Chapter 58
Chapter 58
with you?” Yayi maganar referring to Auwal d’in. “Nothing” kawai ya iya cewa yana sunkuyar da kanshi k’asa. Murmushi Abban yayi, dan kamar yad’an gano Auwal d’in amman sai ya basar kawai aka fara cin abinci. Arshaad ke zaune a kusa da Aslam Abba kuma na ata gefenshi (sun saka shi a tsakiya) Duk su biyun suna lura da yanda yake kallon Hudan wadda ke opposite d’insu akai akai! Gaba d’aya Arshaad sai yaji ya damu sannan bai ji dad’in hakan da Aslam d’in yake yi ba kwata kwata! Amman sai yayi ta k’ok’arin kawar da duk wani negative thinking a kanshi. Ita kanta (Hudan) a takure take, gashi zuciyarta ta hanata sukuni. Loma biyu kawai Sakina ta iya yi cikin kwanciyar hankali dan tunda Auwal ya fara mata ‘Hi’ ‘How are you?’ D’insa taji wani malolo ya tokare mata mak’oshi! Bata san lokacin da ta ajjiye spoon d’inta da k’arfi ba wanda hakan ya janyo hankalin kowa kansu… Dariya Abba yayi dan tun d’azu yanata lura da su, cikin dariyar yace “Ya takura miki ko?” Da sauri tace “Eh wallahi Abbac kace mishi....” Kasa k’arasawa tayi sakamokon zungurinta da Hudan tayi, k’asa k’asa tace “kinga Daddy fa yanda yake kallonki, ki yi shiru” Kallon inda Daddyn yake tayi, karaff! Taga itan yake kallo yana d’an murmushi, gaba d’aya sai kunya ta lullub’eta tayi k’asa da kanta. Y’ar guntuwar dariya Daddyn yayi kafin yace “K’arasa mana Sakina… Ace mishi ya daina takura miki ko?” Cikin dariyan ya kalli Auwal kafin yace “Auwal, Allah har a gama cin abincin nan kar inji ta sake kawomin k’arar ka!” Shi dai Auwal shiru kawai yayi kamar ruwa ya cinye sa.. Arshaad kuwa dariyar mugunta yake yi mishi a ranshi yace “Allah mai had’i!” Don ya tabbata Auwal sai yaci kwal ubanshi a hannun Sakina. Daddy kuwa kallonsu yake ta yi lokaci zuwa lokaci….tabbas daman ya d’an fahimci akwai abunda yake damun Auwal kuma yake kaishi side d’in Abba! Kenan wannan Yarinyar ce, but yaga kwata kwata Yarinyar bata da interest a kansa shi kuma gashi ya fahimci tsakani da Allah Auwal d’in nasa yake son Yarinyar. A zuciyar shi ya hau adduar ‘Allah ya karkato da hankalinta ga Auwal d’in a samu yayi aure ya bar wannan tsalle tsallen, dan tabbas ya hango nutsuwar d’an masa a tareda Yarinyar……. Har aka kammala, Auwal bai sake yi mata magana ba. Sai da aka d’an tab’a hira tukunna aka watse. Arshaad na son ya gana da Hudan amman Abba yayi kane kane! Har d’aki suka rakasu shi da su Sudais kamar d’azu… Sakina ce ta kawo musu tofi suka yi sallama suka tafi shi da Aslam..... Suna shiga d’akin, suka hango wayar Hudan dake kan gado tana kyalli, da sauri Shuraim ya k’arasa yaje ya d’auko dan yanayin tafiyar tata kafin ta isa kiran zai iya tsinkewa, amman dukda hakan kafin ta kai ga amsawa kiran ya tsinke. Gabanta ne ya fad’i ganin 20 missed calls d’in Mama akan screen d’in, tana shirin kira wani kiran ya sake shigowa…. Tana amsawa taji Maman ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Duk hankalina ya tashi na d’auka jikin naki ne ya motsa.” Murmushi Hudan tayi tana k’arasa zama a kan gado kafin tace “Da sauki Alhamdulillah, ai na fad’a miki na warke fa Mama ki daina d’aga hankalinki.” Ajiyar zuciya Mama ta sauk’e sannan tace “Gobe zamu zo mu dubaki ni da Ummu in shaa Allah.” Hudan, cikin d’an zaro ido na murna tana murmushi tace “Na gode kuwa sosai Mama zan ji dad’i, sai kin zo.” Murmushi itama Maman tayi