Chapter 15
Chapter 15
shi da Hudan yake k’ok’arin toshe duk wata hanyar da zata kawo musu matsala, yanzu haka ya ware millions zai siya musu gida, ta yadda In su Mammy sun zo ba zasu samu abun kushewa ba balle har Granpa yaji ya hana, su Abba kuwa ya san su zasu zo nema mishi aure, so gidan uncle Muhammad ba zai zama matsala ba! Dan anan aka shirya za a had’u dan ba daban jiran Dad d’in da suka tsaya yi ba ma to da tuni sun zo an gama magana. Har ga Allah ba zai tab’a iya rayuwa babu Hudan ba, kwata kwata, shi baya jin ma a tarihi akwai wani mahaluk’in da ya tab’a yiwa wata kalar son da yake yiwa Huda since day 1, gashi kuma yau Mahaifiyarta da kanta ta kalle shi tace ‘zata rabashi da ita!’ Bai ankaraba kawai yaji hawaye yana wanke mishi fuska! Sunayen Allah ya fara ambata yanayi yana kuka, kamar k’aramin Yaro. Da kyar ya samu zuciyar data yunk’ura mishi ta d’an lafa. Ganin babu Mama ba labarin ta, ya sanya kawai ya yanke shawarar komawa gida yayi wanka daga nan ya kira Ummu a san abunyi! Dan in ba ruwa ya samu ya sakarwa kanshi ba baya jin kalmar ‘A’ zata iya futowa daga bakinshi a halin da yake ciki........... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 37 Kamar yadda Arshaad ya tsara, sai da ya lallab’a yayi wanka da kyar tare da hutun awa d’aya! Tukunna yaji d’an dama dama, cikin tsantsar mutuwar jiki ya lalubo wayarshi ya danna kiran Ummu. Sai da ta kusan katsewa tukunna aka d’auka, a tunanin shi ko hayaniyar biki ne yasa ta jinkirin amsawa sai dai kuma tana d’auka yaji hayaniya da koke koke! Cike da fargaba ya hau tambayarta, nan take gayamishi..... ....”Suna shirin shigowa Kano, wani Abokin Junaidu ya kira Baba! Bayan sun gaisa ne yake ce mishi ‘dama ya kira ne a kan maganar Junaidu! Wai an sake shi tun satin baya da ya wuce sai dai kuma babu irin kalar binciken da basu yi ba amman an rasa shi! Wajen kwana uku kenan yau. Lokacin da aka sallameshi yayi mishi waya yace ‘zai zo gidanshi, ya d’an kimtsa tukunna ya wuce Kano, bayaso ya sanar da kowa dan surprise zai yi musu’. Yayi ta zaman jiran nashi amma shiru! Sau daga baya yaji labarin accident da aka samu a garin guda uku ata wajajen k’iri k’iri d’in! mota biyu ta y’an kasuwa ce, d’ayar kuwa ta prisoners d’in ne waenda aka saki sai dai kuma duk sun k’one k’urmus! Dan ko iya tantancesu ba a yi! Yayi shiru ya tsaya bai fad’a musu ba domin yanaso yayi bincike sosai tukunna dan shi tunanin shi yana bashi ba lalle har da Junaidun ba amman duk wani investigation yana tabbatar da akwai gawar Junaidun a ciki! Shiyasa kawai ya yanke shawarar kira ya fad’a musu..’ Gashinan yanzu haka a mutuary in babu damuwa wasu a cikinsu suzo dan ana da buk’atar su wajen tantance gawar da kuma ragowar abubuwan da ya kamata!!’.” (Da kyar Baba ya iya k’arasawa gida ya d’auki kud’ad’e da atms da abun buk’ata ya mik’a Ja’afar wajen K’asimu suka kama hanyar Lagos! Suma su Abba Madu suna ajjiyesu a gidan Baaba Talatu ya juya shi da su Ya Jamilu. Yanzu haka sun kama hanyar Lagos d’in.) “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” Shine abunda Arshaad yayi ta maimaitawa, yana jiwo Sadiya tana ihu tana wallahi “sai tayi sharia da y’an sanda da sojojin da suka rik’e mata Yaro bayan sun gano bashi da laifin