Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 86

Chapter 86

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Sakina suka take musu baya. Hudan, so take ta yakice tunanin Arshaad a kanta amman ta kasa! K’arshema bigewa tayi da adduar Allah yasa tana fita ta ganshi amman yanayin yanda taji an zaunar da ita a doguwar kujerar da aka k’awata domin ita da shi ne yasanya ta fahimci bai zo d’inba. Ummu ce ta fito ta bud’e taro da addua sannan ta fara gabatar da al’ada a Huda, A matsayin uwa. Mama suna parlourn Madu, tun lokacin da Mommy da Aslam suka zo suka buk’aci ganinta har yanzu bata samu damar fitowa ba. Wata distant relative d’in Shuwa wadda zata d’an girmi Shuwan kad’an ce ta k’arasa wajen sannan cewa Ummu “Ina uwar Angon? Ta zo ta zauna a kusa da ke yadda kina gamawa zata karb’a. Sannan ba ayi welcomin Ango ba kuma ba aga shigowarsu ba besides ai dole sai yananan ma tukunna za ayi komai. Na ga bai riga yazo ba amman kin yi wuff kin fara abu haka bayan kuma akwai abubuwa da yawa before wannan.” Karaf! A kunnen umma. Daman neman abun yi suke yi ita da Anty Zainab shiyasa suka zo suka zauna a k’asa gefen kujerar Amarya. Da sauri sannan da d’an k’arfi yadda ta tabbatar kowa zai ji Umman tace “Eh kam tabbas!” Sannan ta mik’e tsaye kafin tace “Uwar Ango! Tana Ina? Ana buk’atar Uwar Ango a nan yanzu yanzu” Da k’arfi ta yadda kowa ya iya jiyota tunda daman wak’ar da aka kunna a low tune yake kuma iya murya ne kawai babu kid’a. Da sauri Ummu tace “Umma meye haka? Idan kin yi min magana ba zan je In kirata baneba? Ko hakan da kika yi kina tunanin shi zai sa ta fito?” Still da k’arfi Umma ta sake cewa “A’a, ai ji nayi kamar kince bata zo ba! Gashi shima Angon shiru. Duk da dai ni ba Shuwa bace ba amman Tabbas na asan cewa Ango da Amarya a tare ake shafa musu lalle, manshanu, da ragowan abubuwa! Dan har yau ina tuno naki, a tare aka shafa muku ke da Muhammadu wanda ya zo wurwuri bai tsaya b’ata lokaciba, Ita kuwa yayarki daman ba a yi mata ba shiyasa gaba d’aya auren nata duk biyun suka tab’arb’are! To kuwa kinga ai ba zan so auren Huda itama ya samu matsala ba ko? Dan haka gara mu jira Angon ya zo ko nan da k’arfe taran dare ne mu masu iya jiransu ne har sai shi da uwarshi sun zo an yi alada yadda ya kamata!”. Ta k’arashe maganar har wani karkarwa jikinta yake yi, wanda kana gani ka san bala’ine kawai yake cinta. Ummu bata ga k’arasowar Sakina ba sai tayi tana cewa “Eh tabbas kam Hajiya Umma kya zauna ai kiyi ta jira tunda daman kallon kwaf da munafurci ne ya kawo ki! Mu nan dukkannin mu munada aikin yi kuma ba mu da lokacin zaman jira har k’arfe taran dare! In dai Ango kike son gani to ki bada nan da awa biyu zaki ganshi sun iso tare shi da iyayenshi maza da za su kawo lefe wanda na tabbatar abunda ya tsaidasu kenan ba wai abunda makirar zuciyarki ta shirya miki ba!” Umma na shirin k’arasowa inda Sakinar take taga Ummu ta d’auke ta da mari! Cikin yaren Shuwa Ummu ta hau yiwa Sakinar fad’a k’asa k’asa yanda ta tabbar ba kowa ne zai ji su, tace “Baki da hankali ashe? A cikin dangi da y’an uwa za ki bud’e baki kina yiwa babbar mata rashin kunya haka? So kike a tafi dake a baki? Wuce! Wuce ki tafi chaan sama d’akin Shuwa ki rufe! Idan ba ni na neme ki ba wallahi kika fito sai ranki yayi mugun b’aci!”