Chapter 51
Chapter 51
don bashi da wani sauran energy, gaba d’aya jikin shi yayi lakwass!!!. Sakina kuwa so take ta gama da Jalila ta koma kanshi idan bai daina yi mata wannan kallon k’urillar ba!. Hudan tana lura dasu, dan haka ta gama aiyyanawa a ranta suna komawa d’aki zata zaiyyanewa Sakinan waye shi!! Kar ma ta soma bashi fuska dan ita tun zuwan su Munjibir park ta gama aminta da Auwal ba mutumin kirki bane ba!. ...duk sunyi shiruuu, kowa da abunda yake tunani a ranshi. Nishi suka fara ji sama sama, da sauri duk suka juya kanta.. Wani lumlumshe ido take yi tana layi, kafin ta tafi luuuu ta fad’i akan kafet d’in! Da mugun sauri Sakina ta d’auki robar ruwan dake gefenta ta nufeta, ta na zxuwa ta bud’e murfin ta kelaya mata ruwan mai mugun sanyi dan har da k’ank’ara k’ank’ara ma a ciki!! Ai kuwa a firgice Jalila ta bud’e idonta tana wani mugun tari dan ruwan har cikin hancinta ya shige sosai…. Da kyar ta samu ta seseta kanta ta fara k’ok’arin mik’ewa, tana mikewa kuwa ta d’aga hannunta zata zabgawa Sakina mari shi kuma Arshaad a take ya rik’e hannun da sauri. Wani kalan shock taji a jikinta da wani sanyi a zuciyarta wanda ya sanyata kasa yin motsi! A hankali ta lumshe idanunta tanajin yanda laushin hannun nashi yake ratsa jini tsoka da b’argonta. Muryarsa ce ta dawo da ita duniyar su, jin cikin fad’a fad’a yana cewa “Jalila kin fara isata wallahi ranki zai yi mugun b’aci! Inada abun yi amman kin tsaya sai b’ata mana lokaci kike yi!! Sannan meye na yunk’urin marin nata da kika yi? Ina taimakarki tayi? Kar ki kaini bango, ranki zai b’aci wallahi kinji dai na rantse!!.” Ya fad’i hakan cikin tsananin b’acin rai sannan yayi wurgi da hannun nata, ya wuce ya k’arasa ya durk’usa a wajen, ya fara kokarin dafawa…. Kuka kawai yaji Huda ta saka dan haka da sauri ya sago ya kalle ta. Cikin kukan tace “Ya Arshaad da Allah fa na had’a ka, nace maka komai ya wuce amman still kak’i ka yarda ka hak’ura, itama Ya Jalilan ku barta kawai, ni na fahimci gaskiya, dan Allah ku daina , Al Qur’ani fa ba abun wasa bane ba..” Tana gama fad’an haka ta juya ta haye sama da gudu,,tana kuka. Mik’ewa Arshaad yayi ya dafa kanshi, ya kusan one minute a haka kafin ya juya yana kallon Sakina yace “Kice mata nace idan cikin ya kai 5 ko 7 months in shaa Allah za aje ayi dna test, plss kar tace a’a,,for me.” Yana gama fad’in haka bai jira amsar Sakina ba ya juya ya fice. Haushin su ne ya hana Sakina ci gaba da zama a inuwa d’aya dasu, dan haka ta juya ta haye sama itama. Da k’arfi Jalila ta sauk’e ajjiyar zuciya, bata gama dawowa dede ba taji Auwal ya fincikota da mugun k’arfi, cikin b’acin rai yace “Wanne shirme da iskancine ya sa kika biyo shi in the first place??? Mahaukaciya mara kamun kai kawai!! Daga ji ance tazo a tafi ta shige mota ta biyo mutum zungui zungui. Wallahi yau da wani abun ya fito, toda da hannun nan nawa zan illataki, mahaukaciya kawai.” Ya k’arashe maganar yana sakin ta sannan ya juya yayi hanyar waje. Da sauri ta mik’e ta bishi….. Ba k’aramin artabu suka sha ba a wajen ma, daga k’arshe dai ya hak’ura ya mik’ata gida, yanata faman zazzaga mata ruwan bala’i! Daga nan yace “yayi grounding d’inta! Ko wajen umma kar ta yi gangancin tambayarshi Daga yau babu inda zata sake fita har sai