Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 50

Chapter 50

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,192 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ki yarda da shi wannan matsalarku ce!! Ba wai dama na fad’a miki dan wani abun bane, that very day kin shigone a time d’in da case d’in yake goin that’s why har kika san maganar! Anyways Jalila it’s up to you, sai ki san abun yi… Tunda gashi yanzu ya nace akan ba nashi bane! I think su Granpa ne kawai zasu iya kwatar miki hakkinki dan ni kam daga yau na cire hannuna a case d’innan naku, in shaa Allah.” Ya k’arashe maganar yana mai bud’e hannayenshi biyu ya kai bayan k’eyarsa ya sak’ale sannan yayi resting gaba d’ayansa akan kujerar ya d’aura k’afa d’aya kan d’aya. Wani tuk’uk’i ne ya turnuk’e Sakina, bata san lokacin da ta fara magana ba! Kamar yadda ya yiwa Huda itama hakan tayi mishi Hey! You look here, Auwal kake ko wa? Waye ne ya gayyatoka nan? Wa ya kira ka? Waye ya kasa da kai? Wa yace maka ana son jin opinion d’in ka a cikin maganar nan? Hakanan kawai ka kama ka shigo tsulum! Ka tarar da mutane ko sallama baka yi ba ka hau magana kamar wani kwarkwar!. And let me tell you something abunda kayi yanzun, ya tabbatar da you got something to do with her and the baby! Kuma da kake wani cewa ‘zaka kai magana sama’ Ai da kai! Da mu! Da ita munafukar taka duk munsan gaskiya dan haka ina mai shawartarka da ka tabbatar ka d’auko fad’an da ka san zaka iya k’arasawa, in ta kwab’e!! Ke kuma!” Ta juyo kan Jalila, sannan tace “ki karb’a ki rantse a gaban kowa, sannan ki yi Allah ya isa a duk wanda ya cutar dake haka, a tsakanin Ya Arshaad da wannan Auwal d’in. Hudan Dan Allah ki bawa ya Arshaad, yau zan ga k’aryar iskanci.” Tunda Sakina ta fara magana Auwal yake kallonta ya kasa d’auke ido, k’arshe ma murmushi ya fara yana jin inama kar ta daina. Muryar Jalila ce ta katseshi jin tana cewa “Tou uwata! Ke har kin isa ki gaya min abunda zan yi?” Da sauri Arshaad ya juyo yace “in baki da alwala kije kiyi kizo yanzu” Yayi maganar babu alamun wasa a tattare da shi. Gaba d’aya jikin Jalila ya jik’e da gumi, tun lokacin da aka fara maganar, tsabar tsoro! “Ko bakya ji ne?” Arshaad ya fad’a cikin b’acin rai dan takaicin Yarinyar yake ji ba kad’an ba, ji yake yi kamar yaje yayi ball da ita. Auwal ta d’ago ta kalla, taga yayi mata wani kallon data fassarashi da warning!! Ganin kowa ita yake kallo yasa ta cire mayafinta ta ajjiye ta wuce tana cewa “ina ne toilet?” Wata k’ofa kurkusa Arshaad ya nuna mata yace “ta shiga”. Tana shiga ta turo k’ofar ta jingina tana haki, kamar wadda tayi y’ar tsere! Tunda take bata tab’a shiga tashin hankali irin na yau ba…ko hauka take yi ba zata tab’a dafa Qur’ani akan k’arya ba, akan gaskiyar ka ma ba a cika son kana dafawa ba, balle k’arya! Da albarkar ka ma ya ka k’are ballantana babu! Kuma ita a halin yanzu tana buk’atar albarkarta fiye da ko yaushe, da kusanci da Ubangijin ta! Tana so ta rok’esa arzik’i da soyayyar Arshaad dan muddin taci gaba da ganin Huda a cikin wannan daular alhalin ita bata da shi, to wallahi ta san zuciyarta sai tayi ajalinta…. Ta