Chapter 90
Chapter 90
da kyar ta iya cewa “Ya Auwal Ina wuni” “Fine” kawai yace yana me wuce ta. Da sauri ta sha gabanshi kafin tace “Am dan Allah gida zaka je?” Maida hankalinshi yayi a wayar kafin yace “Eh” A hankali tace “Owk, d’an jirani plss Mammy ta bani sak’o wajen Mom ina so zan kai mata. Bara in d’auko vail d’ina”. Ba tare da ya kalletaba ya k’arasa kan d’ayan daga cikin kujerun parlourn ya zauna still yana danna wayarshi. Ta fahimci yaren kuramen nashi dan haka ta wuce sama da d’an sauri … Bayan 5 minutes ta sauk’o! Ta chanza kaya daga atamfar ankon dake jikinta ta d’aura bak’ar abaya tayi rolling, ta sanya lipstick da powder. Ta yi kyau kuwa ba laifi. Gabanshi tazo ta tsaya sannan tace “muje” Tun kafin sauk’owarta daman ya san ta taho sakamokon k’amshin turarenta da ya karad’e parlorn! Tana sauk’owa kuwa ya lura da ita amman sai ya kawar da kai… Wai me Aaima take nufi ne? Ya kasa gane kanta kwana biyun nan! Har magana take mishi ta WhatsApp yanzu. Yana tunawa lokacin da suke tare yasha gaya mata yana matuk’ar son yaga mace da black abaya tayi rolling abun yana burgeshi shiyasa kusan duk lokacin da zasu fita tare takan yi irin wannan shigar kuma ta san baya son native cloth kwata kwata Inba riga da wando ba to abaya….. “Mu tafi, na shirya” Muryarta ta katse shi. Kallonta yake yi tun daga sama har k’asa! Hakan kuwa ba k’aramin dad’i yayi mata ba. A hankali taji yace “Ina sak’on??” Diriricewa tayi kafin da kyar tace “Yana cikin purse d’innan” Tayi maganar tana nuna mishi purse d’inta wadda ta saka iya wayarta da lipstick a ciki. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya mik’e yayi gaba…. Shi fa har ga Allah kunyar ta yake ji a halin yanzu..idan ya tuna irin yanda ya fito mata k’iri k’iri ya fad’a mata abunda yake buk’ata daga gareta da kuma yanda ya furta mata kalmar ‘ba ya k’aunarta’ Wasu abubuwan da yawa da ya yiyyi idan yana tunasu a yanzu sai ya dinga ji kamar k’asa ta tsage ya shiga! Tabbas Daddy yayi gaskiya daman ya tab’a gaya mishi ‘’’Akwai ranar dana sani!Ranar da zaka ji inama ana yin reverse ayi maka domin ka samu ka aikata alkhairi ka kuma goge duk wani abun da kayi marar kyau. Ranar tana nan zuwa, ko bayan raina za kace na fad’a maka‘’. Tabbas kuwa tun kafin aje ko Ina gashi ranar ta zo Ya san dalilin da ya sanya Sakina take gudunshi ta kuma k’i sa! Bai wuce akan tunanin da take yi na alak’ar shi da cikin jikin Jalila ba ne…..bai san wanne kalar kallo zata yi masa ba idan taji tabbas cikin nasa ne! Ballantana kuma azo kan maganar halayyarshi da baya fatan Allah yasa Sakina ta sani! So yake ya gyara komai ya zama mutumin da ta ambata tana son kasancewa tare da! Gashi already yana da competition, yanzu ahaka ma ta riga ta nuna mishi ta zab’i Ashraff a kansa ina kuma ga idan taji wata magana akanshi! Ya kenan?