Chapter 66
Chapter 66
bad luck bace ba?” Lumshe idanunsa kawai Aslam yayi yana nan zaune a yanda ta barshi ya na jin ta. Cinkin kuka tace “Wallahi Ya Aslam kar ma ku bari In had’u da Yarinyar nan! Bana jin akwai wanda yake jin tsanar d’anuwa kamar yanda nake jin tsanar Huda a raina a yanzu atake naji tsanar ta ta dabaibaye ni. Ko da wasa muka had’u Allah sai na illatata! Tayaya ma za a bar Ya Arshaad ya aureta bayan na tabbatar da Mammy ba zata so ba.” Cikin kukan ta sauk’o ta durk’usa a gaban Aslam sannan ta hau jijjigashi tana cewa “Dan Allah in kowa yak’i fad’a mishi gaskiya Ya Aslam kai ka gaya mishi….in dai yana neman albarkar aure tou kar ya kwaso ta! Mammy ba zata saka ba na sani kuma ya kamata ya fahimci bad luck ce ita.” Surutun Aaima ya isheshi har ga Allah, dan tun d’azu daurewa kawai yake yi, hakan yasa ya bud’e idanunsa da niyyar yi mata magana ya ga ta zabura ta jaa baya a firgice. Cikin tsananin mamaki take kallon yadda kwayar idanunsa suka yi wani irin jaaa lokaci guda. A hankali ya mik’e sannan yace mata “Kiyi hak’uri Aaima, na san dole za kiji zafin rashin Mammy a kusa. Bara inje in d’an huta, anjima kad’an zan dawo mu je dake kiga Mammyn.” Yana gama fad’an haka yayi hanyar fita da sauri ya fice dan so yake yayi nesa da Aaima a yanzu saboda gudun aikata aikin da na sani........... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 49 An gama yi mata gyaran jiki kenan, Arshaad ya zo. Dama tunda ya kira ta yace ‘gashi nan zuwa’, tayi sauri ta tashi akan turaren wutan da take a kai ta fad’a wanka. Tana cikin d’aura d’ankwalinta ta fara jiyo hayaniyar shi da su Sudais! Kasancewar a d’akin k’asa suke yin gyaran jikin. Loose gown ce a jikinta kalar kwanduwar kwai mai haske, dan haka kawai ta d’an d’aura d’ankwalin ta zagayo da edges d’in ta bayan k’eyarta ta sake su suka zubo akan k’irjinta wanda hakan yayi kamar mayafi saboda d’ankwalin yana da d’an girma. Waya ya fara mata dan haka tayi sauri ta fita, ta bar Sakina wadda ake k’arasa mata nata yanzu. Bai ga fitowarta ba, dan haka ya sake d’aga wayar yayi dialing numberta ya kara a kunnenshi… Har ga Allah baya iya b’oye zalamarshi when it comes to Hudan! Y’ar tafiyar nan da yayi ya sanya ya sake fahimtar tsananin mugun k’aunarta da yake yi! Duk da cewa suna waya amman ji yake kamar yayi irin shekarar nan bai ganta ba! Ko dan tak’i yarda su yi video call ne may be shiyasa, he wonders why tak’i yarda suyi video call d’in Sakina dai tace mishi gyara ake mata kuma in ya ganta idan ya zo ba lalle ya biya kud’in gyaran da kyau ba, ba yadda bai yi dasu ba amman fur itama Huda tak’i yadda ta bashi had’in kai ya gantan… Yana cikin wannan tunanin ya fara jiyo wani k’amshi mai mugun fitinannen dad’i, a take yaji jikinshi ya mutu! A hankali yake jin k’amshin na sake shigar mishi hanci yana sake karad’e ko ina yana sake kashe mishi jiki.. Sai da ta kusan k’arasowa inda yake tukunna ya samu k’arfin jikin juyawa sakamokon jin takun tafiyarta wanda flat shoe d’in k’afarta ke badawa… Yana juyowa suka had’a ido! Tsayawa kawai yayi ya kasa ci gaba da motsi, kamar wani statue. “Ya Arshaad wayarka” D’in da Sudais (waenda suke tare dashi a parlourn, d’an gefe kad’an da shi) yace masa ne