Chapter 27
Chapter 27
zai yi mishi maganan Arshaad amman yaji shiru shiyasa shima yana yiwa Maman ‘ya jiki’ ya fita, dan baya so suyi mishi d’in, but ya tsara a ranshi zai gayawa matarshi, duk abinda ya sani, da kuma dalilin yin shirun da yai, saboda kar ayi mishi kallon munafuki. Sai da suka biya duk wani bill sannan suka tafi a lokacin an tafi da mama yi mata eco. Su Kaka ma shirin tafiya gidan su Abba suka yi, aka bar Baaba Talatu. Sai a sannan ne Baba yazo, ganin Maman bata nan yasa suka gaisa da Baaba Talatu ya wuce kasuwa akan zai dawo da azahar in shaa Allah. Su Kaka basu samu damar zuwa gidan su Abba ba, sai la’asar, a sakamokon kiran da aka yi musu akan results d’in da ya fito, dangane da case d’in Junaidu......... Yadda Hudan taga rana haka taga dare, Gwaggo Asabe har mamakinta take yi dan duk juyi in tayi sai taga idonta biyu! Gaba d’aya ta kasa bacci ta k’agu Safiya tayi taje taga jikin Maama, da taga safiya ta k’i yi k’arshe kawai mik’ewa tayi taje ta d’auro alwalla, tazo ta fara jero nafilfili. Tana idar da sallar asuba kuwa bayan ta gama Azkar ta d’anyi karatu, ta shiga tayi wanka. Tana fitowa ta tarar Gwaggo Asabe bata d’akin, hatta sallayar data barta akai ta nad’e. Doguwar rigar da Gwaggo Asaben ta bata jiya had’e da Maclean da brush sabbi ta d’auka ta sanya, luckily ta samu comb a d’akin cikin drawer, dan haka ta goge shi da tissue sannan ta sa hannu ta zare ribbom d’inta ta hau ware tufkar da ta yiwa dogon gashinta wanda yanzu har ya kai tsakiyar bayanta….ita kanta tana mamakin yadda ya tofo a cikin shekara uku! Bayan askin dolen da Ya Jalila tayi mata… Tunawa tayi da Jalila wadda Sakina tayi mata k’us k’us d’in Khadija tace mata ‘kamar ciki ne da ita( Jalilan)’ amman Umma tayi k’arya tace ‘ta tafi jinyar Hansai’. A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya a ranta tana adduar ‘Allah yasa ba cikin ne da ita da gaske ba’ ….abunka da zuciya mai kyau! gaba d’aya duk sai taji tausayin Yayar tata ya lullub’eta, don haka ta hau yi mata addua da fatan alkhairi, tanayi tana taje kanta. Sai da ta gama tsaf, ta d’auko ribbon d’in ta tufke gashin a d’an k’asan tsakiyar kanta kad’an! Ganin yadda jelar take reto ne ya sanya ta kanannad’e gashin waje guda ta tura ta had’e da ribbon d’in, d’ankwalin doguwar rigar ta d’auko tayi style d’in V da d’aurin very simple amman ba karamin kyau tayi ba, ga gashin data duk’unk’une ana iya hango santsi da kyallin shi da uban yawa dan d’ankwalin k’aramine sosai so bai gama rufewa ba. Ta d’auko wayarta kenan zata kira su Mama ta ganta a kashe, ba chargi. Ajiyar zuciya ta sauk’e, daman ta san za ai haka, dan tun jiya chrgin ta yayi low sosai. Zama tayintana jiran Gwaggwo Asabe ta dawo ta ari wayarta ta kira su Mama don duk ta haddace nambobin su. Kusan minti arbain taji shiru.. ga anxiety yana neman kashe ta! Shiyasa ta yanke shawarar mik’ewa, ta hau nemanta. Bata wani sha wahalan neman nata ba, dan tana fitowa daga d’akin taji k’amshi ya cika ko Ina a gidan wanda hakan ne ya tabbatar mata da inda take(Gwaggwo Asaben), dan haka ta nufi k’asa. A k’ofar kitchen d’in suka had’u da Gwaggon, da tray a hannun ta, da kuma tea flask da ta rik’e da kyar. Sai da Hudan da d’an rissinar da kai tukunna ta gaisheta. Da kulawa