yayi sorting out ma kanshi solution!” sannan yace “ko hanya tabi in dai ta hango Arshaad to ta chanja! Don ya lura sam Arshaad d’in bai hak’ura ba, ita kuma wawuya ce, so kasancewar su tare is very dangerous for him.” Ita dai Jalila da “to” kawai ta bishi amman a yanda take jin Arshaad a ranta ai ko labari taji ance zai bi ta waje to fa ita mai iya zuwa ta tsayane ta jira wucewarshi. A gate d’in estate d’in ya tsaya yace “ta fita!” Allah ya so ta mai gadin yaga motarshi kuma ya ganeta dan haka aka barta ta shige. Ko da Aslam yazo, Hudan Sakina ta bawa ta kai masa ruwan karatun… Dinner kam dama a k’oshe suke, gaba d’aya kunyar Arshaad take ji bataso su had’u, iyakar yadda Ya Jalila tayi ta acting ya ishi yasa ta gane gaskiya….ita sai yanzu ma take ganin shiriritarta da ta yarda da su! A gefe guda kuma na zuciyar ta tausayin Jalilan take ji. Yayinda gaba d’aya hankalinta kuma yau ya d’unguma ga son ganin Mama dan har yau Ummu tak’i d’aukar wayarta, wayar Sakina ma ta daina amsawa! Tanaso ta tambaya amman kuma bata son zuwa k’asan dan haka ta yiwa Abban message. Ba a fi mintuna uku ba, taga reply dinshi kamar haka “Ok, no problem, but let it be tomorrow.” Taso zuwa yau d’in, amman ta tura “Thanks Abba ❤️” Kawai, ta mik’e tayi sallah.. Yau basu wani zauna hira sosai ba,,ta dai fad’awa Sakina halin Auwal tace “Don taga yanata kallonta kar yazo mata da shirme” Dariyan takaici Sakinan tayi kafin tace , “First, kin dai san akwai wanda naki dating, right? Second, ga abunda ya yiwa Jalila sannan ya k’ulla makirci wai Ya Arshaad ne. And third, wallahi ni bana son irin waennann mazan kwata kwata yana yinsa bai yi min ba at first sight!”. Ajiyar zuciya Hudan tayi kafin tace “Duk cikin su Ya Arshaad shi ya fita daban i don’t know why.” Murmushi Sakina tayi kafin tace “d’an halak, gashi yana kiranki.” Tayi maganan tana mik’a mata wayar ta dake a hannunta. Karb’a tayi ta amsa bayan sun gaisa ta fara son sake bashi hak’uri amman sam yak’i yarda, a cewarshi bata laifi a gurinshi…….. Tun Sakina najin hiran su sama sama har bacci ya kwasheta bata san lokacin da suka gamaba. Ranar ansha soyayya abun ba a magana dan sai wajen 2 tukunna suka yi hanging up, suka kwanta. Bata samu magana da Sakina ba, kamar yadda ta yanke zata nemi shawarar ta jiya, sai da suka sauk’o yin breakfast… Suna zuwa suka tarar ba kowa dan haka suna zama Huda tace “Daman akwai maganan da nake ta so muyi in mun gama shiryawa” “Ok, akan me?” Sakina ta fad’a tana mai d’an juyowa ta bata dukkannin attention d’inta.” A hankali Hudan tace “Ya arshaad ne, daman already ya yiwa su Abba maganan! So yanzu jiya yace, wai ya nake gani,,jiya sun yi magana da Dad wai sun tsaida in anzo saka rannan za asa two months ne ba wani lokaci za a dauka mai tsawo ba!” “Woow” Sakina tace tana d’an zaro idanuwanta, kafin tace “Amma hakan bai yi wuri ba kuwa?” Da sauri Huda tace “nima dai abunda na gani kenan! Amman dana nuna mishi tun kafin ma In furta sai naga kamar bai ji dad’i ba. Wai shima yana so ya tafi wani course, so kafin a juya sabon session yake son samamun admission sai muje chan ni Ina degree shi kuma yana course din, nashi.” Dai dai nan suka ji sauk’owar Abba, dan haka a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96