Chapter 77
Chapter 77
kuwa Arshaad?” Da sauri ya matsa sosai inda take idanuwanshi har sun cicciko kamar zai yi kuka ya d’aura hannunsa ya rufe mata baki kafin yace “Mammy pleas...” Bai k’arasa ba ta buge hannun cikin tsananin b’acin rai tace “Kar ka yi mini ‘please’ bana son ji! Kun riga kun nuna min matsayi na da kai da ubanka! Naji nagani kuma na fahimta, akwai lokacin da na ware muku kai da shi zan waiwayeku amman ba yanzu ba dan wallahi sai kun san kun wulak’anta, hak’urina ya k’are a cikin gidan nan! Amman yanzu akwai boss d’in da ya kamata mu fara kashewa ni da kai a yau kafin komai.” Bata jira jin me zai ce ba taci gaba “Naji labarin za kayi aure! Jibi ko? To wallahi bari kaji In dai sunana Rukayya kuma nonona ka sha to wallahi muddin ka auri wannan Yarinyar ni kuma a ranar zan tsine maka......................” “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Itace kalmar da Arshaad yake ta nanata wa a ranshi! Ya kasa motsi ya kasa cewa komai…… A ranshi yace “Wannan shine abunda nake gudarwa since day 1, ya zan yi da Mammy, ya zan yi da zuciyata wadda na san muddin aka fasa aurena da Hudan tabbas tarwatsewa za tayi”. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 51 Mammy tana gama fad’in haka ta wuce sama, haka Aaima itama ta bi bayanta tana jin kamar an tsundumata a Aljannah! Suka barshi shi kad’ai a tsaye. A hankali ya nemi kujera ya zauna ya sunkuyar da kai sannan yasa hannu ya dafe kan da hannu biyu.. Yafi minti ashirin a haka, chaan! Ya ji an dafa shi, yana d’agowa suka had’a ido da Dad. Kallon shi Dad d’in yake yi trying to fassara yanayin da yake ciki. Da sauri Arshaad ya mik’e tsaye ya fara k’ok’arin saita kanshi, cikin k’ok’arin danne abunda ya tokare mishi k’irji yace “Ina wuni Dad” Sai da Dad d’in ya d’an k’uraa mishi ido tukun yace “Lafiya kake kuwa?” Murmushi kawai Arshaad d’in ya k’ak’alo kafin yace “Alhamdulillah! All is fine na gaji ne kawai, bara inyi freshening off in kwanta” Ya k’arashe maganan da k’ok’arin barin wajen dan ya lura da kallon da Dad d’in yake mishi so yake ya gane yanayinshi ne. Har ya d’anyi gaba yaji Dad d’in yace “Arshaad” Tsayawa kawai yayi ba tare da ya juyo ba. Ajiyar zuciya Dad d’in ya sauk’e kafin a hankali shi ya taka ya k’arasa inda yake ya tsaya a gaban shi yasa hannu ya dafa kafad’ar shi, cikin kulawa ya fara magana “Son, irin haka is normal! Most a times couple basa tashi samun matsala sai ya rage y’an kwanaki kad’an aurensu.. Ka kwantar da hankalin ka kar ka sa komai a ranka, za ku hirya soon komai ya wuce kamar bai faru ba. Wannan duk aikin shed’an ne so karka bari yayi galaba a kanka. Allah yayi muku albarka.” Cikin sigar zolaya ya ci gaba da cewa “Nan da jibi fa ka zama magidanci, a nan ne zaka fara facing real life da real issues So garama ka shirya! Kar ka bari small things irin haka suyi breaking naka.” Da k’arfi Arshaad ya taune lip d’inshi na k’asa, yana jin yadda zuciyarshi take tafarfasa! Ba k’aramin kokawa yayi da makogwaro da harshenshi ba kafin ya samu su bashi had’in kai wajen furta kalmar “In shaa Allah Dad, thanks a lot.” Murmushi Dad d’in yayi kafin ya d’anyi tapping kafad’ar shi da hannunshi ke a kai yace mishi “good night” daga nan ya nufi hanyar side d’inshi, ya bar Arshaad tsaye a wajen… In banda ajiyar zuciya babu abunda