dad’e a cikin band’akin sosai, har sai da Sakina taje tayi mata knocking tukunna ta bud’e, tana bud’ewa ta zabga mata harara kafin tace “Banza y’ar karere kawai, sarkin zak’ewa!” Dariya Sakina tayi kafin tace “Ai gara ni y’ar karere ce Kuma kirana aka yi takanas! Nazo ba abun kunya ne ya zaunar dani a gidan ba.” Jalila bata ita take ba, dan haka tayi shiru kawai ta fito suka k’arasa parlourn tana tunanin next stage! Gabanta in banda fad’uwa ba abunda yake yi.. Ana tsayawa Sakina ta amshi Al Qur’ani n ta ajjiye akan centre inda yake tun farko, kafin ta kamo hannun Jalila ta kaita wajen tace “Bismillah!” Fusge hannunta Jalila tayi tana hararar ta Kallonta Sakina take sosai da mamaki akan fuskarta kafin tace “Da alama dai taimama kika yi ko? Dan banji alamun danshin ruwa a hannunki ba, ga d’aurin vail d’inki shima rad’au!! Powder ki kuwa kamar ma k’arawa kikayi.” ….Gaskiya In Sakina bata daina shiga huruminta ba wallahi zata illatata a wajen nan!! Wanne irin iskancine wannan??… Jalilan ta aiyyana hakan a ranta. Muryar Hudan taji tana cewa “Ya Jalila idan kin san baki yi alwala ba karki tab’a Qur’anin nan fa, Dan Allah.” Takaici kamar ta shak’eta haka Jalila taji, a ranta tace “Y’ar ‘Yaa Jalilan’ uwa!”. Muryar Arshaad taji yace “Ba kiyi alwalar ba?” Cikin rawar murya tace “Eeh bbb ban dd’akin babu ruwa” Da sauri Hudan tace “Zo muje d’akina, kiyi a chan” Sakina ta yunk’uro za tayi magana taji Arshaad yace “Muje in kunna miki famfon, yana da wuyar sha’ani dama.” Ya fad’i haka yana wucewa gaba. Jikinta har karkarwa yake yi haka ta wuce, ta bishi…. Suna shiga ya kunna mata shower ya kunna famfon sink, da wani famfo a gefe ya nuna mata yanda zata matsa abun tsarkin jikin toilet sannan ya fito ya bata waje ya bar ruwan yanata zuba bai kashe ko d’aya ba. Alwalar tayi ba yadda ta iya, ta kashe famfunan, ta tsaya tana kallon fuskarta a mudubi. Jin yayi knocking yasa gabanta mugun fad’uwa! Ita kam yau ta ga talatar kanta, gashi ba daman tace tana fashin sallah! Da kyar ta iya daurewa ta fice, k’irjinta na dukan uku uku. Suna k’arasowa, Sakina ta mik’a mata vail d’in da ta cire a jikinta d’azu ta ajjiye tace “Bismillah” Fisgewa tayi tana hararar ta. Murmushi Sakina tayi kafin tace “Yarinya yau ko idanunki zasu fad’o k’asa sai kin rantse!”…. ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 08138873799 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** ……A nan fa ake yinta, ga Jalila ga Al Qur’ani a gabanta ga jama’a kowa ya zuba mata ido… Parlourn yayi shiruuuu. Ba abunda yafi bawa Arshaad mamaki irin yanda Auwal ya d’auke wuta diff!!! Don gaba d’aya kamar babu shi a wajen.. Shi kam Auwal yana chaan ya sha’afa da kallon Sakina kamar ya samu tv, sam! Bai damu da kalar harar da take zabga masa a duk sanda suka hada ido ba! Babu abunda yafi tafiya da imaninshi kamar idanuwanta waenda idan ta kalleshi dasu yake ji gaba d’aya kamar an zare mishi lakka bayan fad’uwar gaban da yake tsintar kanshi a ciki..duk wata hayaniyar shi yau ya ji babu ita, yanaso yasa baki a lamarin su Jalilan amman ya kasa,

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});