Chapter 87
Chapter 87
har yanzu Arshaad be k’arasa ba.” “to” kawai Dad d’in yace masa. Yana fita shima Dad din ya d’au waya ya kira Gwaggo Asabe yace “Dan Allah tazo ta ji da Ummi. Zai yiwa drivern da zai kawota kwatancen asibitin da suke....” Drivern da ya kawota (Gwaggwo Asabe) shi ya maidashi mansion d’in. Yana zuwa ya tarar da Daddy ya shirya chap yana jiranshi da akwatuna dozen biyu sun sha decoration sai kuma basket na gift guda biyar, da akwatunan uwa uba gwaggwo da kawu.. Duk sun had’a. Tun sassafe Mommy ta aiko da kayan shi kuma ya duba ya tabbatar komai dai dai. Sai da aka gama loda kayayyakin a motoci wajen goma tukunna Abba ya fito da shirin shi shima da alama rakasu zai yi! Dad, yana shirin shiga mota har driver ya bud’e mishi k’ofar motar ya hango tahowar Abba! Wani takaici ne ya d’ebesa bai san lokacin da ya daka masa tsawa ba! Yace “Idan ka k’araso nan wallahi sai mun kwashi y’an kallo ni da kai! Kaji dai na rantse wallahi!!” Ya k’arashe maganar yana mishi nuni da yatsar shi manuniya yana nuna sama. Ajiyar zuciya Abban ya sauk’e kafin yace “Dad nimafa rakaku zan y....” Cikin fushi Dad d’in yace “Kaga mota nan, zo ka shiga! Amman direct Asibitin da aka kwantar da Ummi zaka je Idan kuma ba haka ba to ka koma ka zauna a ciki. Zab’i d’aya!” idanuwa direbobin da masu aikin suka tsura musu..Ganin da Abba yayi har sun fara kwasar y’an kallon kamar yadda Dad d’in ya ambata ne yasa kawai ya juya ya koma ciki ranshi a mugun b’ace!. Tsaki Dad yayi ya shige motar yana mai cewa “Ba za ku haukata ni ba, wallahi!”. Shi dai Daddy shiga yayi ya zauna a kusa da shi, yana son tambayarshi wata zuciyar kuma sai ta bashi shawarar ya bari ya Dad d’in ya d’an sauk’o tukunna sai suyi magana… A haka drivern ya ja su suka nufi Gandun Albasa Daddy yana mamakin meye haka yake damun Dad?? Dan tabbas ya san akwai abunda aka yi mishi...... GANDUN ALBASA. Baaba Talatu tana fita harabar gidan ta tarar gurin har ya fara kachamewa! Dan bayan Sakina ta bar wajen Umma da Anty Zainab kan Ummu suka dawo wai “ai itace bata yi mata tarbiyya mai kyau ba shiyasa ta raina manya har haka...” Ga kuma wannan tsohuwa ita ma ta kafa ta tsare tace “Sai Ango ya fito tukunna za a fara gabatar da komai!” Yayinda Ummu da wasu cousins d’inta suke ta k’ok’arin ganin sun yayyafa wa lamarin ruwa amman abun ya faskara!. Baaba Talatu ce ta k’arasa ta ja wannan tsohuwar gefe suka had’u ita da Shuwa suna mata magana k’asa k’asa… Ganin kamar ana shirin fara traditional event d’in cikin kwanciyar hankali ne yasanya Umma ta sake cewa “Nima fa kamar uwa nake a wajen Hudan! Dan haka ba zan bari kowa ya tab’a ta ba har sai Angon nata ya k’araso.. idam kuma fasawa yayi ne to kawai a fito a fad’a wa mutane sai a fasa sakata a lallen, dan ba girman mu bane mu tsaya muna yiwa mutane wasa da hankali! Ko ya kuka gani?” Ta k’arashe maganar tana kallon cousins d’in Ummu waenda suke gefen ta! Ba su kad’ai ba kusan kaff wajen babu wanda bai ji abinda tace ba hatta su Shuwa. “Ga Angon nan” Muryar Mommy wadda suka fito su uku yanzu ta daki dodon kunnuwansu! Da sauri Mama da Aslam suka kalleta! Ba tare da ta kallesu ba ta kama hannun Aslam ta fara janshi Mama na binsu a