komai! Inda ace sun bari ranar su Madu sun dawo da shi ai da duk haka ba ta faru ba! Allah ya isanta” Baba Talatu ce ta hau yi mata fad’a, tana cewa “Bata da tawakkali ne? In Allah ya riga ya tsara abu dole sai ya faru! Ta daina yi mishi kururuwa da ihu…” Amman inaaa, bata ji bata gani sai rafka kuka da kururuwar kawai take yi. Jin yadda gidan ya hautsine ne ya sanya kawai yanke shawarar zai nemo Mama da kanshi in shaa Allah, dan haka yayiwa Ummu gaisuwa, kafin ya kashe wayar. .............. Kusan a tare motar Abba da ta Aslam suka k’araso cikin estate d’in! Basu shiga ko wanne gida ba suka yi parking a babban parking lot d’in estate d’in kamar had’in baki. Abba ne ya fara fitowa kafin Aslam, yana k’arasowa inda yake yace “Ka kaita wajen Gwaggo Asabe. Zan nemaku zuwa anjima.” “Ok” Shine abinda Aslam d’in yace sannan ya juya ya fara k’ok’arin bud’e inda Huda take zaune tana kuka har yanzun, shi kuma Abba ya juya ya nufi gidan Ummi. Hannunta ya sake fincika bayan ya bud’e motar ya fito da ita!! Sannan ya zaro wayarshi ya danna kiran Gwaggo Asabe ya kara wayar a kunnenshi… Fisge hannunta tayi da duk k’arfin ta! Sannan ta juya ta bud’e motar ta d’au wayarta tana dubawa dan ita a nata tunanin ma ta fashe ne saboda yadda Aslam d’in ya had’a wayar da hannunta ya runtse a nasa hannunt tun lokacin da yace ‘Mama ba zata tafi da ita ba’ har sanda ya kaita mota…. Rad’ad’i da zugin da hannunta yake mata da kuma tsananin tashin hankalin da take a ciki ne suka hanata d’aukar wayar data fad’i daga hannunta tun shigar ta motar, sai yanzu Ajiyar zuciya ta sauk’e ganin bata yi komai ba hakan yasa ta rufe motar ta d’an juyo da niyyar kiran Mama. D’an satar kallonshi tayi, ganin ya tsareta da dara daran idanuwanshi ne ya sanya ta yin k’asa da kanta sannan tace “Ko baka ja ni ba zan bika! Wayata kawai na d’auka” Tayi maganar cikin muryar kuka. Murmushin rainin wayo yayi mata, kafin yace “Better!” Sannan ya juya ya fara tafiya yana cewa “Gwaggon ta fito, yanada bak’uwar da zai bata, ta same shi a gate!” Hudan kuwa wata zuciyar ce take ce mata ‘ta d’iba a guje ta fice a estate din!’ Amman kuma ta na juyawa tayi ido hud’u da sojoji har hud’u a wajen gate d’in suna zazzaune. Wani sabon kuka ta fashe da shi kafin ta durk’ushe a wajen abun tausayi… A hankali kuma sai ta d’ago wayar tata ta fara k’ok’arin kiran Mama tana adduar Allah yasa taga purse d’inta ta d’auka a cikin d’akin, dan lokacin da Aslam ya jawota purse d’in ta fad’i a k’asa. Aslam kuwa jin da yayi kamar ba mutun a bayan shi ne ya sanya ya juyo dai dai ita kuma da d’ago kanta sukai ido biyu! A zuciye ya taho gadan gadan yana nad’e hannun rigar shi, Ta san me yake shirin yi hakan yasa ta mik’e da sauri, kafin ya k’araso ita tayi hanyar da taga yayi….. Rashin kwarin jiki da kukan da taci ne yasa har yazo ya gota ta ya zamana ita take binshi a baya. Kamar yadda suka yi a bakin Gate d’in ya tarar da Gwaggo Asabe tana jira, nuna mata Hudan kawai yayi sannan yace “Zuwa anjima zan kiraki!” Da mamaki tab fuskarta take kallon Hudan ganin yadda yake kallonta ne ya sata kawai jan hannunta suka shige ciki shi kuma ya nufi gidan Mammy a falon ta na sama ya samu doguwar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96