Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 32

Chapter 32

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Aslam d’in abun a jiye mishi ne, saboda gaba d’aya rayuwarshi ya yita ne cikin fargaba, k’unci da damuwa. Yanzu haka ko Abokanai baya iya tarawa shi kad’ai d’insa yake komai sai dai a d’an dinga zumunci sama sama, Abokin shi na k’ut da k’ut guda d’aya tak a duniya wato Arshaad, da Arshaad ne kawai za kiji suna waya suna d’an raha amma ko mu y’an gida wani lokacin idan ka kirashi sai yak’i d’auka. Tsoronma shiga mutane yake yi balle yayi huld’a dasu.. Naji su Abba suna cewa ‘Kana ganinshi in dai ka fahimci yanayin shi tou tashi d’aya zaka fahimci he’s depressed! Kuma hakan ba a so a mutum especially mai k’arancin shekaru kamar nashi, zai hanashi yin farin ciki a rayuwa ne kwata kwata, har abada!.” Ahankali tace “To amman ya za ayi? Magani in dai sunanshi magani tou ba kalar wanda ba ayi ba amman har yanzu shiru............” Ta k’arshe maganar tana share d’an hawayen daya biyo idanunta a karo na ba adadi. Hudan, itama hawayenta ta goge, a ranta tace “Allah sarki bawan Allah, ashe shiyasa kullum yake cikin fushi, da har nake jin haushinshi.. In shaa Allah daga yau na daina jin haushinshi, Allah ya bawa Mahaifiyarta lafiya.” Maganar Gwaggo Asabe ce ta katseta jin tana cewa “Kema dan Allah idan kin yi sallah ki dinga sakamu a addua Allah ya kawo k’arshen wannan abu.” A hankali Hudan ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “In shaa Allah” Sai kuma ta gyara zamanta ta ci gaba “Amman Gwaggo a duk cikin bayaninki banji inda aka yi mata Sauk’ar Alqur’ani ba!” Cikin katseta Gwaggo Asabe tace “anyi sauk’a Huda, Granpa da Dad da kansu suka je suka raba kud’i lokacin da suka dawo farko farko a islamiyoyi da tsangayar almajurai aka yi ta sauk’a!.” Murmushi Hudan tayi sannan tace “Gwaggo Asabe, idan zan bada shawara a d’auka inaga daa mu da kanmu ya kamata muyi mata sauk’ar bayan an raba a islamiyoyin, kuma in na fahimceki kamar sau d’aya aka tab’a yin sauk’ar ko?” Bata jira jin mai Gwaggo Asaben zata ce ba ta ci gaba “Ni a lokutan baya, idan bamu da lafiya ko wani alamari mara dad’i ya afku Tou bayan Mama ta bamu magani sai ta kammala mana sauk’a, ko lokacin da nake k’arama akwai Yayanmu da yake shaye shaye sai da Mama tayi mishi sauk’ar AlQur’ani sau bakwai!! Ta fara tayi sau hud’u ya warke ya daina amman dake tayi niyyar bakwai d’in zata yi sai da ta k’arasa. Da kuma muka yi wayo haka zata rarraba mana muna tayata da ni dasu Ya Jalila koda izu d’ai d’ai ne mu kan taimaka. Ko yanzu haka In wani abun ya faru rabawa muke yi ni da ita da Sakina wani lokacin da Sumayya, bama wata d’aya muke k’arasawa, in kuma mun kwallafa to a sati muke idawa. Balle nan gidan munada d’an yawa.. Yanzu for example ace mutum shidda kowa ya d’auki izu goma, duk bayan sallar Farilla kayi izu d’aya a kwana biyu fa za mu dinga kammalawa, In kuma izu biyu za ana yi a cikin kwana 1 mun kammala, inda hali kowa in ya kammala sai yayi mata addua dafatan waraka bayan an tofa aruwa a bata tana sha, Daganan ayita yi, kuma akai akai. In Allah ya yarda sai kiga an dace. Dan dai gaskiya kamar yadda kika fad’a abun sam kamar bana asibiti bane ba! Koda ace ma na asibitin ne Sauk’ar Alqur’ani fa shine k’arshen waraka Especially idan mune muka yi da kanmu, saboda waennan na islamiyya ba mu da