Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kujera ya kwanta, zuciyarshi fal da tunani barkatai. ....... A parlourn k’asa Abba ya samu Ummi tana shafa wa jan lallen da aka gama cire mata yanzu mahallabiya. Sallamarshi ce ta katse musu k’us k’us d’in da suke yi ita da Mom wadda ake k’arasa saka mata nata lallen yanzu. Da sauri ta d’ago jin muryar shi, su na had’a ido ta sakar mishi murmushi sannan ta mik’e ta nufe shi…. Bata damu da Mom da mai lallen da suke parlourn ba! Tana isa gareshi tayi hugging d’inshi tana mai yi masa sannu da zuwa…… Binta kawai yake yi da ido, tanata karairaya… A hankali yasa hannu ya zarota daga jikinshi kafin yace “Ki kawo mini abincina sama, kaina yana d’an yi min ciwo.” Murmushi ta kuma saki kafin tace “ok dear” Ta juya, shi kuma ya kama hanyar b’angaren shi. Sai da taga hayewarshi sannan taje wajen Mom ta rad’a mata wata magana, a take suka kwashe da dariya kafin Mom d’in tace “ki tabbatar kin yi amfani da abunda na baki.” Dariya tayi sannan tace “da gudu ma kuwa” kafin ta nufi hanyar kitchen tanata rawar kai! A nutse ta sake gyara kulolin har da ruwan tea tayi mishi warming da duk wani abunda ta san zai buk’ata. Haka nan ta had’o abincin a k’aton baske tayi saman itama. Abba yana shiga d’aki ya kira Dad…bayan sun gaisa ya zayyanewa Dad d’in komai bai b’oye mishi ba! Dad was very shocked daga jin Abba yana da y’a da Maryam!! Tabbas shima ya na zargin waenda Abban yake zargi… Maganar Abban ce ta katse mishi tunani jin yana cewa “Yaya kayi hak’uri da abunda zan aikata, dan Wallahi ko waye yake da hannu, a cikin lamarin nan zan hukuntashi!!Ba zan duba relationship d’in ka da shi ba, gaskiya.” Ajiyar zuciya Dad ya sauk’e sannan yace “Kayi kwakkwaran bincike, kafin In k’araso, in shaa Allah ni da kaina zan tayaka hukunta masu laifi….. Daman jikin Mommy ne ya d’an tsaidamu amma da tuni mun iso ma.” A haka Ummi ta shigo ta sameshi, yana ganinta ya yiwa Yaya sallama ya katse wayar. A hankali ta k’araso ta ajjiye kafin cikin nutsuwa da karairaya ta hau serving nashi. Sai da ta gama ta ajjiye mishi a kan kafet sannan ta d’ago hannuwanta tace “Kaga k’unshi da nayi saboda na san kanaso, in je a zana min bak’in flower ko ka fi son shi ahaka??” Fararaen hannun nata ya kalla da jan lallen ya yiwa matuk’ar kyau amma sai dai shi memokon yaga kyan shi ma, gaba d’aya sai yaji ya tsani jan lalle a take a lokacin!. “Ki barshi haka.” Shine kawai abinda ya iya fitowa daga bakinshi. Mamakin yadda idanunsa suka kad’a suka jazirr!! take Chan kuma sai tayi murmushi..yanayin yadda ya shigo jikinshi a sanyaye, da kuma yadda yanzu taga yanayinshi tabbas ta gane mai yake buk’ata! Hakan yasa ta fara k’ok’arin mik’ewa dan ta samu taje ta yi amfani da abunda Mom ta bata. “Na had’u da Maryam yau...” Wata mahaukaciyar razana tayi kafin ta koma ta zauna kamar wadda aka jawo da k’arfi!!!. Kafeta yayi da idanuwanshi… Yana ganin yadda gaba d’aya ilahirin jikinta yake karkarwa ga wata uwar zufa da take keto mata dukda kuwa sanyin ACn da ya ratsa ko wacece kusurwa ta d’akin. Ya akai suka had’u? A ina suka had’u? Sun yu magana kenan? Ta fad’a mishi komai?