tayi miki message, ungo wayarki, tunda na hau nake ta jin k’arar wayar shine na duba d’akin naga misscalls da messages Za ki zo ki karb’a? Ko kuma ma kawai bara in karanto miki kina daga zaune dan na san mik’ewa yanzu aiki ce a gareki saboda yanayin da kike ciki.” Ba tare da b’ata lokaci ba Mom ta fara karantowa “Aslm Jalila ya gidan, yau banjki....” A zabure Jalila ta mik’e tayi hanyar stairs tana masifa “Adama bana son rashin mutunci! Yanzu ke inda ace uwarki ce tayi miki message zaki yarda a karanto miki….?” A fusace take maganar tana tahowa da d’an cikinta wanda ya d’an fara tasowa! K’arfen stairs d’in ta kama cikin sassarfa ta fara taka stairs d’in har da d’an gudunta, tana zuwa kan na bakwai kuwa ta zulme santsi ya d’ebeta a take ta hantsila ta gangara ta koma k’asa ta fad’a ruf da ciki a kan cikinta! Wata azababbiyar k’ara ta saki daga nan ta saki jiki bata sake motsi ba!. Da sauri Mom wadda daman da tsummanta har biyu ta ajjiye a gefe farkon stairs d’in dan haka ta d’an juya ta d’auka ta sauk’o, dai dai wajen na bakwai d’in ta saka wet one d’in da ta jik’a a ruwan omo ta goge wajen tass kafin ta saka dry one d’in ta goge wajen sosai shima. Dai dai nan Auwal da Aaima waenda k’arar Jalilan ya janyowa hankali suka taho a tare… Da sauri Mom ta d’ago ta kalleshi a rikice kafin tace “Yauwa Auwal zo ka duba inaga jiri ne ya kwasheta kaga ta fad’i kamar ma ta suma bara in d’ebo ruwa.” Ta fad’i hakan tana mai sake duk’unk’une tsummokaran a hannunta Yayinda su kuma gaba d’aya hankalinsu ke a kan Jalila… Idan idanuwansu ba gizo suke musu ba kamar jini ne yake fitowa ta k’asan ta! Shiyasa ma kwata kwata basu lura da Mom d’in ba suka fara sauk’owa har suna y’ar rige rige, ita kuma ta wuce wuff!! Tayi kitchen tana mai cewa “bara in kawo ruwan” Hankalin Aaima ba k’aramin tashi yayi ba ganin kamar ma ta mutu ne! Ga kuma jinin da taga yanata kara b’ulb’ulowa, shi kanshi Auwal duk da cewa babban burinshi a halin yanzu yayi getting rid of Jalilan ne amman sai da ya firgita ba kad’an ba. Suna a haka Mom ta fito, ruwan da ta zo da shi a jug gaba d’aya sai da ta juye mata shi amman ko gezau Jalilan bata yi ba! Ganin haka yasa Auwal yin sama da gudu ya je ya d’auko makullin motarshi ya dawo ya zo ya kinkimeta yayi waje su Mom suna binshi a baya…. Yana gama sakata a bayan mota motocin su Dad na shigowa ganinshi a d’an firgice yasa suka tsaidashi suka hau tambayarshi.. Da kyar ya iya ce musu Jalila ce ta fad’o a bene ta suma ya shige ya tada motar ya fice a 70 ya bar su Mom suna sake yi musu bayani “Allah ya sauwwak’e” suka ce. Shi kam Dad bai ma san wacece suke magana akai ba daga haka suka nufi side d’in Abba dan Dad yad’an yiwa Daddy bayani a mota So ya kamata su sameshi ya maida Ummi first kafin granpa ya tsine mishi, sannan kuma ayi maganar ta yanda za a b’ullo wa haukar Mammy dan sun yi alk’awarin in dai sune mazan mt masu fad’a aji to tabbas gobe sai an d’aura aure bi izinillahi! Babu fashi….. GANDUN ALBASA “Ku bata iska mana ya duk kuka lullub’eta haka ne??!!” Cewar Baaba Talatu wadda take k’arasowa wajen da kyar. Da sauri duk aka fara matsawa gefe. Hansai da Anty Zainab da wasu mata Baaba Talatu ta umarta da su d’auketa a kaita parlourn da ga nan ta cewa Maryam “ta kirawo Likitan da take zuwa tana dubasu.” Hakan kuwa aka yi Nan tace mata “gata nan zuwa tana ma kusa dama, su bata nan da minti goma.” Ko da Likitan ta zo da kyar ta samu Umma ta farfad’o amman ta bada shawarar a kaita emergency a take dan jininta ba k’aramin hawa yayi ba! A motar Abba k’arami wanda suka iso yanzun nan shi da iyalinshi da Mahaifiyarsa da Baban sa aka kaita asibitin. Duk da halin da take ciki da suka had’u da Ya Jamilu a waje bakin motar sai da ta tambayeshi “ina Baba?” “Yana nan” kawai ya iya ce mata daga nan ta shige ita da Anty Zainab wadda ta zauna a gaba suka wuce asibitin. Da kyar Mama ta iya tsayawa aka gama kallon lefen da ita daga nan ta wuce ta shige tayi sama… Tun a corridor d’in d’akin Shuwa ta saki kukan da take ta k’ok’arin dannewa. Da sauri ta tura k’ofar ta shige tana wani matsanancin kuka a tunaninta ba kowa amman tana shiga suka yi ido biyu da Sakina. K’ok’ari take yi ta danne kukan ta wayance amman ta kasa dan haka kawai sai ta durk’usa ta sake sakin shi a wajen da dukkan k’arfinta tanayi kamar ranta zai fita......... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 54 Da sauri Sakina ta k’arasa wajenta ta hau tambayarta “mai ya faru?” Bata iya bata amsa ba, sai da ta d’an dedeta kanta da kyar tukunna ta d’ago jajayen idanunta tana kallon Sakina tace “Kina da number Abba? Baban Huda.” A hankali Sakina ta hau girgiza mata kai..kamar wadda ta tuna wani abun kuma sai ta mik’e ta isa gado inda ta ajjiye purse d’inta, tana cewa “Amman ga wayar Hudan, bara in kira miki shi ta nan” Da sauri Mama ta mik’e ta isa inda take dai dai Sakina ta fara dialing number Abban, Mama ta sa hannu ta karb’a wayar ta kara a kunnenta. Sai da kiran ya kusan tsinkewa tukunna ya d’auka! A hankali taji yace “Princess, how was your day?” Sai da Mama ta lumshe idanunta na sakanni wasu zafafan hawaye suna zubo mata tukunna tace “Horrible, Abba! Her day was horrible!”. Da sauri ya gyara zamanshi kafin yace “Maryam” Cikin son sake tabbatarwa. Cikin kuka tace “Lalata mini rayuwa da farin cikin da kayi bai isheka ba sai da ka had’a da Huda ko? A haka sai faman ik’irari da pretending d’in kana k’aunarta kake yi!.. Abba in dai har kana son ta mai yasa ka jefa ta a irin wannan relationship d’in??? Da ka san mahaukaciyar matar yayanka ba zata so auren Arshaad da Hudan ba mai yasa tun farko kuka had’a? Saboda ku maidamu abun kwatance ko me?? An tara mutane k’iiri k’iri Ango yak’i zuwa! A Ina aka tab’a yin haka? To bara kaji in gaya maka Tunda har Mahaifiyar Arshaad da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96