Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a cikin nata ne ya sa ta had’iye ragowar maganganun data d’ebo! Cikin b’acin rai yace “Ummi! ban tab’a ganin selfish being irin ki ba!. And FYI ba saboda son da kike yi mini bane ya sa kika aikata waennan abubuwan wake up!! Saboda tsananin son da kike yiwa kanki ne ya saki aikata hakan! Kinga dai Ina son Maryam fiye da raina ko?? Amman wallahi inda ace tun farko ta nunamin bata sona kuma akwai wanda take tsananin so, kamar yadda na nuna miki, tou da tabbas zan iya hak’ura da ita, saboda farincikin ta!! That is love, ba wannan shirmen naki ba.” Yana gama fad’in haka ya warce k’asan rigarshi da ta kamo ya wuce ya bud’e k’ofar ya fice a d’akin ya barta nan durk’ushe tana kuka tana kiran sunanshi….. Mom tana zaune a falon da k’unshinta, taga sauk’k’owar Abba… Da k’arfi k’irjinta ya buga! Yadda taga ya sauk’o ya wuce fuuu ranshi a mugun b’ace ko adawo lafiyanta bai amsa ba. Gaba d’aya sai ta kasa nutsuwa… kusan minti biyar ta bayar amman shiru ba Ummi ba labarin ta, dan haka ta yanke shawarar cire lallen! Ko bi takan mai k’unshi da take ta ce mata “bai kamaba” Bata yi ba ta bata kud’inta ta kira mai aiki tace “ta tattare wajen”dan gaba d’aya k’irjinta bugawa yake yi ta rasa dalili. Kaf falon sama da d’akunan ta duba bata nan, har d’ayan side d’in ta sauko ta hau ta sake dubawa nan ma bata nan. Tunawa da tayi Abba yace ta kai mishi abinci bedroom d’inshi ne, yasa da sauri ta nufi stairs d’in da zai kaita side d’in nasa. Tun kafin ta k’arasa d’akin ta fara jiyo sheshshek’ar kuka..dan haka ko sallama bata yi ba ta k’arasa ciki da mugun sauri. A yadda Abba ya fita ya barta a haka ta tarar da ita, da sauri ta k’arasa ta d’ago ta kafin a rikice ta hau tambayarta “mai ya faru?” Kukanta ne ya k’aru, wanda hakan ya sake rikita Mom! Ta d’ago hannu kenan zata tab’ata taga shatin yatsu kwance akan farar fuskarta.. Cikin gigita ta cigaba ta tambayarta tana faman jijjigata Da kyar Ummi wada tun shigowar Mom kukanta ya tsananta ta iya sassauta kukan nata da kyar ta hau gayawa Mom dukkanin abunda ya faru, tana sheshshek’a…. Tunda ta fara magana Mom tayi mutuwar tsaye! Har ta kai aya ta d’ago tana kallonta amma ko gezau bata yi ba. Sai da Ummin ta d’an tab’ata tukunna ta juyo da hankalinta gareta kafin cikin b’acin rai ta fara magana “Ban tab’a ganin dak’ik’iya Irin ki ba! A tunanina rashin wayon ki bai kai haka ba! Amman yau kam na gasgata ya kai har ma ya wuce zatona. In banda rashin hankali, ba duka ba ko kanki Abba zai saka a gabas da wak’a a hannunshi, ya kamata ki fad’a mishi wannan maganganun da muka yi alk’awarin rufawa juna asiri akai har abada??? Barazana ce fa yayi miki!! Tayay ma za kiyi tunanin Abba zai iya yi miki illa?? Na tabbatar ko suman k’arya kika yi tuni zai dawo dai dai hankalinshi kuma ya tashi!! Amman da yake ke d’in dabba ce!! Shine kika tonawa kanki asiri da mu da muka taimakeki, gaba d’aya!! Yanzu ya kike so muy.....”