Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 78

Chapter 78

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

har sai da ya farkar da Sakina da Khadijah amarya y’ar Anty Zainab da suke d’aki d’aya da ita daga bacci. Ganin yanda duk ta rud’e ne yasa Sakina ta shiga tambayarta…. Karb’ar wayar Sakina tayi itama ta shiga kiran sunan shi tana “Are you there? Are u okay??” Amman tsit kake ji ko tari babu. Rikicewa suka yi… Da kyar idea ta fad’owa Sakina hakan yasa da sauri ta d’auki wayarta ta danna kiran Aaima! Sai da kiran ya kusan tsinkewa tukunna aka d’auka, cikin gigita Sakina tace Aaima ina wuni, sorry na tashe ki, Ya Arshaad ne bashi da lafiya, dan Allah ko zaki gayawa Dad in yana gida a duba shi ko kuma ki tura wani wanda yake kusa….” Shiruuu, Sakina taji anyi! Hakan yasa ta sake cewa “Aaima” Ajiyar zuciya taji Aaiman ta sauk’e sannan ta fara magana “Ki turo Hudan mana ta zo ta duba shi! Daga nan ma sai su yi sorting out decision d’in da ya kamata su yanke.. Besides a nan ba wanda zai kulashi saboda rashin lafiyarshi ba zamu iya yi mishi maganinta ba. Spoiler alert!! Bara kiji abunda na san ya jawo mishi ciwon...... Mammy ta dawo d’azu at last ita da su Mom! And tace masa ‘ya hak’ura da auren Huda ko kuma ta tsine mishi!’ Wannan shine abunda ya janyo mishi rashin lafiya na riga da na sani.” Tana gama fad’in haka ta ajjiye wayar. K’amewa Sakina tayi ta kasa cire wayar daga kunnenta! Sai da Hudan ta tab’ota tace “Ya ake ciki Sakina?” Tukunna tayi firgigit ta dawo daga tunanin tashin hankalin data fad’a na y’an sakanni.... ….Dama da ita bata tab’a fadawa kowa ba ne amma haka kurum idan ta tuna Mammy bata san dalili ba sai taji gabanta yana ta fad’uwa! Dan bata san ya tsakaninta da Huda zai kasanceba. Kuma ta lura kamar Arshaad d’in yana ta saurin ayi ayi ai auren su samu su bar k’asar! Tabbas sai yanzu ta fahimci dalilinshi.. To amma mai yasa Ya Arshaad zai so ya had’a ta da surukar da ba zata amsheta ba? Duk kuwa da tsananin k’aunar da suke yiwa juna ai da sun hak’ura!…… “Sakina, akwai matsala ne?” Muryar Hudan cikin rauni, ta katse mata tunaninta…. Juyawa tayi suka had’a ido! A take wani tsananin tausayinta ya rufeta dan bata jin a cikin shekaru ukun nan akwai lokacin da take hango tsantsar k’aunar Arshaad a idanun Hudan kamar wannan lokacin. Da kyar ta iya ce mata “Aaiman bata gida, bara in kira Auwal kawai.” Ta fad’i haka tana me mik’ewa ta fice daga d’akin gaba d’aya. Hudan kwata kwata bata gamsu da maganar tata ba dan haka ta mik’e ta bi bayanta. Suka bar Khadija wadda itama bata wani yarda da maganar Sakinar ba dan ta lura da yanayin da ta shiga tun fara wayarta da wadda suka kira da ‘Aaima’. Tana fita ta samu damar zubar da kwallar da take ta k’ok’arin rik’ewa! Yanzu Ina mafita? Meye abunyi ? Sune tambayoyin da suka toshe mata kwanya sannan ta kasa samun mai bata amsar su. Daman y’an layi har sun fara k’ananan maganganu suna cewa ....Allah dai yasa tarihi kar ya maimaita kanshi Ita maryam bata daddara da family d’in Abba da abunda shi kanshi Abban yayi mata ba shine zata aurawa Huda nephew d’inshi dan kawai taga yana da masifar kud’i! Ga dai Ummu ita da ta auri saffa saffa hankalinta a kwance rayuwarta gwanin ban shaawa amman ita har yau bata samu kwanciyar hankali ba a ta dalilin So da Buri! Ta mannewa