Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 25

Chapter 25

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Sakina ta sauk’e jin muryar Huda sannan tace “Alhamdulillah” Jin yanayin muryar Sakina yasa ta fahimci akwai matsala. Cikin sanyin muryar da bata santa da shi ba taji tace “Huda kuna Ina? bakya hawa watsapp, ba kwa amsa waya tun jiya, gamu kuma mun dawo gida bakwa nan. Ina kukaje gaba d’aya hankalin mu ya sake tashi.” Da sauri Huda tace “Sakina Mama bata gida? Ya naji muryar ki wani iri duk ya dishe?” Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e, har zata fad’a mata kuma sai tayi shiru (saboda su Madu sun ce a bari a fara yin test na gawarwakin da ake expecting akwai Junaidun a ciki da jinin Baba, before ayi confirming nashi as dead ) Hakan yasa tace mata “Ban gane ‘Mama bata gida ba’ bakwa tare? Ke kina ina?”. Gefe guda Hudan ta koma kan kujerar dining ta zauna sannan ta fara bawa Sakina labarin tun daga sumewar da Mama tayi jiya da safe, har kawo yanzu da take son gudowa…. To fa!! Ana wata ga wata. Numfashi Sakina ta fesar kafin tace “With all that is goin on Hudan, congratulations! Kin had’u da Mahaifinki finally, and baya gudunki, kamar yadda mutane suke fad’a. But first Maama, so yanzu ki bani kamar 20 minutes haka za sake kira in shaa Allah.” ......Su Abba kafin su koma ciki suka tsaya shi da Daddy suka yanke shawara…suna zuwa suka sanar musu cewa “Shi da Daddy za su bar gidan, Dad da Gramma kuma za su zauna. Addua suka dinga yi akan Allah yasa kowa ya yarda. Ba dan su Gramma sun so ba haka nan suna ji suna gani suka amince da tafiyar su su kad’ai, Dad yaso ace shi ne yabi Abba tunda shine Babba Amman bayan sun keb’e sai suka yi mishi bayani akan kasancewar shi babban ne yasa suka ce ya zauna a estate d’in, sannan ya taimaka ya dedeta Gramma da Granpa, kafin ya koma Abuja, dan tun a wajen meeting d’in suka fahimci iyayen nasu suna fushi da juna wanda hakan it’s not usual. Ahaka ba dan rai yaso ba aka tsara akan gobe zasu bar estate d’in kafin a samu komai ya dedeta In Granpa ya sauk’o su dawo, Dad ne ya basu mukullin makeken mansion d’inshi wanda ke anan bayan su kad’an yace “su zauna su biyu a tare ba sai sun raba gidaje ba.” Dan ana hoping d’in daidaituwar komai soon in shaa Allah. Daddy yayita jiran Granpa ya kirashi yace “yayi resigning, ya kawo takardun companies d’in da yake rik’e dasu sannan ya sauk’a a md d’in MT UK branch Amman ga mamakin shi sai yaji shiru, bai ce masa komai ba......... Sakina tana katse kiran ta mik’e ta isa inda Ummu take ta jaa hannunta suka koma gefe, ganin haka yasa Shuwa itama ta iso inda suke, nan Sakina ta zayyane musu komai. Kafin awa d’aya gaba d’aya su Kaka kowa ya hargitse a neman Mama har da Madu wanda ba kad’an ba kowa yaji dad’in yadda ya shiga cikin lamarin. Babu inda ba a duba ba har wajen 10 amman shiru. Ummu ce ta bada shawarar “aje asibitin malan d’in a sake bincika ta!.” Nan d’inma ba Inda basu duba ba dan rarrabuwa ma suka yi amman shiru… Tunda suka fito Baba yake ta maimaita magana d’aya “Aje gidansu Abba! Shi ya tabbatar idan aka yi kwakkwaran bincike a gidan za a ganta. Ya san tabbas Abba ne ya d’auke Maryam ya b’oyeta bashi da tantama! A kira y’an sanda a kama Abba…waye waye.” Su Ummu tun suna k’ok’arin fahimtar da shi har suka hak’ura suka kyaleshi kawai dan sun