Chapter 31
Chapter 31
farko yana shigowa zata fara kuka!! Sai kuma ta dawo ihu!!! Daga k’arshe dai ko asibitin in Aslam ya shigo tun kafin ya k’araso inda take zata hau kururuwa tana kuka kowa ta nan ne yake gane Aslam ya iso! Wani abun mamaki shine ta warke garau ta fara magana ta gane kowa amman fa ko a labari idan aka sako Aslam tou yanzu hankalin kowa zai tashi!! Ba k’aramin kid’ima Likitocin suka yi ba dan su kansu sun zama confuse..A iyaka sanin su masu irin wannan matsalar basa haka amman duba da suka yi da shi ta fara ganewa a lokacin data farfad’o ya sanya suka yi y’an bincikensu, iya abunda tunanin su ya basu ne ya sanya su dangantata da psychiatric. Allah sarki Aslam, a lokacin sai da ta kai ga shima aka bashi gado a asibitin tsabar tashin hankalin daya shiga. Yaro ne shi a lokacin amman kasancewarshi mai kaifin basira yasa ya fahimci komai. Dan zan iya ce miki har yau ban tab’a ganin Yaro mai wayo tarin ilimi da kaifin basira irin Aslam ba, har gobe in da wani d’an ajinsu da suka yi makaranta zai zo gidannan to ba zaki tab’a ji ya kirashi da aslam ba , sai dai suce mishi ‘gifted’ Dan wani abun time d’in a makaranta ba sai an koya mishi bama yake iyawa, in kuma ya iya to ya zauna kenan! Ga wayo kamar wani d’an shekaru dayawa.” Ajiyar zuciya Gwaggo Asabe ta sauk’e sannan ta ci gaba “A lokacin hankalin kowa a tashe yake, ni kaina da nake nan da ban ganta ido da ido tana haukan ba sai da naji a jikina, abu yak’i ci yak’i cinyewa har aka shafe wata biyu a haka, ga Aslam a kwance… Tausayin shi da ya lullub’e Granpa gashi yana ganin yana neman mutuwa ne yasashi fara nemawa Aisha magani gadan gadan ba kama hannun Yaro, duk inda yaji labarin Likitan kwakwalwa nan zai tarkata su su nufi k’asar! Cikin shekara biyu zan iya ce miki sun kusa zagaye duniya dan ba k’asar da ba a je ba, in dai kinajin ta kuma sananniyace. Amman dukda haka Allah bai kawo sauk’in ba, saboda lokacin samun sauk’in bai yi ba. Daga karshe dai hak’ura suka yi suka dawo gida Nigeria. Ai ana dawowa abun yafi na daa, ba k’aramin tsorata muka yi ba dan nima nazo a lokacin…Idan Aslam baya gidan nan to k’alau amman ko bakin MT yazo yanzu zata birkice, abun tausayi In kana nan dole kayi kuka, don Aisha mahaukaciya tuburan ta koma. Shawara d’aya Granpa ya yanke shine na ‘kai Aslam boarding school’ don samun sauk’in kowa and ya kamata yaci gaba da karatu kuma ya maida hankali saboda an barshi a baya sosai… A lokacin shekarunshi sun haura 14. Da kyar Aslam d’in ya yarda, ya tafi bayan Granpa yayi mishi alkawarin ‘duk inda magani yake a duniyar nan in dai akwaishi to zai nemawa Mommy d’insa, ko nawa ne kud’in ba zai gaji da biya ba, koda kuwa zai k’arar da duk abunda ya tara ne!!!’. Haka nan aka tarkata Aslam aka kaishi boarding cikin tsananin k’unci, yana kuka muna kuka ba dan munso ba. Wani abun takaicin ko hutu Aslam bai isa ya zo ba, sai dai In kana buk’atar ganinshi kai kaje ka ganshi a inda yake, k’iri k’iri zaman estate d’innan ya gagareshi… Ganin abun na Aisha bana k’are bane yasa suka kira wani babban Likita daga k’asar waje har gida Nigeria ya dinga kula da ita, shi ne ya bada shawarar a kulle su ita da Aslam a d’aki d’aya su kad’ai, for 24 hours, to kuma abun bai yi dad’iba don shi yayi