mutumin da yafi k’arfin ta nesa ba kusa ba.... Jin k’arar bud’e k’ofar d’akin nasu ne ya sanya Sakina goge hawayenta da sauri, sannan ta lalubo number Auwal ba dan ranta yana so ba ta fara kiranshi…. Bacci bai dad’e da d’aukarsa ba dan bai dad’e da kwanciya ba amman yana fara baccin ya hau mafarkinta............. Yana cikin mafarkin nata k’arar wayarshi ta katse mishi mafarkin…. Kamar ba zai juya ba bayan ya farkan sai kuma yayi tunanin ko Granpa ne dan haka yayi tsaki ya lalubo wayar akan bedside ya amsa ya kara a kunnnen shi ba tare daya duba mai kiran nasa ba. Jin shiru yasa tace “Ya Auwal” A hankali. Bude idanuwansa yayi da kyau kafin ya zaro wayar daga kunnenshi ya kalla sosai ya tabbatar itan ce tukunna ya mayar da wayar kan kunnensa ya mik’e zaune yana adduar ‘Allah yasa lafiya’ dan ya san ba k’aramin abu bane zai sanya Sakina ta kirashi kuma cikin daren nan ba. Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “How far” Dan lokaci d’aya ranshi ya b’aci bayan ya tuno ta Ita da Ashraff d’azu. Ba tare da b’ata lokaciba tace mishi “Ya Arshaad ne suke tunanin bashi da lafiya dan yanzu ma kamar suma yayi suna cikin waya da Hudan.” Ta san maybe Hudan ce ta fito d’azun kuma maybe tana tsaye a bayantata dan haka sai ta tak’aita maganar tata sannan tace “Dan Allah yaje ya dubo shi” “Okay” Kawai yace daga nan ya kashe wayar ya mik’e ya fad’a toilet yad’an d’auraye fuskarshi ya chanja zuwa jallabiya tukunna ya fita.......... Sai da ya daddannawa gate man d’in zagi, tukunna ya barshi ya fita A cewar shi (gateman d’in) Daddy ya hana a na barinshi yana fita cikin dare. Sai mita yake yi shi kad’ai a mota haka ya isa gate na estate d’in MT ..a ranshi yana aiyyanawa ‘Da mutane sun san halin da yake ciki to da ko kallonshi ba zasu dinga yi ba! Komai b’ata mishi rai yake yi tun d’azu...’ Allah ya so shi bai samu matsala da mai gadin main estate d’in ba, sai dai ya rok’esa akan ‘ya bi a hankali kar ya bari Granpa ya ganshi dan zai iya cewa a bakin aikin shi’ Jinjina kai kawai yayi ya wuce ciki. Ya dad’e yana knocking jin shiru yasa ya yanke shawarar kiran Aaima yace mata ‘ta kira layin wata a cikin masu aikin gidan tazo ta bud’e mishi k’ofa.......’ Tunda Sakina ta kira ta bacci ya k’aura daga idanunta, tana cikin chatting kiranshi ya shigo wayar tata. Ta dad’e tana kallon number, kasancewar ta dad’e da goge numbershi amman ta na nan a kwakwalwarta bata gogu ba! A take jikinta ya mutu.. Sai da wayar ta kusan tsinkewa tukun ta samu damar amsawa, cikin sanyin jiki ta kara a kunnenta tace “Hello” Ba tare da ya amsa ba yace “Aaima Arshaad is sick, na zo duba halin da yake ciki kuma k’ofan ank’i bud’ewa.. Can you do me a favor ki kira wani wanda kika sani a cikin gidan yazo ya bud’e min? It’s an emergency” Tunda ya fara magana ta lumshe idonta har ya kai aya a hankali tace “to” kawai, ta tsinke kiran. Kamar 5 minutes yaji ana k’ok’arin bud’e k’ofar, ana bud’ewa ya kutsa kai ciki ba tare da ya kalli bayan k’ofar ba inda take, yayi hanyar side d’in Arshaad direct kawai. “Ina wuni” Yaji muryar ta. D’an juyowa yayi ya kalleta a ranshi yace “Ashe ta dawo.” Ba yabo ba fallasa yace “Lafiya” Kawai ya juya ya nufi hanyar part d’in Arshaad. “Ya k’ara haske, sai dai yad’an rame kad’an! Ya k’ara kyau.”

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});