Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 59

Chapter 59

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

b’ular gashin dake jikinta… Daman tun da safe da tace masa “za su fita ita da Ummu” taga kamar rashin yarda a fuskarshi. Laifinta d’aya da tak’i fad’a masa gaskiya wanda ita kuma dalilinta shine ‘Ta san ba barinta zai yi ba’ ita kuma har ga Allah tana so tazo taga Huda. Dafa ta d’in da Ummu tayi ne yasa ta d’anyi firgigit ta dawo cikin haiyyacinta, tana mai k’ak’alo murmushi. Cikin d’an k’arfin hali ta cewa su Huda “su koma gida, kar a ga sun dad’e.” Sai da suka d’anyi y’ar kwallar su, tukunna suka rabu bayan ta sake tambayar Hudan akan “tana son Arshaad d’in?” Hudan kuma ta amsa mata da ‘eh’ sannan suka wuce… …Tunda Ummu da Madu suka zaunar da ita( Mama) suka fahimtar da ita sosai ta d’an dawo saita, tana k’ok’ari taga ta jaa y’arta itama a jiki su zauna lafiya wata rana sai labari…fushi da turjiya ba inda yake kai mutum sai garin dana sani, In Allah yayi auren yanzu shine mafi alkhairi kuma sai anyi a yanzun to fa idan ta dage tace zata hana tsaf rabo zai iya kasheta! Shiyasa tun ranar farko a waya bayan su Hudan sun dawo da ta tambayeta ita kuma Hudan tace mata ‘eh, tana sonshi’ shikenan Mama ta shafe komai, ta rungumi abunda Allah ya k’addaro da hannu bibbiyu……. Da kyar suka samu adaidaita sahu, Ummu dai ta lura akwai abunda ya firgita Mama amman ganin tayi tanbayar har ta gaji bata bata amsar komai ba ya sanya kawai ta kyaleta, a tunaninta maybe ko Abba ta gani. Mama aka fara ajjiyewa, sannan Ummu suka wuce ita da mai napep d’in ko shiga bata yi ba dan yau week end so tana son yin kwalema, saboda tun da Sakina ta tafi aiyuka duk sun yi mata yawa sun ch’ab’e mata. Tun a soro taga machine d’in Baba kamar yanda ta fita ta bari, amman k’ofar d’akin shi a rufe da kwad’o! Tunani ta fara a ranta tace “kenan bai dawo ya d’auka ba ko dai aiki ya wuce a napep d’in? Mai yasa ma ya bisu a napep in the first place?….” Da wannan tunanin ta k’arasa k’ofar d’akinta ta zaro makulli a y’ar purse d’inta. Gidan shiruuu, ba kowa. Tana d’aura makullin a ramin shi taji k’ofar tayi motsi! A take gabanta ya yanke ya fad’i. A hankali ta d’an tura k’ofar, ga mamakinta sai ta ga ta bud’u! Cikin rawar murya tayi sallama tare da kutsa kai ta shiga ciki. Turus! Haka ta ja ta tsaya sakamokon ido hud’u da suka yi da Baba wand yake a kwance a kan gadon nata yayi pillow da hannuwanshi akan pillows d’in da ya d’aura kanshi, ya d’aura k’afa d’aya kan d’aya yana d’an jijjigawa…. Ba abunda yafi d’agawa Mama hankali sai yanda taga idanun Baba sun sauya kala! Idan aka ce mata tunda ya dawo yake kuka tabbas ba zata musa ba domin kuwa idanunsa sun yi jaaaaa!! Sun k’ank’ance hatta fuskarshi sai da ta d’an kumbura. Bata gama fahimtar yanayin da yake ciki ba taji yace “Ai nayi tunanin ba zaki dawo nan ba!” Yayi maganar yana mik’ewa ya isa k’ofar d’akin, kawai taga ya sa key ya juyo yana kallon ta. A take wani mugun tsoro ya dirar mata, for the first time da taji tsananin tsoron Baba tunda take a rayuwarta dan hatta yanayin maganar shi yau ta sauya, kamar wani wanda yayi shaye shaye. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e, yana kallonta kafin ya sake cewa “Tun yaushe kuka fara had’uwa?” Yayi mata tambayar yana kallon kwayar idanunta waenda suka rine da b’acin rai da takaici, ga tsoro sannan ga ruwan hawaye da ya cika su taf!! Itan ma shi take kallon, tsaf ta fahimci wa yake nufi amman kawai sai tace mishi “Da wa kenan??” Murmushi yayi, kafin yace “Abba” Kanshi tsaye. Hawayen da take k’ok’arin rik’ewa ne suka yi nasarar zubo mata, cikin karyewar zuciya tace “Zargina kake yi?” Bata jira jin amsarshiba taci gaba da magana “Ka yarda ko kar ka yarda Rabo na da in ga Abba a idona wallahi tun ranar da ya d’auke Huda daga wajena a asibiti! Wanda a ranar kuma rabona da shi shekara goma sha takwas!..” Cikin katseta yace “Mai ya kai ki gidanshi yau?” “Y’ata naje gani, kuma ko gidan ban shiga baduk da na san ka sani kuma ka gani….Indai bibiyar da kayi mini ta biya to ya kamata ace ka fahimci ba wajen Abba naje ba! Tun da muka je ko gate d’in gidan ban tab’a ba, kuma inda wajenshi zan je to da ba zan d’auki Ummu muje tare ba da ni kad’ai zan je.” Ajiyar zuciya ya sauk’e, ransa na k’arasa baci yace “Kinga kin kama kanki!! Abunda nake so inji kenan! Kalmar ki ta k’arshe da kika fad’a yanzun ta bada ma’ana kwarai Maryam! Amman karki damu dan a yau d’innan ba zan barki ba sai na tabbatar da cewa ko a hanya In Abban ya ganki ba lalle ya iya gane ki ba!” Cikin b’acin rai Mama tace “Ko a musulunci ba a aure da zargi! Na gaji da halinka na gaji da abunda kake yi min na gaji da komai na gidan nan! Kuma wallahi tunda zargina kake yi to ba zan sake zaman second d’aya da kai ba!.” Ta k’arashe maganar tana kuka ta zagayeshi… Tana k’ok’arin fita yayi mata wata mahaukaciyar fincika, ya janyo ta da k’arfin tsiya kafin ya cillata ta tafi ta fad’a kan dressing mirrow, ta bugu sosai dan hatta madubin sai da ya fashe, sannan ta buga cikinta a jikin tudun katakon da ake jeran kayan kwalliya…. Farfashewar da gilashin yayi ne ya sanya wasu suka ji mata ciwo a goshi da hannu, take jini ya b’alle ya fara zuba. Bai damu ba! Ya sake juyo da ita ya kifa mata wani marin da sai da ta kai k’asa, tana shirin tashi ya hau dukanta ba ji ba gani yana ball da ita! Cikin tsananin b’acin rai yana cewa “Yanzu kin shirya da su Hajiya ko? Wato kina da wajen zuwa kuma y’arki ta samu matsugunni shine har kike da bakin ce mini za ki bar gidana saboda rashin halacci ko? Ai daman na san using d’ina kawai kike yi tun ba yau ba, burinki a yanzu bai wucce in barki ki je ki auri Abba ba ko? To wallahi bari kiji ko mutuwa zan yi sai dai mu tafi tare ba dai in barki ki koma masa ba!!…” Yana hawaye yana maganganu kamar zararre yana jibgarta….. . Idan ana maganar dakuwa to Mama ta daku a hannunshi, tun tana salati tana neman d’ouki har k’arfinta ya k’are ta kasa furta komai. Ya fad’i gaskiya kam Tabbas! Dan ko ita da kanta a yanzu da ace zata kalli madubi to ba lallai ta iya gane kanta ba, ballantana kuma Abba. Karshema da Baba yaga abun bai yi mishi ba, katakon da take rataye jakankunan ta ya raruma ya maka mata a k’afa! Tun daga nan da tayi wata razananniyar k’ara bata sake motsawa ba! Fahimtar da yayi ta sume ne ya sanya shi sarara mata ya juya nufi gefen gadon yana layi ya zauna dab’ass!!! Ya dafe kanshi

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});