… Sune tambayoyin da suka taru suka sake gigitata! D’agowa tayi za tayi magana, sai kuma taga yadda ya zuba mata lulu eyes d’inshi da sukai jaa, wanda sai yanzu ne ta gane b’acin raine, ashe. Tattaro duk wata basira da wayon da Allah ya bata tayi kana ta had’a da y’ar ragowar jarumta da kwarin jikinta, kafin tace “Wannan kuma matsalarkace! Tunda har ka bijirewa Mahaifinki wanda yayi ik’irarin tsine maka a kanta, to me yasa ni zan tsaya damuwa da kishi?” Tana gama fad’in haka ta fara k’ok’arin mik’ewa, dan tabbas In taci gaba da zama to nan da nan zai b’aro jirginta. Dukda cewa bata da tabbacin Maryam d’in ta gaya mishi sunada baby tare, amman hatta muryarta rawa take yi, sannan idanuwanta duk sun kawo ruwa! Ga shi kuma Abban ya tsare ta da ido, it’s like akwai abinda yake son fahimta… Dan haka ta mik’e tayi hanyar k’ofar fita da sassarfa. Abinda bata saniba shine tun a reaction d’inta na farko Abba ya riga ya b’aro jirginta, gashi kuma yanzu rashin wayonta na son barin d’akin ya sake tabbatar mishi! Dan haka yayi hanzarin mik’ewa shima, ya rigata isa ga k’ofar ya shiga gabanta ya tsaya!. Kasa d’agowa tayi ta kalleshi.. He can feel yadda numfashinta suke korar juna daga inda yake tsaye!. Juyawa kawai yai ya murza key d’in ya zare shi, sannan ya cilla cikin aljihun wandon shi. A take razana da firgicin da take ciki suka sake hauhawa! Tun ba ma daya juyo taga yadda ya tamke fuska kamar bai tab’a dariya ba, zata iya rantsuwa tunda aka haifota duniya bata tab’a ganin Abba a irin wannan yanayin ba. Cikin dakakkiyar muryar da bata da alamun wasa a cikinta yace “Ummi!! A cikin biyun nan, inaso ki zab’i d’aya.” Yayi maganar yana mata alamu da y’an yatsun hannunshi na dama daya d’aga mata su daidai setin fuskarta. Na farko Ko ki gaya min gaskiya tun farko abunda ya faru…yadda kuka yi kuka rufe ba tare da kowa ya ji ba, da yadda aka y munanan kalaman da ban san na rubuta suba suka isa ga Maryam, Inason jin komai da komai karki b’oye min ko, alif. Ko kuma (na biyu) In yi miki dukan mutuwar da ko Mahaifiyar ki in da ace zata dawo duniya ba lalle ta shaidakiba, sannan in k’ara miki da saki, kuma in kulle ki dake da duk wanda ya taimaka miki.! Sannan inaso ki sani sharia zan yi ta gaskiya yadda ko Granpa bai isa ya kwatoki ba wallahi, idan kuma ya tilastamin to tabbas zamu iya samun matsala da shi dan ba zan iya yi mishi biyayya wajen wofantar da hukunta waenda suka raba ni da y’ata ba!.” Wani irin mahaukacin bugawa k’irjin Ummi ya hau yi, especially ma da taji zancenshi na k’arshe. Amma Maryam an yi shegiyar mata!! Wato fad’a mishi tayi kenan! Yanzu Ina mafita?? K’aryatawa za tayi ko kuma ya zata yi? Itakam yau ta shiga tara ma ba uku ba! Ga shi ba Mom a kusa. “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” Ta fara maimaitawa tana neman taimakon Ubangiji, dan tabbas shi kad’ai ne zai iya cetonta a hannun Abba a yau. Tsawar da ya daka mata ne, ya katse mata tunanin, a take ta durk’ushe a wajen ta fara kuka. “Ba kya ji na ne!!!!” Ya fad’a cikin hargowa har wata kwalla tana zuba daga idonshi tsabar b’acin rai. Shiru tayi in banda kuka ba abunda take yi. Dukan mace kwata kwata baya cikin tsarin Abba But Ummi left him with no other choice, bai san lokacin da ya fincikota ya mik’ar da ita tsaye ba! Bata gama sosa, gefen wuyanta da takeji kamar ta yanke sakamokon janyotan da yayi da hannun rigarta ba, taji sauk’ar wani irin gigitaccen Marin da ya kusan d’auke mata nunfashi, bata gama

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});