. Cikin katseta Ummi, tace “Adama wallahi ke kike ganin kamar barazana ce amman ba haka baneba, da gaske na hango tashin hankalin da ban tab’a gani ba a cikin kwayar idanunsa, kuma na tabbatar zai iya aikata dukkanin abunda ya fad’a din. Ba abinda yafi d’aga mini hankali irin kalmar ‘saki’ da ya ambata! Shiyasa kika ga nayi haka, kin sanni zan iya yin komai domin inga na kare aurena! Kuma baya ga haka a tunanina idan na fad’a mishi gaskiya to zai yarda da ni kuma ya fara trusting d’ina daganan ya so ni! Shi da bakinshi yace ‘In na fad’a mishi gaskiya komai zai wuce, in kuma ban fad’a ba har saki sai ya had’a mini dashi km....” Marin da Mom ta d’auketa da shi ne ya katse mata ragowan maganartata… Cike da mamaki ta d’ago tana kallon Mom….za ta yi magana Mom d’in tayi saurin d’aga mata hannu sannan tace “Lalle Ummi, wato kin yi komai saboda kare aurenki da jawo hankalin mijinki gareki ko? Mu kuma fa? Da kika zubar mana da k’ima, kika sakamu a matsala? Ke a ganinki kin yi mana adalci kenan?. Ko dan kinga ke baki da wani ishashshen laifi a cikin lamarin shiyasa? To bari kiji in gaya miki kinga wannan abunda kika yi?” Bata jira jin amsartaba tace “ba zai jawo yarda tsakaninki ke da Abba ba ballantana a tafi kan maganar so, in banda bak’in jini da tsana ba abunda rashin tunaninki ya jawo miki!!!. Kuma inaso ki sani, ni da sake shiga harkarki har gaban abada!! Saboda na lura kowa kanshi ya sani dan haka kowa yayi ta kansa.” Tana gama fad’an haka ta juya tayi hanyar fita, sai kuma ta sake juyowa kana tace mata “In zan baki shawara ki d’auka, gara ki hak’ura, saboda inda ace Abba zai so ki to da tuni an wuce wajen!! Amman har yanzu shiru.. Ga kuma sababbin obstacles a gabanki Kin tonawa kanki asiri kuma ga Maryam ta dawo rayuwar shi sannan ga y’arsa da mukeda tabbacin ita zata had’a su!! So kawai gara….” K’arar jiniyar y’an sandan da ta jiyo ne ya sakata yin shiru!! Take gabanta ya yanke ya fad’i, kallon Ummi take yi wadda itama jin jiniyar y’an sanda ya sakata sake rud’ewa! Cikin karkarwar jiki tace “Kamar jiniyar y’an sanda nake ji.” Tun kafin ta rufe bakinta, Mom tace “Ba ‘kamar’ baneba tabbas jini y’ar y’an sanda ne. Tuni ilahirin jikin Ummi ya sake rikicewa da karkarwa, ga uban gumi sai sake keto mata yake yi ta ko wacce k’ofar gashin jikinta, kana ganin ta ka san bata da gaskiya, fuskarta tayi jajir. Da sauri ta k’araso kusa da Mom kafin tace “Adama me kenan hakan yake nufi? Kina tunanin Abb....” “Tabbas Zainab mijinki ya cika tantirin d’an iska kuma mara mutunci! Da y’an sanda zai had’a mu kenan ko me??” Cewar Mom. Ummi bata san lokacin da ta fashe da wani irin mahaukacin kuka ba! Tsoronta d’aya a yanzu kar Granpa yaji zancen nan. “Innalillahi wa innailaihirraji un” Ta shiga maimaitawa, sannan ta fara kallon d’akin tana neman hanyar guduwa, da sauri ta juya ta nufi k’ofar closet, da mugun gudu. Daidai nan Abba ya shigo da y’an sanda mata guda biyu! Mom ya nuna musu yace “suyi arresting d’inta” A take kuwa suka yo kanta.. Babu abinda yafi d’agawa Mom hankali kamar ankwar da suka saka mata, bata san lokacin da idanunta suka kawo ruwa ba. Waige waige Abba ya hau yi…Chan ya hango k’ofar closet a d’an bud’e kad’an hakan yasa ya isa wajen gadan gadan ya bud’e k’ofar ya shiga, ya fara dube dube! Idanuwanshine suka sauk’a a ,wajen jallabiyoyin da aka rar rataye…gani yai wajen yana d’an motsi, hakan yasa ya k’urawa wajen ido, cikin sa’a kuwa ya hango k’afafun Ummi da suka sha jan lalle ta chan k’asa Ai kuwa ya janyo gaba d’aya kayan wajen da sun kusan 30 ya zubar dasu a k’asa! Tarr!!

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});