Arshaad yake sauk’ewa a jere a jere. Ganin ya fara ganin duhu duhu, kar yaje ya fad’i a wajen yasa ya lallab’a ya nufi side d’inshi shima dake nan a k’asan. Da kyar ya kai kanshi toilet bayan ya ajjiye suite d’in hannunshi akan gadon. Ko agogon hannunshi bai samu ya cire ba ya yana shiga toilet d’in ya sakarwa kanshin shower ta ko’ina da ruwa mai mugun sanyi! Ya dad’e a haka kafin da kyar ya samu ya fito kayan jikinshi na d’igar ruwa.. Dai dai nan ya ji wayarsa ta hau ringing, hannu yasa a aljihu kafin ya zaro wayar k’irar iphone 13 ya kalla screen d’in! A take damuwar da ya samu ta d’an ragu ta dawo mishi sabuwa ta sake hauhawa sakamokon ganin mai kiran nasa.. Har ta tsinke bai d’aga ba kuma bai daina kallon screen d’inba! Yana a yanda yake wani kiran ya sake shigowa… A hankali hannunshi na rawa ya d’auka ya kai kunnenshi kawai yayi shiru bai ce komai ba. Cikin sanyin muryarta yaji tace “Ya Arshaad.” Ajiyar zuciya ya sauk’e ya lumshe idanuwanshi da suka yi jaaa wanda hakan ya bawa hawayen da yake ta addabar zuciyarshi daman zubowa ta ido d’aya! Kafin d’ayan idon shima ya samu damar zubo da nashi hawayen... Ajiyar zuciya kawai taji yana sauk’ewa a jejjere Hakan yasa a d’an rud’e tace “Ya Arshaad ka yi mini magana pls, baka da lafiya ne yanzu? Mai ya faru” Da kyar ya iya k’arasawa bakin gadonsa ya zauna dan ya fara rawar sanyi ba kad’an ba! Yana zama wata wawiyar atishawa ta kece mishi wanda yasa Hudan mik’ewa daga kwancen da take, kafin tace “Mura ko? Sorry sannu ka sha magani tou?” Sai a sannan taji yayi magana “Hudan!” “Naam” tace da sauri dan daman so take taji ya furta wani abun dan shirun nashi ba k’aramin tsoratata yayi ba. A hankali ya d’an yi tari kafin yace “Do you love me??” Ta d’anji kunyar tambayar amma jin yanayin shi da kuma muryarshi wata iri yasa tace “Yes, a lot” A hankali yace “Say it” Shiruu, ta d’anyi kafin a hankali yaji tace “I love you” Sai da yad’an lumshe idanuwansa kafin yace “To what extent??” Ya sake jeho mata wata tambayar. Zuwa yanzu kam yad’an fara birkita mata lissafi hakan yasa tace “Ya Arshaad meye ne yake damunka?” Tayi masa tambayar kamar zata fashe da kuka. Cikin tsare gida yace “Just answer me! How much?? To what extent za ki iya zuwa domin kiga mun mallaki junan mu??” Ita dai ba abunda take fahimta daga shi zuwa yanzu, gashi tana jin yanda numfashinshi yake seizing sama sama! Daurewa tayi tace “Kamar yaya?” Dan da gasken bata fahimta ba. Da kyar ya dedeta numfashinshi kafin yace “Idan Mama tace ki hak’ura da ni, za ki hak’ura?? Sai da ya sake maimaita mata tambayar tukunna tace “Maama ba zata tab’a cewa In hak’ura da kai ba! Meyene ya faru na kasa gane komai” Bai bata amsar ba sai cewa yayi “Idan Maama tace ki hak’ura da ni, za ki hak’ura??” Ta kasa fahimtar inda ya dosa, kawai sai ta yanke shawarar ce mishi “Ya Arshaad ai albarkar iyaye shine abinda ake buk’ata! In basu da niyyar sakawa meye amfanin auren da za ayi babu albarka?” Rintse idanuwansa yayi da k’arfi! Tuni numfashinshi suka fara korar juna… She can feel it dan haka duk sai ta sake rud’ewa ta hau kiran sunan shi amman yak’i kulata, k’arshema wani irin tari taji yana yi, yayi kusan 3 minutes yana tarin Hudan tana kuka tana kiran sunanshi amman shiru wanda hakan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96