baya kamar rak’umi da akala shi kuma yana binta!.. Bata cikashi ba sai da ta kaishi gefen Hudan sannan ta zaunar da shi. Da sauri Ummu ta matso k’asa k’asa tace “Mommy a Al’ada fa dole sai Angon zai.... Cikin katseta Mommy tace “A addini fa?” Bata jira Ummu ta bata amsa ba ta sake ce mata “Kalla nan kinga” Tayi maganar tana nuna mata Huda wadda sai a lokacin Ummu ta lura da yanda mayafinta ya jik’e sharkaf! Wanda kana gani ka san ruwan hawaye ne… Mommy bata jira jin me zata ce ba ta ci gaba da yi mata magana k’asa k’asa irin na masu hankali, tace “Saboda ita kawai ki bari ayi a gama! Na tabbatar ba wai rashin zuwan Arshaad kad’ai bane ya saka ta kuka ba! Har da maganganun matar nan! Tun muna parlourn bayankun nan muke juyo komai. Dan Allah kar kice a’a! Kalla kiga mutane kowa ya zuba ido an fara k’ananun maganganu, na tabbatar in dai ba Angon suka gani ba to haka za a tashi ana gulmace gulmace shima kuma sai idan an samu waenchan matan sun bari anyi d’in kenan. Na tabbatar mutane k’alilan ne kuma na jikinku sosai suka san ba Arshaad bane wannan, ba kowa ne zai gane ba so dan Allah ki kwantar da hankalinki ayi abun nan a gama without any more dramas. Saka lalle ai ba d’aurin aure bane ba, ba komai kawai bidi’a ce so mu bisu kawai ayi a gama.” Tana gama fad’an haka ta juya ga jamaar wajen tace “Kuyi hak’uri mun yi latti wani d’an uzuri ne ya tsaida mu! Sunana Hajiya Aisha Maman Ango, mun gode kwarai da zuwanku dan taya mu farin ciki.” Daga nan ta juya ta cewa Ummu “Ni zan fara ko ke?” Da murmushi kwance akan fuskarta. Kallonta kawai suke yi daga Ummu har Mama.....…… Mama da Ummu sun so hana mai video coverage da pics d’auka amman ganin yanda hankalin kowa yake a kansu da kuma Mommy wadda tace ‘su bari kawai tunda ga wasu ma a gefe suna ta d’auka da waya’ ne ya sanya kawai suka hak’ura. K’awayen su Huda kuwa abun ba k’aramin d’aure musu kai yayi ba dan tabbas sun san wannan ba da shi akayi cocktail jiya ba, kuma ba shine a pre wedding ba! A haka dai suka bar maganar akan in an tashi za suni komai a bakin Sakina.... Aslam kuwa so yake ya mik’e amman sam ya kasa! Ya rasa dalili..tun da yake bai tab’a jin fargaba irin wadda yake ciki a halin yanzu ba! Ana cewa k’afafuwa da gangar jikin mutun suna sagewa ya koma kamar gunki bai tab’a yarda da hakan ba sai yau da ya faru a kansa dan hatta kwayar idanunsa ya kasa juyawa, so yake ya runtse idanuwanshi ya samu ya dedeta zuciyar shi amman sam ya kasa! Yana nan a haka yaji Ummu na rufa mishi wata jibgegiyar alkyabba akan jamfar jikinshi Akan hular kanshi Ummu ta d’aura mishi wani jan kyalle mai tambarin moon a gaba golden colour (Allah yaso suna da extra) Daga nan ta mik’a mishi wata sanda wadda ta ci ado! Tace masa “ungo, rik’e” Mommy ce ta kama hannunshi ta sanya mishi sandar sannan ta had’a da nata hannun ta maste! Sai a lokacin ya samu nasarar lumshe idanuwanshi sannan ya d’an bud’e su kad’an yana kallon k’asa.... Ba tare da b’ata lokaci ba aka fara gudanar da alada…….. Bayan uwar Amarya da uwar Ango sun yi, ragowar jama a suma suka zo suka sanya musu suka basu gift daga nan aka fara serving abinci. Sai a lokacin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96