Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 65

Chapter 65

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wani had’add’en fari k’al d’in yadi d’inkin boda, yayi matuk’ar karb’ar jikinshi, ya murza sky blue d’in hula zanna bukar sai kyalli take yi, sawunshi sanye cikin farin takalmi sau ciki mai mugun kyau, sai silver agogo da ya d’aura a tsintsiyar hannunshi. K’amshin turarenshi ne ya sanar da Aslam fitowarshi! Dan haka ya bud’e idanuwanshi da suka yi jaa ya zuba mishi. Suna had’a ido Arshaad ya d’auke kai ya tamke fuska yayi hanyar fita. Murmushi Aslam d’in yayi kafin yace “Irin wannan tamke fuska haka! So kake idan kaje ka firgitata?” Banza Arshaad yayi da shi ya ci gaba da tafiyar shi. “You promised Aaima akan za kuyi magana kuma zaka kaita wajen Mammy, remember?” Arshaad ya sake jin muryar Aslam d’in. Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e, bayan ya tsaya cak! Ba tare da ya juyo ba dan har ya kai k’ofa. Yafi 1 minute a hakan, kafin chaan! Ya juyo ya fara takawa zuwa inda Aslam d’in yake zaune. A kan 3 seater yake zaune dan haka shima ya zauna a kai a gefen shi kad’an, cikin nutsuwa yace “Are you ready to talk?” Murmushi Aslam d’in yayi kafin yace “About?” Cikin d’an b’acin rai Arshaad yace “Ok!! Shikenan, kaga tafiya ta.” Ya fad’a yana mik’ewa tsaye. A hankali Aslam yace “Ka san dai akwai abubuwa da yawa a kaina ko? How kake tunanin zan fahimci wanne kake nufi?” Iska Arshaad ya furzar kafin ya komo ya zauna sannan cikin kulawa yace “Akan abunda yake damun ka kwana biyun nan nake so muyi magana! Ka chanja Aslam, Abba ma sai da ya kira ya tambayeni ko akwai abunda na sani yana damunka, dan ya tambayeka kace mishi ba komai!. Na tambayeka tun a waya kace ba komai, yanzu gani nan face to face so talk! Ka gaya min ko menene idan na addua ne in tayaka idan kuma na taimakone in taimaka maka I hate to see you like this! Dan Allah ka gaya mini ko menene i promise to help.” Murmushi Aslam yayi kafin yace “Ba komai fa Arshaad. Kawai matsalan Mommy ne daga shi ba komai. Ko kuna ganin halin da muke ciki ni da ita for years bai kai ya maidani haka ba?” Ya k’arashe maganar yana kafeshi da kyawawan idanuwanshi da har yanzu basu gama dawowa dai dai ba. Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e dan ya fahimci Aslam bai shirya fad’a mishi matsalarshi ba tunda yayi haka kuma ya san ko ya tilasta ba sani zai yi ba….. Yana cikin wannan tunanin Aaima ta sauk’o, ta shirya tsaf cikin abaya blue black tayi rolling, tayi masifar yin kyau. A hankali ta k’araso inda suke tace “Ya Arshaad muje” Tana gama fad’in haka ta juya zata wuce Aslam ya rik’o hannunta. Sai da ta turo baki tukun ta juyo ta kalleshi. Bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba ganin ya kama kunnenshi d’aya da hannu d’aya yayi kalar tausayi. Zare hannun nata tayi da ke a cikin nashi kafin ta zauna tukunna tace “Allah ya Aslam gani nayi gaba d’aya kamar haushina kake ji, tunda fa ka d’auko ni kake ta wani hantara ta, kamar irin ka tsaneni d’innan. Ni Ina chan a skul ba ni da labarin da ya wuce naku amman na dawo duk baku ma yi murna da ganina ba.” Murmushi kawai Aslam d’in yayi kafin yace “Sorry Auta. Mun yi murna sosai. We good?” Murmushi ta d’anyi itama sannan ta d’aga mishi kai alamar ‘eh’. D’an guntun smiling Arshaad yayi tukun yace “Aaima mun samu newest member a family d’innan! Daughter