Chapter 34
Chapter 34
Auwal kamar yayi hauka, gashi an gama kwashe kaya ya san shi kawai Daddy yake jira ya kai Jalila sannan yazo su tafi, ga kuma batun ta na zata tona mishi asiri, kar fa Yarinyar nan ta jik’a mishi aiki!! A daa yana underestimating d’inta yanzu kam ta fara bashi tsoro gaskiya, he has to do something, duk da cewa Mom tace mishi ‘ya jira ta tana dawowa zata yi maganinta’ amman gaskiya he cant wait!! Yana tsoro kar kwab’arsa tayi ruwa, gara kawai ya k’are komai dan shi gani yake ma it’s like sun rabu da Arshaad d’in tunda ta sameshi dan haka tayaya zai iya breaking d’inshi!!! Takaici ya taru ya yiwa Auwal yawa, ga Jalila sai maganganu take yab’a masa… Da kyar ya iya controlling kanshi dan ji yake yi kamar yaje ya rufeta da duka ko ya samu sauk’i! A hankali very calm ya k’arasa inda take ya kamo hannunta Da sauri ta fisge hannun kafin tace “Ai wallahi anyi an gama babu k’ari!! Mayaudari kawai, haka kurum ka cuceni! Ga wasu zantukanka waenda har yau na kasa fahimtar alk’iblarka a kaina..” Cikin tsananin fushin da ya kasa dannewa yace “na cuceki ko kin cuce ni?? Ke kin San ko waye ni kuwa? Wallahi ba dan abunda na shirya akan ki ba ko a y’ar aiki ba zan tab’a yarda ki zo mini ba! Kina magana kamar irin dole d’innan nayi miki, Ina ce da yardarki kika bini har gidan? Zaki wani rainawa mutane hankali, wallahi ki bini a hankali tun ban fito miki a asalin Auwal d’ina ba!! Magana kad’an In anyi kice wani ‘za kije ki tona min asiri’ To bari kiji, tsaf! Zan iya cewa Daddy na maidake gida! In kulle ki anan yunwa ta kasheki daga baya in zo in fitar da gawar ki babu wanda zai ji labari, tunda itama uwarki kwad’ayi ya rufe mata ido ai bata cewa kowa kina nan ba! Stupid useless girl kawai! Banza wadda bata da daraja kwata kwata, Akuya ma ta fiki daraja tunda ita wani lokacin tana guduwa tana jan aji, ke kuwa ana ce miki kule za ki ce cass!.” Takaici da tsoro ne suka sanya Jalila fashewa da kuka, wani irin takaicin Umma take ji yana taso mata.. Shiyasa fa ita tayi ta dodging, har ga Allah irin rayuwar nan da yadda ta yarda dashi nan da nan ba hakan ta tsarawa kanta ba! Ita dai ta san tanada burin son auren mai kud’i, amma kalli yanzu yadda ta koma, duk ata dalilin biyewa son zuciyar Umma, gashi ta hanata zubar da cikin, kamar ba ita ta tsugunna ta haifeta ba! Tunda take ba a tab’a yi mata zagin daya girgiza taji haushinshi ba kamar kalar zagin da Auwal yake yi mata especially na yau dan ko ranar daya maidata gida bata ji ciwon zagin kamar na yau ba, kuma gaskiya ya fad’a!. Gashi yanda taga ya birkice tabbas zai iya aikata abunda ya fad’a d’in… Kuka take yi bil hakk’i da gaskiya. A take ta gama tsarawa kanta zata ce a zubar da cikin kawai ta koma wajen Umma, kowa ya huta. Ganin yadda tayi ladab ne ya k’ara bawa bawa Auwal kwarin guiwar aiwatar da abunda kwakwalwarshi ta shirya mishi yanzun nan, dan haka ya k’arasa inda take tsugunne shima ya tsugunna, fuskarshi ba alamun wasa yace “Look Jalila, let’s just get this done over with… Zan baki 5 million” Da sauri ta d’ago manyan idanuwanta tana kallonshi. D’aga kanshi yayi alamun ‘yes’ sannan yace “Miliyan biyar!” All I want you to do is ‘Kice cikinnan na Arshaad ne, kuma in sama da k’asa zasu had’e kar ki chanja maganan ki, ko a gaban waye, ke hatta uwar data haifeki inaso ki birkice mata kice na Arshaad ne kawai!’ Gaskiyar Maganar ya tsaya daga ni sai ke. Kar ki damu In komai yazo gangara ni zan san yadda zan yi, komai zai fita normal, ba zaki samu wata matsala ba, understood???”. Rarraba ido ta fara yi tana k’ok’arin yin magana, suka jiyo sallamar Arshaad. D’agowa sukayi dukkansu suna kallon hanyar shigowa. Cikin takunshi ya k’araso cikin parlour… Wani killer smile Auwal yayi kafin ya mik’e tsaye yace “D’an halak! Maganar ka muke yi” Cikin nutsuwa Arshaad d’in ya k’araso inda suke, kallon Jalila yayi yaga yanda take kuka, a ranshi yana mamakin ina Auwal ya samota haka, gashi sai kuka take yi… Ganin ba wannan ne ya kawo shi ba yasa ya d’auke idonshi a kanta ya maida kan Auwal d’in sannan yace “Daddy is waiting, infact everyone, for you, kayi sauri dan yace karka bari yazo ya sameka a nan!” Yana gama fad’in haka ya juya ya fara k’ok’arin fita. Da mamaki Auwal yake kallonshi da Jalilan wadda tunda Arshaad d’in ya fara magana take kallonshi, Ganin arshaad d’in na shirin fita ba tare da ya ma sake kallon Jalilan ba yasa Auwal yin ta maza ya zagaya ya tsaya a gaban shi sannan yace “Saurin me kake yi? I’m just trying to clean up your mess here fa, amman kayi kamar ma baka santa ba, ko In barta ta tafi wajen su Abba ne?” D’an dakatawa Arshaad yayi sai kuma ya juya yana kallon Jalilan.. Da ido Auwal yayi mata signal d’in da ta kasa ganewa, ita dai kawai sai ta mik’e, kamar an tsoma ta a ruwa jikinta na d’an rawa. Murmushi Auwal d’in yayi sannan ya zagayo yace “Talk mana Jalila, ko tsoronshi kike ji yau kuma?” Kame kame Jalila ta fara yi, ta rasa ta Ina zata fara dan Bata san me zata ce ba, gashi duk da halin da take ciki tunda taji Auwal ya ambaci miliyan biyar ta rikice, hali zanen dutse!. Don haka tace “Daman nazo ne akan maganar mu” Tayi maganar jikina na d’an karkarwa dan har yanxu k’irjinta bugawa yake yi… yau ce rana ta farko data tsaya ta k’arewa Arshaad kallo!! Ita dai tun lokacin da yake zuwa wajen Hudan ta san yana burgeta kuma yanayin shi, maganarsa, tsayi da k’amshin turarenshi suna mugun k’ara kid’imata! Kawai dai ita ta san tana so Arshaad har cikin zuciyarta, amman yau data tsaya ta k’are mishi kallo ta sake rikicewa kuma ta tabbatar idan har bata sameshiba to ko dai ta mutu ko kuma ta shiga hauka… K’irjinta in banda bugawa babu abinda yake yi, gashi ya tsareta da dogayen shanyayyun idanuwanshi, cikin tsare gida yace “Wacce magana kenan?? Do i know you?” Wata dariya Auwal ya saka kafin ya k’araso yana cewa “Okayy!! Bari in yi maka dalla dalla.. Maganar cikinka wanda ke a jikinta! Shi ta biyo ka ku k’arasa.” Arshaad zuwa yanzu yazo wuya! Don haka ya yanke shawarar cin uban Auwal dan ya lura bayan rainin hankalin da yake yi mishi, harda hauka ma ya fara damunshi kwana biyu, gara a yita ta k’are ko zai dawo hankalin shi, in hauka ya za ayi ya d’auko Yarinyar da bai tab’a ganiba a rayuwarshi ya hau yi mishi wani maganan banza da wofi??! A fusace ya juyo yana shirin yin kan Auwal, sukaji k’arar fad’uwar abu, da sauri duk suka juya suna kallon k’ofa.. Arshaad, ya san yana da gaskiya amman kalar kallon tuhumar da Hudan take yi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96