kafin tace “take care, kina dai shan maganinki ko? Na sanki da k’in shan magani.” Cikin yin y’ar dariya Hudan tace “Maama kin manta Sakina na tare dani.” Y’ar k’aramar dariya taji itama Maman tayi kafin tace “Hakane fa, sai mun zo goben in shaa Allah, Hajiya ma tace a gaida ke!” A hankali Hudan tace “kiran ki tayi? Kun shirya? Na ga rannan ma tayi miki magana a gida lokacin a gaban kowa.” Ajiyar zuciya Maman ta sauk’e kafin tace “Kirana tayi takanas Hudan dan taji jikinki da kuma yanda nake” ta k’arashe maganar tana share hawayenta. Murmushi Hudan tayi itama kwalla ta zubo mata, kafin tace “Alhamdulillah” Tana share hawaye sannan tace “Sai kun zo Mama” Tana murmushi, itama murmushin tayi sukai sallama ta kashe wayar. Cike da nishad’i Abba dake tsaye a kanta yace “Y’ar gidan Mama” Cikin yanayin zolaya. Cikin d’an murmushi tace “Wai hankalinta ya kasa kwanciya gobe zata zo ta ganni” ta k’arashe maganar cike da zumud’i. Murmushi Abban yayi sannan yace “Allah ya kaimu goben” ya shafa kanta tukun ya juya ya fita. “Sai da safe” Shuraim yayi mata, Sudais ma haka, yayi pecking cheek d’inta sannan ya fita. A hankali ta kwanta ta lumshe idanunta ahaka Sakina ta shigo ta sameta. Nan take fad’a mata good news d’in! Ta kuwa yi murna, sannan tace “Ai daman lokacin dana ce mata har a asibiti kika kwanta baki ji yanda hankalinta ya tashi ba, daman na san ba lalle ta iya hak’ura ba, sai tazo. Allah ya kaimu goben ya kawosu lafiya.” A hankali Hudan tace “ameen” tana hamma...... Tun da suka tashi da safe suke expecting d’in su Mama, har girki suka d’anyi musu dukda rashin k’arfin jikinta sai shirye shirye suke yi. Suna cikin setting dining Abba ya shigo, murmushi yayi a ranshi yana yaba irin k’aunar da y’ar tasa take yi wa Maman ta. Sai da yazo ya dafa kanta tukunna ma ta fahimci ya shigo. Gaishesa suka yi ya amsa musu cikin kulawa kafin yace “Suje da Linda (mai girki) ta bata kayan wankinsu da suka tara, masu wanki zasu fara. Da mamaki yake kallonta, jin tace “Ai su kullum In suka cire kayansu a washing machine suka sakawa su wanke” Sannan ta k’ara da cewa “Akwai fa washing machine a toilet din nawa Abba” Murmushi yayi ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace mata “Na wanke inners ne wannan dota. Next time ku tara akwai masu wanki da guga da suke yi, time to time. Yanzu ku bata kayan ta kai musu sai a goge” Da ‘to’ suka amsa ya wuce Sakina ma ta kira Linda suka wuce domin ta bata kayan, ta bar Huda anan tana ci gaba da setting dining. Sai bayan sallar azahar, Ummu tayi musu waya tace “su fito, suna waje.” Sai da suka gayawa Abbas tukunna suka fita…. Babu yadda basu yi da su ba akan su shigo ciki amman suka k’i shiga gidan. Sun d’an jima a wajen, dan ma unguwar ba mai mutane da yawa bace ba dan babu k’afa a layin, shima titin shiruuuu. Daga baya Mama ta bawa Hudan ledar su tsami gayen da tace ta taho mata dasu. Aikuwa taji dad’i sosai, ta dinga murna, nan Mama ta cewa Sakina “kar su durfafi mand’on suyi ta sha fa dan in suka sha da yawa zai kunche musu ciki.” Mama, tunda sukazo dama taga wata adaidaita sahu tayi parking, sai yanzu taga mai mashin d’in yana juyowa, kamar ance ta kalli cikin napep d’in suka had’a ido da Baba! A take gabanta ya yanke yayi wani irin fad’uwa! Sannan zufa ta hau keto mata ta ko wacce
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96