Chapter 82
Chapter 82
Da sauri Mammy tace “Wallahi Hajiya Hudan ba k’aramin alhaki bace ba! Ki dubafa ki ga tun daga ranar data shigo estate d’innan nake cikin tashin hankali..” Cikin d’an b’acin rai Maman nata tace “To yanzu ya za ki yi? Kinga fa wannan abun da muka san za kiyi wallahi shiyasa muka k’i mu fad’a miki maganar auren tun kina cell! Ki tsaya ki danne zuciyarki yanda kika saba, ki fara gano matsalar da ta shiga tsakaninki da Mijinki a samu a gyara a shawo kanshi in yaso daga baya sai kiyi yadda kikeso Amman yanzu idan kikayi yunk’urin hana auren nan, wallahi kowa bak’in ki zai gani, kuma hatta Arshaad d’in dakike ta haukar ‘kar Hudan ta janye miki shi’ Ke ce da kanki gashi kike k’ok’arin kawo matsala a tsakaninku da kanki gashi kina turashi away from you dan Wallahi kinji na rantse miki yadda Arshaad ya kwallafa rai akan Yarinyar nan muddin kika sake kika zama silar da ya rasata to kuwa ba zai tab’a yafe miki ba! Kuma sai kin yi dana sani. Ki bari ayi auren sai mu san abunyi. Yanzu kar ki fito b’aro b’aro a matsayin wadda ta hanashi aurent....” Cikin katseta Mammy tace “Ki kwantar da hankalinki ni na san ta inda zan b’ullo mishi yana jin maganata ai yana yi min biyayya. Matsalar da za a samu shine In har na bari ya aureta! D’azu fa muka gama waya da Adama wai ashe ma k’asar za su bari gaba d’aya! Haba dan Allah taya ba zan yi kuka ba? D’ana kwalli d’aya a duniya zata d’auke shi su tafi sai ta gama mallakeshi tukun a dawo min da fanko? Dama yanzun ma ya aka k’are?? Ballantana kuma yaje yayi spending years da ita! Ni kawai ku kyaleni dan girman Allah, dan na tabbatar ranar da Arshaad ya aureta to ni kuma zan iya barin duniyar nan a ranar.” Ta k’arashe tana sake fashewa da wani sabon kuka. Cikin fad’a Maman nata tace “Baki rabu da su Adaman nan ba har yanzu ko? Na ce miki ki tsaya ku fara shiryawa da Mijinki ki fara gano matsalar da ta shig..........” Da sauri Mammy tace “Matsalata da Dad, Aisha ce! Na rigada na sani. Ki bari kawai in fara kashe wannan boss d’in after that idan na tashi bi ta kan Aisha wallahi duk wanda ya ce zai shiga tsakani sai na had’a da shi”. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 52 Cikin fad’a Maman nata tace “Baki rabu da su Adaman nan ba har yanzu ko? Na ce miki ki tsaya ku fara shiryawa da Mijinki ki fara gano matsalar da ta shig..........” Da sauri Mammy tace “Matsalata da Dad, Aisha ce! Na rigada na sani. Ki bari kawai in fara kashe wannan boss d’in after that idan na tashi bi ta kan Aisha wallahi duk wanda ya ce zai shiga tsakani sai na had’a da shi”. Tana gama fad’in haka ta juya ta fice da sauri tana share hawayenta. Ko bi ta kan y’an parlourn bata yi ba, ta wuce sama abunta tana huci. Tana fita Maman nata ta sauk’e ajiyar zuciya! A hankali ta kalli Hajiya Binta tace “Allah ya rufa asiri..tunda tak’i jin maganata ni uwarta! Ni zan tafi yanzu, idan ta yarda aje wajen event d’in su Amaryar to ku rakashi Idan kuma ta hana sai ku zuba mata ido. Sannan ki samu y’an uwanki ki jasu gefe kice nace ‘ko me zata yi kar wanda yayi yunk’urin hanata’ Ita ta sani. Taje tayi yadda taga ya dace.” Tana gama fad’in haka itama tayi hanyar waje cikin y’ar tafiyar su ta tsoffi... Sallama ta yiwa matan dake babban