lura abun nashi ba na k’are bane. Ganin dare ya lula yasa Ummu tace bara kafin su koma gida ta shiga masallacin can tayi sallar isha dan gaba d’aya ta sha’afa bata yi ba gashi lokaci ya tafi sosai, sai a lokacin Sakina itama ta tuna bata yi ba hakan yasa suka nufi famfo suka yi alwalla tare daga nan suka shiga masallacin domin gabatar da sallah… Babu kowa a ciki sai wasu mata guda biyu a chaan k’uryar masallacin, d’ayar a zaune da Yaro a hannunta d’ayar kuma ta juya baya tana kallon bango alamun bacci ma take yi. Cikin nutsuwa suka gabataar da sallar su suka d’ora da doguwar Adduar Allah ya baiyyana musu Mama. Daga nan suka mik’e suka fara k’ok’arin fita. Ummi ji tayi kawai gabanta ya yanke ya fad’i, kamar kuma ance ta juya…bata san daliliba amman taji tana buk’atar juyawan… Matan nan na d’azu ta sake kallo still suna a yadda suke, har tana shirin juyawa idanunta suka kai kan atamfar jikin matar kwance da mayafinta, sai a yanzu ma ta lura da kayan dan sanda suka shigo kwata kwata hankalinsu baya tare dasu, gasu a gajiye. Kusan a tare zuciyoyinsu suka buga ita da Sakina wadda itama taga atamfa da mayafin jikin Mama Tabbas mayafin Mama ne wannan Atamfar kuma ankon wunin kai amarya Khadijah ne. Da sauri Sakina tace “Maamaa!” Sai kuma ta k’arasa wajen da sauri ta hau tab’ata ganin bata motsi yasa ta sa hannu ta juyo da ita. “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Shine abinda Sakina Ummu da matar dake gefen Mama suka fad’a a tare. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 39 Da sauri Sakina tace “Mamaa” sai kuma ta k’arasa wajen da sauri ta hau tattab’a ta, ganin bata motsi yasa ta sa hannu ta juyo da ita! “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Shine abinda Sakina Ummu da matar dake gefen Mama suka fad’a a tare, dan a yadda Sakina ta juyo da ita haka ta biyo hannun Sakinan ta taho yuuu ta zube wanwar kwanciyar rigingine. Ummu mutuwar tsaye tayi a wajen, so take ta k’arasa inda suke amman ta gagara sakamokon ganin y’ar uwartata da tayi kwance tamkar gawa! Ta kasa tab’uka komai banda hawaye ba abunda take yi. Sakina wadda ta rikice tanata tattab’a Maman ne ta juyo tace “Ummu ki zo ki kamata mu mik’ata emergency.. Mama ce amman bata numfashi.” Jin hakan ba k’aramin sake rikita Ummu yayi ba, ita dai kawai ta ganta a gabansu a tsaye amman bata san ya aka yi ta isa wajen ba. Matar nan ce ta matso itama ta hau jijjiga Mama tana cewa “kumafa yanzun nan muka gama magana da ita, tun jiya muke nan tare da ita. In banda kuka ba abunda take yi, nayi tambayar duniyar nan tak’i kulani… Sai dai kawai taje tayo alwala tazo tayi ta sallah. Sai d’azu ne da naga kamar batta lafiya nace ‘tazo muje in rakata taga Likita’, shine na samu ta d’an kulani ta inda take ce min ‘bara ta d’an yi bacci, idan ta farka sai muje’.” Ita dai Sakina cicib’arta ta fara k’ok’arin yi hakan yasa suma suka sa hannu suka taimaka mata suka yi waje da ita..... Su Madu suna tsaye a k’ofar shiga emergency.. Kana ganinsu ka san hankalinsu ba a jikinshi yake ba! Ga tsananin gajiyar da suke tare da ita Dan ma Allah ya taimaka Abokin Junaidu ne ya biya musu kud’in jirgi su kuma suka biyawa Baba Saboda yaga yanayin tsufansu gashi da ya kira Baban ma a hanya ya jisu suna dawowa daga wata tafiyar…. Ba dan haka ba

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});