. Juyawa kawai Sakina tayi ta wuce tana ji kamar ta had’iye zuciyarta! A kan Umma aka mareta a gaban mutane haka!? Kuma ta tabbatar tunda Umma ta fara wannan maganganun to fa idan taka mata burki aka yi ba ko kuma Arshaad d’in ta gani ba tabbas ba zata tab’a barin mutane su sha ruwa ba. Ita daman tun d’azu da ta ganta tazo da sassafe ta san ba alkhairi ne ya kawota ba. Ita da take da abun fad’a a gindi amma shine har take da audacity d’in yin magana! Wallahi yau da Ummu ta barta da sai ta yiwa Umma zazzagar kwanyo.... Da wannan tunanin ta k’arasa d’akin Shuwa, sai a lokacin hawayen bak’in ciki suka samu nasarar zubo mata… Daga Shuwa sai Baabaa Talatu ne a d’akin suna shirya tukuicin da za a bayar in an kawo lefe. Baaba Talatu tana ganin ta shigo tana kuka ta mik’e tana “Subahanallah, mai ya faru? Ke da waye?” Da sauri ta k’arasa ta hau shafa fuskarta inda hannun Ummu ya fito tarr!! Ya kwanta akan farar fuskarta Cikin fad’a Baaba Talatun tace “Wanne d’an iskan ne ya mare ki??” Fashewa tayi da kuka cikin kukan tace “Umma ce take ta abubuwa a waje, shine Ummu ta mareni wai dan....” Ai bata tsaya jin k’arshen ba, tayi waje. Shuwa ce ta iya daurewa ta tsaya ta ji labarin Sakinar tukunna ta mik’e itama tace mata “ta zauna a d’akin, kar taje ko ina . Bari taje taji ba’asin abunda yasa Angon bai k’araso ba...........” BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 53 Shuwa ce ta iya daurewa ta tsaya ta ji labarin Sakinar, tukunna ta mik’e itama tace mata “ta zauna a d’akin, kar taje ko ina. Bari taje taji ba’asin abunda yasa Angon bai k’araso ba.” “To” Kawai Sakina tace, tana mai sake goge fuskarta sannan ta koma gefe ta fara warware laffayar jikinta da d’aurin d’ankwalin dake kanta.. Sai da ya rage daga ita sai long camisole d’inta wadda ta saka a ciki mai dogon hannu yayinda dogon gashinta ya kwanta a gadon bayanta sannan ta fara k’ok’arin kiran Arshaad... Tayi mishi misscalls sun fi ashirin amman shiru. Dan haka nan da nan hankalinta ya sake tashi…. Tun jiya take danne zuciyarta take k’ok’arin kawar da maganar da Aaima ta gaya mata a cikin kwakwalwarta amman kuma attitude d’in Arshaad da k’in zuwanshi a yanzu ya yi matuk’ar bata tsoro. Ba wadda take jin fargabar taji wannan batu irin Hudan shiyasa jiya ta kwana Sallah akan Allah yasa maganar Aaima ta zama k’arya idan kuma gaskiyace Allah yasa su Abba su gyara lamarin cikin sauk’i… Gaba d’aya hankalinta a tashe yake dauriya ce kawai take yi, tana kuma k’ok’arin taga ba wanda ta bari ya ma ji zancen har a samu a gyara lamarin in sha Allah. Ganin arshaad d’in bashi da niyyar amsa ta ne yasa kawai ta kira Auwal dan taji me ke faruwa a ina aka tsaya.. Shi sai a bakinta ma yake jin wai ‘Arshaad d’in bai je ba’ Saboda shi suna asibiti. Ganin kamar bai san me yake faruwa ba ya sanya taja bakinta tayi shiru saboda ance yawan yayata magana kan iya tabbatar da gasgatuwar ta. Dan haka kawai sai tace mishi “ya duba musu Arshaad din pls” Daga haka suka yi sallama. Daman shima yana da shirinshi zai je wajen So yanzu zai duba Arshaad d’in sai su wuce tare kawai dan haka ya cewa Dad “Bara yaje gida, Sakina ta kirashi wai

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});