Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mishi asiri, wallahi.” Auwal kamar yayi hauka, gashi an gama kwashe kaya ya san shi kawai Daddy yake jira ya kai Jalila sannan yazo su tafi, ga kuma batun ta na zata tona mishi asiri, kar fa Yarinyar nan ta jik’a mishi aiki!! A daa yana underestimating d’inta yanzu kam ta fara bashi tsoro gaskiya, he has to do something, duk da cewa Mom tace mishi ‘ya jira ta tana dawowa zata yi maganinta’ amman gaskiya he cant wait!! Yana tsoro kar kwab’arsa tayi ruwa, gara kawai ya k’are komai dan shi gani yake ma it’s like sun rabu da Arshaad d’in tunda ta sameshi dan haka tayaya zai iya breaking d’inshi!!! Takaici ya taru ya yiwa Auwal yawa, ga Jalila sai maganganu take yab’a masa… Da kyar ya iya controlling kanshi dan ji yake yi kamar yaje ya rufeta da duka ko ya samu sauk’i! A hankali very calm ya k’arasa inda take ya kamo hannunta Da sauri ta fisge hannun kafin tace “Ai wallahi anyi an gama babu k’ari!! Mayaudari kawai, haka kurum ka cuceni! Ga wasu zantukanka waenda har yau na kasa fahimtar alk’iblarka a kaina..” Cikin tsananin fushin da ya kasa dannewa yace “na cuceki ko kin cuce ni?? Ke kin San ko waye ni kuwa? Wallahi ba dan abunda na shirya akan ki ba ko a y’ar aiki ba zan tab’a yarda ki zo mini ba! Kina magana kamar irin dole d’innan nayi miki, Ina ce da yardarki kika bini har gidan? Zaki wani rainawa mutane hankali, wallahi ki bini a hankali tun ban fito miki a asalin Auwal d’ina ba!! Magana kad’an In anyi kice wani ‘za kije ki tona min asiri’ To bari kiji, tsaf! Zan iya cewa Daddy na maidake gida! In kulle ki anan yunwa ta kasheki daga baya in zo in fitar da gawar ki babu wanda zai ji labari, tunda itama uwarki kwad’ayi ya rufe mata ido ai bata cewa kowa kina nan ba! Stupid useless girl kawai! Banza wadda bata da daraja kwata kwata, Akuya ma ta fiki daraja tunda ita wani lokacin tana guduwa tana jan aji, ke kuwa ana ce miki kule za ki ce cass!.” Takaici da tsoro ne suka sanya Jalila fashewa da kuka, wani irin takaicin Umma take ji yana taso mata.. Shiyasa fa ita tayi ta dodging, har ga Allah irin rayuwar nan da yadda ta yarda dashi nan da nan ba hakan ta tsarawa kanta ba! Ita dai ta san tanada burin son auren mai kud’i, amma kalli yanzu yadda ta koma, duk ata dalilin biyewa son zuciyar Umma, gashi ta hanata zubar da cikin, kamar ba ita ta tsugunna ta haifeta ba! Tunda take ba a tab’a yi mata zagin daya girgiza taji haushinshi ba kamar kalar zagin da Auwal yake yi mata especially na yau dan ko ranar daya maidata gida bata ji ciwon zagin kamar na yau ba, kuma gaskiya ya fad’a!. Gashi yanda taga ya birkice tabbas zai iya aikata abunda ya fad’a d’in… Kuka take yi bil hakk’i da gaskiya. A take ta gama tsarawa kanta zata ce a zubar da cikin kawai ta koma wajen Umma, kowa ya huta. Ganin yadda tayi ladab ne ya k’ara bawa bawa Auwal kwarin guiwar aiwatar da abunda kwakwalwarshi ta shirya mishi yanzun nan, dan haka ya k’arasa inda take tsugunne shima ya tsugunna, fuskarshi ba alamun wasa yace “Look Jalila, let’s just get this done over with… Zan baki 5 million” Da sauri ta d’ago manyan idanuwanta tana kallonshi. D’aga kanshi yayi alamun ‘yes’ sannan yace “Miliyan biyar!” All I want you to do is ‘Kice cikinnan na Arshaad ne, kuma in sama da k’asa zasu had’e kar ki chanja maganan ki, ko a gaban waye, ke hatta uwar data haifeki inaso ki birkice mata kice na Arshaad ne kawai!’ Gaskiyar Maganar ya tsaya daga ni sai ke. Kar ki damu In komai yazo gangara ni zan san yadda zan yi, komai zai fita normal, ba zaki samu wata matsala ba, understood???”. Rarraba ido ta fara yi tana k’ok’arin yin magana, suka jiyo sallamar Arshaad. D’agowa sukayi dukkansu suna kallon hanyar shigowa. Cikin takunshi ya k’araso cikin parlour… Wani killer smile Auwal yayi kafin ya mik’e tsaye yace “D’an halak! Maganar ka muke yi” Cikin nutsuwa Arshaad d’in ya k’araso inda suke, kallon Jalila yayi yaga yanda take kuka, a ranshi yana mamakin ina Auwal ya samota haka, gashi sai kuka take yi… Ganin ba wannan ne ya kawo shi ba yasa ya d’auke idonshi a kanta ya maida kan Auwal d’in sannan yace “Daddy is waiting, infact everyone, for you, kayi sauri dan yace karka bari yazo ya sameka a nan!” Yana gama fad’in haka ya juya ya fara k’ok’arin fita. Da mamaki Auwal yake kallonshi da Jalilan wadda tunda Arshaad d’in ya fara magana take kallonshi, Ganin arshaad d’in na shirin fita ba tare da ya ma sake kallon Jalilan ba yasa Auwal yin ta maza ya zagaya ya tsaya a gaban shi sannan yace “Saurin me kake yi? I’m just trying to clean up your mess here fa, amman kayi kamar ma baka santa ba, ko In barta ta tafi wajen su Abba ne?” D’an dakatawa Arshaad yayi sai kuma ya juya yana kallon Jalilan.. Da ido Auwal yayi mata signal d’in da ta kasa ganewa, ita dai kawai sai ta mik’e, kamar an tsoma ta a ruwa jikinta na d’an rawa. Murmushi Auwal d’in yayi sannan ya zagayo yace “Talk mana Jalila, ko tsoronshi kike ji yau kuma?” Kame kame Jalila ta fara yi, ta rasa ta Ina zata fara dan Bata san me zata ce ba, gashi duk da halin da take ciki tunda taji Auwal ya ambaci miliyan biyar ta rikice, hali zanen dutse!. Don haka tace “Daman nazo ne akan maganar mu” Tayi maganar jikina na d’an karkarwa dan har yanxu k’irjinta bugawa yake yi… yau ce rana ta farko data tsaya ta k’arewa Arshaad kallo!! Ita dai tun lokacin da yake zuwa wajen Hudan ta san yana burgeta kuma yanayin shi, maganarsa, tsayi da k’amshin turarenshi suna mugun k’ara kid’imata! Kawai dai ita ta san tana so Arshaad har cikin zuciyarta, amman yau data tsaya ta k’are mishi kallo ta sake rikicewa kuma ta tabbatar idan har bata sameshiba to ko dai ta mutu ko kuma ta shiga hauka… K’irjinta in banda bugawa babu abinda yake yi, gashi ya tsareta da dogayen shanyayyun idanuwanshi, cikin tsare gida yace “Wacce magana kenan?? Do i know you?” Wata dariya Auwal ya saka kafin ya k’araso yana cewa “Okayy!! Bari in yi maka dalla dalla.. Maganar cikinka wanda ke a jikinta! Shi ta biyo ka ku k’arasa.” Arshaad zuwa yanzu yazo wuya! Don haka ya yanke shawarar cin uban Auwal dan ya lura bayan rainin hankalin da yake yi mishi, harda hauka ma ya fara damunshi kwana biyu, gara a yita ta k’are ko zai dawo hankalin shi, in hauka ya za ayi ya d’auko Yarinyar da bai tab’a ganiba a rayuwarshi ya hau yi mishi wani maganan banza da wofi??! A fusace ya juyo yana shirin yin kan Auwal, sukaji k’arar fad’uwar abu, da sauri duk suka juya suna kallon k’ofa.. Arshaad, ya san yana da gaskiya amman kalar kallon tuhumar da

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});