…., “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Itace kalmar da ya ambata yana mai dafa motar shi dan har sun iso bakin motar. Da sauri Aaima tace “Subahanallah Ya Auwal mai ya faru?” Tana mai matsowa inda yake. Sai da ya d’an runtse idanunsa kafin ya dawo dai dai tukunna ya samu yace mata “Ba komai, shiga mu tafi” Yana mai zagayawa ya bud’e mazaunin driver ya zauna. Tana shigowa ya tada motar yaja suka fita. Har suka isa mansion d’in nasu babu wanda ya samu damar furta kalmar ‘a’ a cikin su. Shi ya fara fita daga nan itama ta fito suka nufi ciki. Suna shiga parlourn suka tarar da Jalila ta d’aura k’afa d’aya kan d’aya ga remote a hannunta tana ta chanja channel… Lumshe idanuwanshi yayi a hankali ya shak’i iska ya furzar sannan ya bud’e idanuwan nashi a hankali a fili yace “My worst regret!!” Ya kasa gaba ya kasa baya. Aaima ce tayi k’arfin halin k’arasawa tsakiyar parlourn inda Jalilan take tana kallon ta da d’an mamaki dan kamar bata tab’a ganinta ba. Fitowar Mom daga kitchen ne ya katse mata tunani har shi Auwal d’in Uwa mai dad’i suna had’a ido yaji wani sanyi a ranshi… Takawa yayi har inda take yana zuwa ya sa hannu yayi hugging d’inta..... Tun a cell Mom take aiyyana kalar abubuwan da zata yiwa Auwal kala kala In Allah ya maidota gida lafiya dukda kuwa tana shakkarshi, babu yadda bata yi mishi shi da Arshaad akan su basu kud’i su samu su fito ba amman suka hana su saboda suna shakkar Granpa sannan basu san darajar su uba and sun rainasu! Sannan ta dawo amman tun jiya take zuba ido but bataga k’eyarsa ba. A hankali yace “welcome home“ Ta manta rabon da Auwal ya nuna wani affection a kanta irin haka, ba ta san lokacin da wata kwalla ta zubo mata ba, a hankali tasa hannu ta share tana jin duk wata wutar masifar da ta shirya juye mishi tana sauk’a daga k’irjinta. Muryar Jalila ce ta katsesu jin da d’an k’arfi tace “Adama ina shayin nawa??” Da mamaki Aaiima take kallonta sai kuma ta juya tana kallon su Mom. Da sauri Auwal ya cika Mom ya yunk’ura zai yi wajen yaji ta rik’e mishi hannu yana juyowa ta girgiza mishi kai daga nan ta koma kitchen ta d’auko tea d’in daman ta gama had’awa waya take so tayi shiyasa ta manta ta fito d’aukar wayar. Zata nufi wajen Jalilan amma ga mamakinta sai taga Auwal ya tare, yace “Ba zata kaiwa Jalilan ba wallahi!. Idan tana son sha to tazo ta d’auka anan d’in!” Ya fad’a hakan yana mai karb’ar tea d’in ya d’aura akan dining sannan yaja hannun Mom d’in za suyi sama. Da kyar mamakin Auwal ya barta ta iya ce mishi “Ban ci abinci ba, Bara in na gama sai muyi saman dukkanmu ko?” Ajiyar zuciya ya sauk’e ya watsawa Jalilan wata uwar hararar da sai da y’an hanjin cikinta suka kad’a! Daga nan ya cika hannun Mom d’in ya wuce sama. Tabbas Jalila ta d’an sha jinin jikinta kuma it’s like kamar akwai abunda yake damunshi sannan tanada buk’atar kud’i daga hannunshi da kuma alfarmar ya barta ta je wajen Umma dan she can’t afford to loose Arshaad, duk da kuwa Umman tace mata akwai nasara amman tana son zuwa yau ta bita ta je da k’afafuwanta, shiyasa ta barshi kuma bata sake yiwa Mom wani yunk’uri ba ta hak’ura kawai ta barshi akan idan ya d’an huce kamar nan da 20 minutes haka zata kirashi ta zayyane mishi buk’atun ta. Hira sosai Mom da Aaima suke yi, Jalila kuwa tana gefe tanata hura hanci. Chan Mom ta cewa Aaiman tazo suje suci abinci. Haka suka mik’e suka isa dining d’in sukai lunch d’insu cikin kwanciyar hankali. Sai a sannan Aaima take tambayar Mom wacece jalila? Murmushi kawai Mom d’in tayi sannan tace mata “no one” kawai, daga nan tace “Ta mik’e ta je ta jirata a parlourn sama. Hakan kuwa akayi, Mom na ganin wucewar Aaima ta mik’e itama tayi kitchen….. Dama tun d’azu ta sallami cooks da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96