ya d’an dawo dashi daga duniyar da ya lula. A hankali ya rik’o wayar wadda ta kusan zamewa daga hannunshi kafin ya iya cewa “Lafiya, ya gida?” Still yana kallonta. Hudan ita kuwa kunyar kallon take ji, dan haka ta fara kame kame ta kasa cewa komai bayan gaisuwar da tayi masa. Sun yi kusan minti biyu a haka! Ganin bashi da niyyar d’auke idanunsa daga kanta yasa ta sake cewa ”Ya hanya? Ka dawo lafiya?” “Alhamdulillah” Ya ce kawai ya ci gaba da abinda yasa a gaba… Wani irin kallo yake yi mata, tun daga kan y’an yatsun k’afarta har kan d’ankwalinta idan ya dire sai ya sake komawa daga inda ya faro kamar ya samu tv. Ganin abun nashi ba na k’are bane ba yasa tace “Ya Arshaad dan Allah ka daina kallona” Tana rufe fuskarta da tafin hannunta, a shagwab’a. Hakan da tayi kuwa ba k’aramin kyau ya k’ara mata ba. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Sorry na daina. Ina Sakina? Kice tazo ta karb’i tukuici mai tsoka.” Ya fadi hakan a kasalance still bai daina kallon nata ba sai dai yanzu ya fara motsi ba kamar d’azu da ya k’ame ba. Cikin son kawo k’arshen kallon tace “Ana yi mata gyaran jiki, in ta gama zata fito. Ka je kaci abinci yanzu, da kaina na yi maka girkin.” Ta fad’a tana sunkuyar da kanta k’asa. Wani sassanyan murmushi Arshaad yayi, yana mai jinsa a sama! Farin cikin da yake ciki yau anya zai iya misaltuwa kuwa? Cikin murmushin yace “Anya Huda ranar da aka ce an d’aura mana aure ba zan mutu dan dad’i ba kuwa?”. Da sauri ta d’ago ta kalleshi, sai kuma ta tura baki ta kauda kai ta d’an b’ata rai. Dariya yayi this time around kafin yace “Sorry tou, ba zan suma dan dad’i ba kuwa? Just looking at you fa da kuma jin wai kin yi min girki da waennan kyawawan hannayen naki! Wallahi ji nake kamar in yi ihu dan murna, Ina kuma ga in akace kin zama mallakina gaba d’aya?” Dariya ta d’anyi tana me sunkuyar da kanta k’asa, kafin tace “To muje kaci kar ya huce”. Ya lura ta gaji da kallon shiyasa take ta so su bar wajen ta samu su daina facing d’in juna, dan haka yayi murmushi kawai kafin yace “Mu je tou” A ranshi ya raya ‘I can’t help it, ni kaina inaso In d’an janye idon but na kasa.’ Ita tayi serving nashi bayan sun isa dining d’in, kamar yanda yayi zato kuwa, tana gamawa ta nemi kujera ta hud’un wadda yake kai a side d’inshi ta zauna. Dariya ta bashi dan haka sai da ya d’anyi dariyarshi tukun ya mik’e yaje inda take yace “Tashi ki ga” Rau rau tayi da ido za tayi magana yace “Shiiii, taso” A hankali ta mik’e ta bishi. Sai da ya zagaya d’ayan side d’in tukunna ya zaunar da ita a kujerar da take setin tashi Kamar za tayi kuka tace “Ya Arshaad to kar ka kalleni” Dariya yayi yace “Tou” kawai, ya zagaya ya zauna ya fara cin abincin shi yana santi yana kallon nata da bata so. Ko plate d’in abincin baya kalla, kawai spoon yake sakawa ya d’ebo ya kai baki, dad’i har kwanyarshi. Suna a haka Sakina ta fito, jin an bud’e k’ofa kuma an nufo dining d’in ne ya sanya ya d’an juya. Murmushi yayi kafin yace “Ta hannun dama! Kina da babbar kyauta yau.” Cikin dariya Sakina ta k’araso suka gaisa tayi mishi sannu da zuwa. Fitowar Abba wanda zai fita ne yasa tace musu “tana zuwa” tabi bayan Abban wanda ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96