Chapter 52
Chapter 52
hankali Sakina wadda duk jikinta yayi sanyi jin za a rabata da best frnd d’inta tace “Anjima ma ji me su Mama za suce, in munje.” Cikin girmamawa suka gaisheshi ya amsa da kulawa yana ce musu “ai da sun fara kawai” Sai da suka kammala ya kalli Hudan yace “ki cewa Arshaad idan ya dawo a office ya zo, ku zo tare Ina son ganin ku!” Da “to” ta amsa, shi kuma ya tambaya ko “akwai abinda suke buk’ata zai fita shima” a hankali tace “a’a” sukai yi mishi a dawo lafiya, ya wuce. Gidan shiru, daga su sai masu aiki… Tun lokacin da Abba ya fita take nazari a kanshi, kamar akwai abunda yake damunshi, dan har sai da ta yiwa Sakina maganar… Murmushi Sakina tayi kafin tace “Hudan he just knew you fa, kuma yanzu ana shirin aurar da ke, dole yaji ba dad’i mana.” Jikinta itama duk sai yayi sanyi, ba abunda yafi d’aga mata hankali, irin barin k’asar da Ya Arshaad yace za suyi, ta san aure dolene dama wata rana za tayi shi, but bata tab’a kawowa nan kusa ba, kuma ba a k’asar ta ba. Haka dai ta wuni ranar sukuku kana ganinta tashi d’aya zaka fahimci akwai abinda yake damunta! Ko da Sudais ya shigo musu shi da Sakina suka yi ta shirmen su tana jin su k’arshema kwanciya tayi ta lumshe idanunta kamar mai bacci Sakina kanta k’arfin hali kawai take yi tana daurewa, dan bataso itama ta zama moody kamar Hudan ta sake d’aga mata hankali. Kafin Magriba Arshaad d’in yace mata zai dawo, so tana gani 6 yayi ta mik’e ta isa parlourn Abba. Knocking tayi aka bata izinin shiga, a hankali da sallama ta tura k’ofar ta shige ciki. Aiki ta sameshi yanayi tuk’uru ga takardu da computer a gabanshi takardun duk a zuzzube. Suna had’a ido yayi murmushi ya ture kayan aikin gefe ya bata dukkannin attention d’inshi bayan ya nuna mata gefen shi inda yake zaune a 2 sitter yace “ta zauna.” Bayan sun gaisa ba tare da b’ata lokaci ba yace mata “Dad d’in Arshaad jiya ya kirashi akan maganarsu ..... Yayi mata bayani dai dalla dalla kamar yadda Arshaad yayi mata jiya” Kafin ya k’ara da cewa “Kina son shi! In ba kya sonshi ki fad’amin, ba zan bari ki auri wanda ba kya so ba!” Just say watever it is that you feel towards him ko friendship ko love ko ma meye just feel free to tell me” Ya k’arashe maganan yana kallonta da dukkan hankalinshi. Shiruuu, tayi tana d’an jin kunyar cewa Abban tana son shi k’iri k’iri, dan haka tace “Abba mun ma shirya mun daina fad’an, duk abunda kuka yanke dai dai ne.” Ya fahimceta sarai amman yace “Kina sonshi kenan? Za ki aureshi?” A hankali ta d’aga kanta, sannan tayi saurin rufe idonta da tafun hannunta. Murmushi yayi, bai ce komai ba, daga nan d’akin ya d’au shiru. A hankali Hudan ta aro jarumta kafin tace “Daman Abba akwai wata magana danake ta so in rok’e ka” Kallonta yayi kafin yace “Un hm, Ina jinki” A hankali tace “akan su Ummi ne Abba dan Allah ka..” Tun kafin ta k’arasa yace “Maganan ya fita a hannuna tun tuni, so karki sake min maganan bana son ji.” Ganin da tayi kamar ranshi ya b’aci ne yasa tace “Sorry Abba” A hankali ya sauk’e ajjiyar a zuciya kana yace “It’s okay” Dai dai nan suka ji ana knocking! Izinin shigowa ya bada, hakan ya sa ya turo k’ofar a hankali ya shigo… K’amshin turarenshi ne yasa ta ganeshi! Me kuma ya zo yi? Ta yiwa kanta tambayar a cikin ranta. Bata gama