Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 63

Chapter 63

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kuka! Bata iya ci gaba da tsayuwa a wajen ba kawai tayi hanyar sama ta kyalesu, ganin haka yasa Baaba Talatu ta bi bayanta. D’akin da aka gyara mata a k’asa mai aikin ta nuna musu dan haka suka nufi d’akin da ita. An gyara d’akin sosai an wanke band’aki, an sa turaren wuta sai tashin k’amshi yake yi. Kuka Mama ta fara yi ana shigar da ita d’akin… Ummi ta san za a rina daman saboda tana tunawa nan ne d’akin Maman a lokacin da take budurwar. Da kyar suka lallasheta tayi shiru, tana tunanin rabonta da d’akin tun ranar da tabi Abba suka gudu! Bayan nan Ko tazo gidan, a tsakar gida ake tarar ta ko alwalla za tayi sai dai ta shiga band’akin tsakar gida, a hakan shima sai in ya zama dole ne kuma in Shuwa taga dama. Ita da Sakina ne suka kamata suka d’aura akan gadon dukda tanata ce musu “zata iya fa”. Favorite food d’inta Shuwa ta sa aka dafa, da mai aikin ta kawo tana bud’ewa suka saki murmushi a tare ita da Ummu. Ummu kalmar “Alhamdulillah” kawai take ta maimaitawa a zuciyarta, ga dukkan alamu Shuwa ta sauk’o! Allah yasa ta yarda ta yafewa Maryam a samu komai ya dawo dai dai kamar daa. Sai dare bayan Ummu ta tafi tukun Shuwa ta shigo. Kwata kwata Maryam ta rasa dalilin da yasa Hajiya Shuwan bata iya had’a ido da ita dan yanzun ma “ya jiki?” tayi mata ta kuma tambayeta “ko akwai abunda take buk’ata” ba tare da ta bari sun had’a ido ba. Da “a’a” ta amsa, dan haka tayi mata “Allah ya k’ara sauk’i” da “sai da safe” ta fice da sauri. Da daddaren ma abincin da Shuwa ta san Maryam d’in tana so tasa aka yi a gidan. A washegarin ranar da aka sallami Maryam aka sako ya Usman! Tunda Baaba Talatu taji labarin za a sake shi yau ta tafi gidanshi ta chake. Suna d’aki ita da Sadiya, suka ji k’arar bud’ewar d’akin shi dan haka suka nufi chan. Baaba Talatu tana ganinshi ta fara kuka haka ita ma Sadiya, sai da su Kaka suka daka musu tsawa tukun suka nutsu. Abinci kawai Baaba Talatu ta bari ya ci, daga nan ta cewa Sadiya “ta d’an basu guri” ko gama fita bata bari Sadiyan ta yi ba ta hau kwararo mishi bayanin halin da ake ciki. Tashin hankalin da ba a saka mishi rana!!! Tsananin tashin hankalin da Baba ya shiga ba zai fad’u ba! Gashi Kaka yace “wallahi ko a k’ofar gidan Madu ya ganshi sai ya tsine mishi!” Madu zai yi magana, Kaka yace masa “Dan Allah yayi shiru, kar yace komai” daga nan ya jaa hannunshi suka fita, suka tafi. Yadda Baba ya hargitse sai da Baaba Talatu ta yi dana sanin fad’a masa… K’arshema kuka ya saka mata, ga tsananin rad’ad’in ciwukan jikinshi ga rad’ad’in zuciya ga tashin hankali!! Kuka wiwi haka ya dinga yi kamar k’aramin Yaro. Shi har ga Allah ya shirya ne akan ….Bayan ya saketa! Ya san zata yi ta Allah Allah ta fita a idda dan ta auri Abba shima kuma Abban haka! Shikuma ana i gobe ko jibi zata fita daga iddar sai ya zo yace ya maida ita! A tunanin shi hakan zai sanya Maryam ta hak’ura gaba d’aya, dan ya san ta tun Yarinta bata son ayi ta ja mata rai akan abu........ BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 48 Da kyar aka samu Baba ya d’an nutsu Tukunna Baaba Talatu ta tafi da alk’awarin gobe da sassafe zata dawo! Washegari, tana zuwa ta tarar da Umma a d’akin tana kuka bata kai ga tambayarta ba Umman ta mik’a mata wata takarda, cikin kuka tace “Yanzu saboda Maryam shine zai tattara kaff ya tafi wajen Ya Jamilu saboda Allah? Ni kuma fa? Ni da y’ay’ana ba damuwarshi bace kenan?. Baaba Talatu rasa bakin magana tayi…..haka suka kasance Sadiya tana kuka ita kuma tayi zurfi a lissafi da tunane tunane ga damuwa kafin da kyar ta shiga bawa Sadiyan hak’uri har ta samu ta d’an nustu. A Washegarin, da safe kafin Ummu ta wuce office ta zo ta dubasu… A d’akin ta tarar da Shuwa itama ta sauk’o duba Maman. Sai da ta tabbatar komai yayi settlling Maman tayi wanka ta ci abinci tukunna ta fara shirin fita dan client d’inta already tana office tana jiranta… Tana mai cewa Huda “akwai bak’uwar da zata yi daga Maiduguri”. Daga haka ta sa kai ta wuce bayan Hudan tace mata “to, Allah ya kaimu.” Tace “Ammen”. K’arfe uku bak’uwar ta iso, mai gyaran jiki. D’aki guda Shuwa tasa aka ware ake gyarata ciki da waje….tun tana nok’ewa har ta sake, Sakina ita ma ba a barta a baya ba, dan duk abinda aka gogama Huda a fatarta itama sai ta goga Kafin sati biyu suka yi wani kyau na ban mamaki, in ka gansu kamar ka sacesu ka gudu. A lokacin bikin Hudan da Arshaad bai kai saura sati uku ba. A lokacin kuma k’afar Mama ta warke ba laifi, kasancewar transverse fracture ta samu shiyasa abun yazo da sauk’i, but still bata gama warkewa ba, so zata ke zuwa follow ups akai akai. Abba baya samun zuwa gidan ganin Mama, sai dai yakan zo ya karb’i ruwan karatu a wajen su Hudan time to time! Wani lokacin kuma yace kawai suyi addu’a daga gidan Arshaad ma daga inda yake , yake yi. Idan Abban yazo Hudan ce ke kai mishi a mota inda yayi parking, yana so ya shiga ya gaida Shuwa yaga jikin Maman amman bai san ta ina zai fara ba! Har yau yana tuno b’acin ran da ya gani a idanun Shuwa ranar daya kawo Maryam Madu kam suna had’uwa su gaisa da shi da Kaka wasu lokutan ma tare suke yin sallar Isha.. Haka nan yanaji yana gani in ya karb’a sak’on zai tafi, ga dai Maryam a kusa amman ba daman ganinta. Yana yawan kiran waya yace Hudan ta bata amma k’iri k’iri zata k’i karb’a, ayi ayi tak’i, k’arshe dai In ya kira sai Sakina ta karb’a ta sa wayar a speaker ta ajjiye akan gado, su fita da sauri… Tun Maman tana yi musu fad’a har ta daina. In suka dawo a inda suka ajjiyar wayar anan suke tarar da ita, Mama tayi ta mata fad’a amman gobe ma sai ta k’ara, in ta cika magana tace “Ai lada take nema, dan ita aure take shirin k’ullawa!” Dan haka kawai Mama sai ta daina fad’an ta daina biyeta, dan ta ga alamun kakarta ma take son mayar da ita, ita kuma bata shirya biyeta akan zancen Abba ba. A Satinsu na biyu ne Abban ya nemi su koma haka, Mama taso yin musu amman Shuwa tasa baki.. Sakina kam ta nace ba zata bi Hudan ba tace “ai yanzu ta saba da kowa” Sai da taga Huda na shirin yi mata kuka tana had’awa da magiya tukunna ta yarda zata bita a ranta tana tuno irin nacin Auwal da bataso! Dan wallahi ita saboda shi ne ma daa d’in tace ba zata bi Hudan ba! Bata san a ina ya samu nunbertaba amman kullum sai ya kirata bata gajiya

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});