sanadiyyar da Aslam ya bar k’asar nan wanda sai yanzu ne Allah ya dawo mana da shi! Da farko an tsara akan zai d’an dinga lek’owa Hutu sai yake sauk’a gidan Abba, yadda ba zasu had’u da ita ba, har zuwa lokacin da Allah zai kawo sauk’i Amman abunda ya faru a wannan rana ya sanya Aslam yin yaji mai mugun tsayi ya tarkata komai nashi ya tafi sai dai waya, shima wani lokacin sai yake gudun d’auka!. Arshaad da su Abba suna yawan zuwa duboshi, Auwal ne ma yaje sau d’aya, amman Arshaad a shekara ma yakan je sau biyu shi da Abba..saboda shi Aslam ko hutu idan anyi na makaranta baya iya dawowa sai dai yayi achan Oxford Uni inda yayi karatunshi. Aslam a Oxford yayi karatu, Arshaad kuma Dubai aka kaishi Auwal kuma Cairo. Da yake Granpa ne duk ya kaisu..duk da halin da Aslam yake ciki sai da aka fara k’ananan maganganu, Adama da Ummi, wai ‘har yanzu Granpa bai daina nuna bambanci ba’ Sosai Granpa da maganar ta koma mishi yayi musu tataas!!!Kuma ya taso da maganar mallakawa Aslam MT gaba d’aya inyaso sai yaga me za suyi!. Da kyar da sid’in goshi Gramma ta tausheshi, sannan ta lallabashi, sannan tai k’ok’arin fahimtar dashi abubuwan da hakan ka iya janyowa…. Awannan lokacin kuwa anci sa’a ya fahimceta sosai, don da kanshi kuma ya dawo yace ‘a tsakanin Auwal Arshaad da Aslam, duk wanda yaga he’s capable to shi zai mallakawa MT’. Dad yayi mugun mugun yin farin ciki daga jin wannan decision na Granpa, bawai yana zargin wani ba, kawai dai yaji releaf, kuma shima baya son bambancin da Granpa d’in ya dad’e yana nunawa especially tsakanin Arshaad da Aslam, don duk abun nan da ake yi ko sau d’aya Arshaad bai tab’a nuna b’acin ranshi ba, dukda kuwa uba d’aya ne ya haifesu shi da Aslam d’in, Idan akwai fitinanne tou Auwal ne! Amman Arshaad shi ba ruwanshi yana da kauda kai kunyarshi ce ma ta sanya Dad yake yiwa Mahaifiyarshi wani abun dan kar yaga ga kamar bai damu da ita sosai ba. Kowa idan zaki tambaya a estate d’innan ya baki sheda akan Arshaad to zai ce miki ‘yanada hak’uri da kauda kai da kuma saurin yafiya’. Aslam yana kammala degree na farko aka d’aura shi a matsayin MD na MT branch d’in dake achan k’asar da yake, wanda ada Abba ne a wajen. Ayyuka Aslam yake yi bashi da lokacin kanshima, kuma daman hakan yake so dan hakan ya tsarawa kanshi tun farkon komawarshi UK d’in, yana k’ok’arin kullum yaga ya zama busy dan kar ma ya bawa kanshi daman yin tunani.. Aikin kuwa ya taimakeshi ta b’angarori da dama dan Yana da nashi campny d’in a chan, na sarrafa takalma wanda k’wazonshi guminshi da kuma taimakon Granpa wanda yake aika mishi kud’i kamar hauka suka taimaka masa ya had’a ya bud’e wanda yanzu naji suna cewa yanaso ya bud’e wani branch d’in anan ko kuma ya dawo nan ma, gaba d’aya. Kuma akwai wani daban da zasu bud’e na zanen gidaje shi da Abba! Ga mt ga kuma karatu wanda a yanzu ya kammala PHD d’inshi… A b’angaren nasarori Aslam ya samu kam ba a magana sai dai kuma shi duk basa gabanshi, inda za ace ya tatttara ya bada abashi lafiyan Mahaifiyarshi na tabbatar kafin k’iftawar ido zai iya sallama komai! Ba shi kad’ai ba hatta mu duk tsawon wannan lokacin buri daya muke da shi shine ‘Aisha ta warke hankalin kowa ya kwanta’ Dan shi kanshi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96