wannan tunanin ba, ta ji muryar Arshaad yana sallama alamun tare suka shigo. Rashin nutsuwar da takan tsinci kanta a ciki ne ya ziyarceta a take, lokaci guda!. Akan kujerun suka nemi wajaje suka zazzauna. Sai da suka gama gaisawa da Abban tukun ta juya ta gaidasu A hankali Aslam yace “Lafiya Alhamdulillah” Arshaad kuma yana d’an murmushi ya d’aga mata gira d’aya yace “fine” a hankali. Murmushi tayi itama ta maida kanta k’asa. A hankali Aslam ya lumshe idanuwanshi kafin ya bud’e yace “Abba, Arshaad yace wai akwai meeting inzo kana son ganinmu” Murmushi Abba wanda ya fahimci Arshaad d’in yayi kafin yace “Ni shi kad’ai na kira, sai dai kuma na lura har kunyar surukai ta fara shiga tsakaninmu tunda gashi sai da ya nemo d’an rakiya.” Murmushi Arshaad d’in yayi ya sunkuyar da kanshi k’asa yana danna wayarshi dan gaskiya Abban ya fad’a sam bai san daliliba amman wata kunyarshi yake ji kwana biyun nan. D’an murmushi kad’an Aslam d’in yayi yana mai sauk’e ajiyar zuciya. A hankali Abba ya sauk’e ajiyar zuciya shima kafin yace “Mun gama magana da Huda saura kai” Har zai fara magana sai kuma ya juyo yace “Daughter akwai wani abun da kike son sanar dani ko shikenan?” A hankali tace “ba komai Abba duk na fad’a kawai dai maganar zuwa wajen Mama ne, k’arfe nawa?” Murmushi yayi yace “bayan isha zan kaiki ku shirya ko?” Da “to” ta amsa tana murmushi kafin ya sallameta tayi musu sallama, ta wuce. D’an gyaran murya Abba yayi kafin yace “Arshaad!” Jin yanda Abban ya kirasa yasa Arshaad d’in d’agowa yana kallonshi with full attention. “No need na In tsaya tamabayar ka ko kana son Hudan tunda gashi duk ka fad’a mana ko? But inaso In sake tabbatarwa tunda kaga shi aure ba abun wasa bane, sannan kuma inaso ka tsayar da kanka da hankalinka waje guda kafin a gama magana, dan naji Dad yana cewa 2 months kawai za a saka bikin saboda tafiyarka! So kaga kar aje abu ya taho kuma kuzo ku fara inda inda, bayan ba wannan lokacin.” D’an tari kad’an Aslam yayi, kafin ya mik’e tsaye yace “Abba Ina zuwa, i’m thirsty” Bai jira jin me zasu ce ba ya fice daga parlourn ya sauk’a chaan k’asa. Yana fita Abba ya ci gaba da cewa “Sannan magana ta biyu! Why do you hide Hudan away from me?? Meye shirinka? Bana so ka b’oye min komai” A hankali Arshaad ya lumshe shanyayyun Idanunshi, kafin ya bud’e su ya d’aura akan Abban sannan ya fara magana “Abba ba 2 months ba, ko nan da 2 days ne aka yanke ranar aurenmu, I’m ready in auri Hudan dan ita nake so, so na tsakani da Allah, Ita nake son aura in rayu da ita har abada, na yanke wa kaina wannan decision d’in 3 years ago and I don’t think akwai rana d’aya dana tab’a jin tunanin sauya decision d’ina. Magana ta biyu kuma Tabbas na fahimci wacece Huda, tun ranar da muka had’u da Mama a graduation d’inta saboda naga pictures d’inta (Mama) da yawa a locker d’inka da sunan ta and everything a time d’in da kace in tayaka, parking. But I’m really sorry Abba i was selfish back then, shiyasa na k’i fad’awa kowa har ita (Hudan) dan na san no mattarr how much I love her itama take sona muddin iyayenta (b’angaren uwa) suka fahimci waye ni to ba zasu tab’a yarda da auren mu ba duba da issues d’in da suke tsakanin families d’in kuma kaima it
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96