parlourn daga nan ta wuce abunta. Har k’ofar mota ragowar sister’s d’in Mammy guda biyu k’annenta suka rakata, suka bud’e mata gidan baya ta shiga suka rufe driver yaja suka tafi. Su duk basu san wainar da ake toyawa ba Hajiya Binta wadda ta kasa fitowa parlourn tun tafiyar Mahaifiyar tasu ce kawai ta sani dan haka suna komawa aka shiga bidiri ana ciye ciye ana ta hotuna! Fitowar Ango da Aaima ne ya k’arawa abun armashi, ba a dad’e ba Mom da Ummi wadda ta d’an ji sauk’i suka shigo, nan suka had’u aka yi ta hotuna…. After kamar 30 minutes haka, aka fara shirye shiryen tafiya gidan su Amarya, anata had’a gifts.. Dai dai nan Mammy ta sauk’o. Sai da gaban Arshaad ya yanke ya fad’i amman ya dake ya k’arasa inda take ya fara k’ok’arin jan hannunta yana cewa “ta zo su yi hoto” Ko alamar zata motsa bata yi ba dan haka ya tsaya ya d’an kalleta yace “Mammy dan Allah mana, mutane suna kallo fa, ki zo muje” Ya fad’a yana sake k’ok’arin janta. Suna a haka sisters d’inta da Aaima suka iso wajen. Fisgewa tayi da mugun k’arfi, kafin tace masa “Idan baka je ka cire wannan wata kalar shigar ba wallahi Arshaad sai na ci ubanka!! Sannan ni za ka mayar y’ar iska mai magana biyu? Mu gama magana da kai amma ka je ka wani shirya tsaf sannan dan tsabar raini kazo kana ce min wani muje muyi hoto? Da kai da hoton kun ci kutumar ubanku!” Runtse idanunsa yayi da mugun k’arfi! Dai dai nan Mommy da Aslam waenda suka shigo yanzun suka nufo su, suka k’araso! Kusan duk sun ji furucinta. Da mamaki suke kallonta, a hankali Aslam yad’an dafa kafad’ar Arshaad d’in, dukda bai gama sanin wainar da ake toyawa ba amman yad’an fahimci wani abun, hakan ya sanya shi jin mugun tausayinsa ya rufeshi.... Da mamaki Mommy take kallon Mammy kafin tace “Lafiya kuwa? Me naji kamar kin ce?” “Amin, wa alaiki Assalam Aisha!” Mammy ta fad’a cikin tsareta da ido tana jin wani mugun tsanarta na taso mata… Murmushi Mommy tayi kafin tace “Assalam alaikom, me yake faruwa ne Arshaad?” Ta yi maganar tana me mayar da akalar tambayar tata kan Arshaad saboda tsananin mamakin Mammy da ya rufeta.. Tunda suke tare ko da wasa Mammy bata tab’a yi mata kwatankwacin irin haka ba. Arshaad Yana shirin yin magana Mom ta k’araso tace “Ya dai? Kukayi cirko cirko duk anan?” Kafin ta kalli Mommy tace “Ina ta yi miki magana Mommy, kika k’i kulani kika wuce. Ina wuni.” Dai dai nan Ummi itama ta k’araso wajen nasu. Cikin kulawa Mommy tace “Yi hak’uri Adama, hankalina ya yo kansu ne dan naga kamar ba k’alau ba.” Da sauri Mammy tace “K’alau d’in....” Cikin katseta da d’an k’arfi Mom tace “Haba k’alau ne mana, komai normal Ina?” Ta fad’i hakan tana kallon Mammy da d’an sign d’in tayi calming down mana… Tsaf Mammy ta fahimceta.. Itafa ta rasa gane dalilin da yasa su Adama da y’an uwanta suke tunanin zata iya yin wata kissa a wannan stage d’in! Taya ma zata iya danne wannan duka dubu d’in da akai mata? Ya an dake ta kuma suna so su hana ta kuka??… Mom na shirin yin magana taji Ummi tace “Arshaad akwai matsala ne? Yi magana mana, kar lokaci ya k’ure! Kaga yanzu tafiya za mu yi.” Da sauri Mommy tace “Dankuwa har na cewa Maryam d’in ma mun kusan fitowa, na san mu suke jira yanzu haka.” Ajiyar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96