d’in Abba. Na san kin san labarin Anty Maryam ko? To tanada y’a Hudan!” Cikin murmushi ya k’ara da cewa “Hudan dai da kika sani” Cikin zaro ido Aaima tace “Ma shaa Allah! Haba no wonder! Dama ba nayi ta ce maka tana kama da Abba da Ya Aslam ba kwanaki kace min a’a idonane kawai.” Ta fad’a haka da tsantsar farin ciki kwance akan kyakkyawar fuskarta. Kafin ta tashi ta fara juyi da d’n tsalle tana cewa “Alhamdulillah nima nayi y’ar uwa! Yanzu Gramma sai ta daina yi min tsiya ta daina cemin k’anwar maza yayar maza.. Tana Ina (Hudan)?” Sai kuma ta d’anyi jim! Tayi shiru daga baya ta zauna tukunna tace “Mai yasa Abba bai fad’a ba? Tun farko?” Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e kafin yace “Anan za kiji dalilin da yasa baki ga Mammy a gidan nan ba!” ….Tiryan tiryan haka ya zayyano mata abunda ya faru tun daga farko har k’arshe!… Sharkaf haka fuskar Aaima ta jik’e da hawaye kafin ya k’arasa bata labarin. Yana yin shiru tace “Mammy tana cell? Yaya ka san inane cell kuwa?. Ina Hudan take? Ashe shiyasa na daina ganinta a wasapp rannan har kiran ta nayi tak’i d’auka, munafuka!!!” Cikin b’acin rai Arshaad yace “Watch your words, Aaima! Ni na hanata ta fad’a miki komai, ita kuma tace ba zata iya chattn dake ba tana yi miki b’oye b’oye, shiyasa na d’auki wayoyinsu ita da Sakina nayi blocking d’inki ba tare da su kansu sun sani ba! Na fi so sai mun had’u ido da ido tukunna in yi miki bayanin komai da kaina saboda na san haka ce zata faru! Ku mata k’aramar kwakwalwa gareku ba zaki duba circumstances da situations ba kawai wanda yake naki shi za kiyi sopporting! Yanzu ki nutsu tukun mu yi magana…” Mik’ewa Aaima tayi taje gabanshi ta tsaya idanuwanta na tsiyayar da ruwan hawaye ba k’akk’autawa wani nabin wani tace “Kenan kai supporting Hudan kake ko Yaya? Over Mammy, Yaya Mammy fa!!!” Ta k’arashe maganar cikin tsawa. Mikewa shima Arshaad yayi cikin fad’a yace “Bana sopporting kowa! In fact case d’innan ba a hannuna yake ba kuma ba a hannun Abba ko ita Hudan yake ba! A hannun Granpa yake dan haka in kinga zaki iya kina iya zuwa kiyi mishi wannan haukar..” Yana gama fad’an hakan ya juya ya fice fuuuu kamar zai tashi sama. A hankali ta durk’ushe a wajen ta na wani irin kuka mai chin rai. A hankali Aslam ya mik’e ya k’arasa inda take ya d’ago ta ya zaunar a kan kujera kafin shima ya zauna, ya fara lallashinta… Cikin kuka tace , “Ya aslam Hudan is bad news! Kaga fa daga zuwanta gidannan abunda ya faru.. Na tsaneta wallahi” “Shhhhh” Aslam yace, yana sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “She’s his fiance, dole in kin fara jin haushinta tun yanzu zai yi fushi dake And Aaima zai fi miki sauk’i idan kika rungumi Hudan kuka zauna lafiya dan she’s family kuma gashi za ta sake zama family.” Cikin rashin fahimta tace “Noo Ya Aslam, kalla fa ka gani bata riga ta zama fiancé d’intasa ba amma ji yanda yake yi a kanta, what if ta zama?”. Murmushi yayi kafin yace “Saura sati uku bikin.” Da sauri Aaima ta kalle shi sai kuma ta fashe da kuka tana cewa “Kaga irin abunda rashin Mammy a kusa kan jawo ko? Ni Ina ma na san da wani engagement balle maganar aure! Kana gani fa Ya Aslam muna waya muna chattn kusan kullum amman no one even bothers to tell me…da ga zuwan Yarinya ta hargitsa gida yanzu tana shirin hargitsa zumunci sannan a haka kace ba

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});