Gwaggo Asabe ta amsa… Har ga Allah ta dad’e bata had’u da Yarinya mai hankali da nutsuwa irin Huda ba, ga kyau tubarkallah…shiyasa lokaci guda suka saba, taji ta shiga ranta sosai! Har k’asan zuciyarta take yiwa Aslam d’insu kwad’ayin auren Yarinyar saboda ta had’a komai ga kyau ga hankali ga nutsuwa gata y’ar uwarshi! Sai dai kuma yadda taga Arshaad yana shige mata sosai, watak’il shi ne zai fara cewa yana sonta, dan jiya ta lura har wata y’ar hira suka tsaya yi a parlour, sai wani nan nan yake yi da ita….. Hannu Huda ta saka tana k’ok’arin karb’ar tea flask d’in dake hannunta wanda hakan ne ya katse mata tunanin ta! Ba musu ta sakar mata , dan itama tana jin yadda ya kusan fad’uwa. A tare suka nufi hanyar sama, tana gaba Hudan na biye mata baya, wata hanya suka kuma d’auka bayan sun shanye stairs d’in, nan ta sake hango wani bene, benen suka bi suka hau, suna kaiwa k’arshe suka tarar ta wata y’ar k’ofa A bud’e k’ofar take hakan yasa suka shige, dogon corridor ne sosai, sai k’ofofi biyu, d’aya a farko farko hanyar dama, d’ayar kuma a kusan k’arshen dogon corridor d’in ta hannun hagu, Wadda itan taga Gwaggwon ta nufa, sai da suka iso bakin k’ofar, tukun suka tsaya! Rik’on tray d’in Gwaggwo Asabe ta gyara sosai a hannu d’aya sanna tasa hannu tayi knocking, tukun taja ta tsaya, ta gyara ruk’on tray d’in. Kusan minti biyu tukunna suka ji ance “come in” Hudan ta kalla tace “tayi amfani da empty hand d’inta ta bud’e musu.” Hakan tayi, bayan ta murd’a handle d’in a hankali ta d’an tura sai kuma ta matsawa Gwaggo Asabe don ta fara shiga.. Murmushi Gwaggon Asabe tayi sannan ta shige Itama Hudan ta bita a baya. Sai da ta rufe k’ofar tukun ta juyo ta fara kallon d’akin…. “Ma shaa Allah” tace, a ranta. Ba zaka kirashi d’aki ba kuma ba zaka kirashi da parlour ba, ga set d’in kujeru har da k’aramin dining, da makekiyar tv d’in da bata tab’a ganin irin ta ba, ga kuma set d’in gado shima komai akwai, royal, light blue da fari haka colour d’in kujeru da gadon suke, hatta pentin d’akin haka yake. Ga kuma wani glass door, wanda kana iya hango swimming pool da shuke shuke da kujerun shak’atawa. K’auyanci ta fara, don a ranta ta hau rayawa “daman ana pool a sama? saman ma ta biyu! Ita tunda take bata tab’a ganin d’aki mai girma sosai da kyau irin wannan ba!”…… Tunanin ta ne ya katse jin Dad yana cewa “Hudan k’araso mana ya kika tsaya a k’ofa?”. Sai a lokacin hankalin ta ya kai kan Dad, da wata mata a zaune a gefen shi yana rik’e da hannunta. Ji tayi kamar ta rusa kuka!! Da ta san gurinshi Gwaggo Asabe zata zo da bata biyo ta ba, kenan ita duk b’uyab da takeyi ma a banza, tunda gashi a gidanshi ma ta kwana ba tare data sani ba, kuma yadda ya nuna it’s like ya san tana nan d’in, shikenan ta san yanzu zai kira Abba shi kuma ya hanata zuwa taga Mama. Gwaggo Asabe ce ta katsemata tunani jin ta sake cewa “Huda k’araso mana.” A hankali take takawa izuwa bakin gadon inda suke… Taji Dad yana cewa “Ashe da gaskiyar Abba, daman ya ce tana wajensu Aslam ni ban yarda ba, sune suka kawota jiyan ko?” D’an murmushi Gwaggo Asabe tayi kafin tace “Eh jiya lokacin da ka kira ni, Arshaad bai dad’e da kawota ba, shi ya rakota.” Hudan dake jin su duk sai taji
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96