tabbas, yanzu duniya ta chanja ba lalle In sun karb’i kud’in suna sakawa anayi ba…..” Maganarta ce ta katse jin mutum a tsaye a bayanta ya dafa kanta, tana juyowa sukai ido hud’u da Dad da Abba a bayanshi suna murmushi, waenda shigowarsu kenan suna d’an tatauna wata magani suka ji bayanin Hudan. Dad ne yace “y’ar albarka, naji dad’in wannan shawarar taki sosai. Kuma daga yanzu in shaa Allah zata fara aiki. Kafin masu kwashe kaya su gama na san mun kammala in shaa Allah, na yau.” Yana gama fad’in haka ya d’au waya ya kira Arshaad da Aslam yace “su sameshi.” Sai da ya gama wayar, Hudan ta d’an zame daga kan kujera inda take ta shiga gaida Abba. Shima Dad d’in ta sake gaidashi. Cikin kulawa suka amsa mata sannan suka cigaba ta tattaunawarsu da alamun magana mai muhummanci suke yi. Hudan sai d’ar d’ar takeyi a tunaninta kar Abba yai mata fad’an abunda tayi mishi jiya, shima ya lura da yanayin ta shiyasama ya fasa zuwa inda take, amman da yayi niyyar jin yadda ta kwana da kuma jin ko akwai abunda takeso dan harga Allah shikam yana so ya zama tare da y’arsa ya jaa ta a jiki ko sa samu su saba da juna sosai. Arshaad ne ya fara shigowa… Tsayawa Hudan tayi tana kallonshi dan ta manta rabon da ta ganshi da k’ananan kaya, yafi ta’ammali da shaddodi da yadi, sab’anin yau da yake sanye da wata shirt army green dark an rubuta ‘KING’ a jikin gaban rigar da zanen crown d’in king d’in ata k’asa. Rigar irin mai d’an kama jiki ce, hakan ya taimaka wajen fito da ainahin surar jikinshi dan kana iya hango packs d’inshi na sama sama ta cikin rigar da yadda dantsen hannunshi yake a mummurd’e! Wandon nashi shima ba jeans bane yana yin rigar ne black in colour bai kamashi ba kwata kwata ta sama amman roba ne, kasancewar ya d’an matse daga guiwar wandon zuwa k’asa yasa ya zama kamar pencil trouser ta k’asan… Kayan yayi matuk’ar fito da asalin surarshi ta giant! Ga wani fitinannen k’amshi mai tsayawa a rai da yake zubawa dan tunda ya shigo parlourn ya karad’e da k’amshin shi, tun bai iso inda suke ba…. Hudan bata gama k’are mishi kallo ba suka had’a ido da shi, gira d’aya ya d’aga mata yana d’an murmushin gefen baki, da sauri ta sunkuyar da kanta k’asa kunya duk ta lullub’eta ganin ya kamata tana kallonshi . Ganin yadda tayi ne ya sanyashi sakin wani lallausan murmushi, kafin ya k’arasa inda su Dad suke ya shiga gaidasu cikin girmamawa. Ya so ya k’arasa wajen Hudan dan shima ba k’aramin kyau tayi mishi cikin rigar abaya blueblack mai stones, d’aurin da ta yiwa kanta da d’ankwalin abayan ya yi matuk’ar burgeshi! Amman sai Dad ya tsareshi ta hanyar fara yi mishi bayani abunda za suyi ba tare da b’ata lokaci ba, 100%ya amince da kuma jinjina ga wanda ya kawo shawarar dan abunda ya kamata ayi kenan, cikin jin dad’i Dad yace “ai Hudan ce” da d’an murmushi ya juyo yana kallonta, yanzun ma sauri tayi tai k’asa da kanta, don still satar kallonshi take yi, harga Allah Ya Arshaad yayi kyau yau sosai…… Tana wannan tunanin hancinta ya fara jiyo mata wani k’amshi na daban, wanda a take ya cika mata hanci, kuma ta fahimci wanene Kasancewar a kan kujerar dake gaban side d’inshi take ne yasanya ta fara jin k’amshin kafin kowa, bata san daliliba ba kuma tasan mai ya faru ba, amman ko lokacin idan anyi laifi a islamiyyarsu za a dakesu tabbas zuciyarta bata yin kalar

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});