Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 29

Chapter 29

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta sauk’e sannan tace “bani minti talatin, inje inyi wanka, Ina dawowa za kiji komai in shaa Allah.” Kamar yadda Gwaggo Asabe tace Sai da tayi wanka ta dawo ta zauna sannan ta fara bata labari………… Asalin sunan Mommy, Aisha ana kiranta da Humaira, k’anwarta d’ayar duniya Khadijah wadda ake kira da Asabe. Aisha da Asabe sun taso cikin yanayin k’unci na rayuwa ata dalilin babu.. Yahaya ya had’u da Aisha ne lokacin da ya kai ziyara Taraba, jalingo a wani d’an k’aramin k’auye. Ata dalilin, masallaci da makarantun addinin daya d’auki nauyin ginawa. A rafii yana zagaye ita kuma taje d’ebo ruwa suka had’u. Tunda ya kyalla ido ya ganta ya rikice, a lokacin Mahaifiyarsu ta rasu Mahaifinta kawai ya rage musu. Tun Aisha tana kauce mishi har itama ta fara kulashi sama sama. Tashi d’aya ba kwana kwana ya nuna mata yana k’aunarta kuma yana son aurenta, Bata bashi amsa ba tace “yaje ya samu Mahaifinta”. Yahaya bai yi wani jinkiriba yaje ya samu Mahaifinta da maganar sannan yayi mishi alk’awarin ‘bayan auren zai barta tayi karatu har sai tace bataso’, dan ya lura burin Mahaifin nasu kenan. D’an guntun bincike akayi akan Yahaya, a lokacin, daga nan Mahaifinta ya bashi aurenta yace masa “duk lokacin daya shirya yazo da iyayenshi a d’aura” To fa!! anan ake yinta, dan k’iri k’iri Granpa ya nuna k’iyayyar shi muraran akan Aisha da inda ta fito, acewarshi “sam ba a jin auren d’ansa bace ita d’in!!!”. Buwayar Ubangiji, rabon Aslam, da soyayyar Granpa a matarshi ne suka tabbatar da auren Yahaya da Aisha wanda aka d’aura a k’auyen Jalingo ba tare da halartar Granpa ba. Tabbas anyi rigima ba k’arama ba, kafin, da kuma bayan auren!. Zan iya cewa ban taba ganin macen da ta sha wahala a hannun suruki kamar Aisha ba! Sauk’in ta d’aya Gramma tana mugun sonta ba kad’an ba, dan tun lokacin da Yahaya yaje mata da labarin Aisha farat d’aya taji Yarinyar ta kwanta mata, ita ta dinga lallab’a Granpa har aka yi auren. To bayan auren ma haka tayi ta fama, in tak’aice miki labari hankalin Granpa bai kwanta da Aisha ba har sai da ya aurawa Yahaya ajin nashi da yake ik’irari! Wanda ranar d’aurin auren ana d’aurawa Yahaya yana hawaye kamar k’aramin Yaro, dan zan iya cewa ban tab’a ganin Mijin da yake matuk’ar so da gudun b’acin ran matarshiba kamar Yahaya ba. Sauk’i d’aya da Aisha ta samu a gurin Granpa shine haihuwar Aslam da tayi, zan iya ce miki ko y’ay’an da Granpa ya haifa a cikinshi bayayi musu kalar son da yake yiwa Aslam, ko dan ya kasance jikansa na farko ne? Allah kad’ai ya sani. Tun ranar da aka haifeshi da ya d’auke shi aka tabbatar da hakan, domin kuwa kalar farin cikin da yayi kowa sai da ya gani ya tabbatar da ‘Granpa na cikin farin ciki’!. Zakkah da sadakar da ya bayar kuwa bana jin har yau a tarihin kaf garin Kano an tab’a bada irinta. Aslam ya taso cikin gata, duk wani abu da kika sani Granpa ne yake yi mishi… A tunanin kowa, Granpa zai kasance irin kakannin nan masu shagwab’a jikokinsa ne, sai dai kuma shekarar Aslam biyar a duniya aka haifi Arshaad amman kwata kwata Granpa bai yi wani murna sosai ba ma balle aje ga maganar shagali da jan shi a jiki kamar yadda kowa ya d’auka… Tun ranar da aka haifeshi da ya d’auke shi bai k’ara d’aukar sa ba, Aslam kuwa kullum suna tare, hatta abinci tare suke ci, takanas ya nemo wani bature yake yi mishi lesson a gida, da yamma kuma wani balarabe ne yake koyar da shi addini! Sai da Granpa ya fahimci loneliness da rashin wasa da Yara agemate d’in Aslam d’in kan iya jawo mishi wani ci baya a rayuwarshi tukunna ya nemi makarantar da tafi ko wacce tsada a kaf Nigeria ya turashi a Abuja wajen mahaifinshi, tare da kwakkwaran warning a me makarantar na “kar a tab’a mishi jika ko me kuwa zaiyi! Kuma kar a bari aci zalinshi.” Duk da yana da wayo sosai dan, a lokacin shekararshi tara Arshaad hud’u Auwal kuma uku wanda shima Granpa bai wani nuna farinciki ko tunanin janshi a jiki ba tun sanda aka haifeshi. A lokacin ne kuma Yahaya ya sake tadawa Granpa maganar yana so ya tafi da Aisha Abuja , daman ya tab’a nunawa Granpa son yin hakan amman fur k’iri k’iri Granpa ya nuna mishi sai dai ya tafi da Mammy saboda itace tayi karatu bayan k’iri k’iri babu irin artabun da baayi da shi ba amman fur haka ya hana Aishan yin karatu acewarsa ‘irin su In suka yi karatu gagarar mutum suke yi!’. A lokacin ya nace akan sai dai ya tafi da Mammy ita zata iya zaman Abuja wata k’ilan ma ta d’an dinga taimaka mishi ta fannin aiki, shi kuma Yahaya yace ‘ba zai tafi da ita ba! Ko da ace Aisha bata kasance uwargidanshi ba tou tabbas da ita zai tafi’….. Mistake d’aya wanda Yahaya yayi kuma yake kan yi har yanzu shine ‘k’iri k’iri yake nuna fifici a tsakanin matanshi’ (k’iri k’iri yake nunawa kowa ba tare da shakkar wani abu ba ‘ya fi son Aisha a kan Mammy’. Da kyar a wannan lokacin dan sai dai Gramma ta shiga tsakani tukunna case ya mutu, dan daa Granpa cewa yayi sai ya tafi da Mammy dole! Shi kuma yak’i. Tou kuma da Aslam ya koma chan ma da ya sake yin maganar Aisha ta bishi, still magana d’aya irinta farko shima Granpa ya maimaita mishi ‘sai dai ya tafi da Mammy’ shi kuma yak’i, Shiyasa har yau shi kad’ai yake zaune a Abuja, yanzu haka shi da Aaima ne kawai a gidan. K’in tafiya da Mammy da Yahaya yayi ata dalilin Aisha yasa Granpa ya rufe ido ya dinga keta mata ruwan rashin mutunci kala kala, ga Adama da Ummi suma basu barta ba, Mammyn ce ma ita bata shiri da ita kuma bata fad’a da ita. A lokacin ne kuma Mahaifinta ya rasu, Allah yaso ni nayi aure don da ban san ya zan yi ba saboda shi kanshi Mahaifin namu su uku aka haifa biyun duk sun rasu, Mahaifiyar mu kuma daga gidan marayu ma aka aurota, balle inyi tunanin zuwa gidan y’an uwa! Dan a lokacin halin da Aisha take ciki a gidannan, ko mage bata isa ta d’auko tace zata rik’e ba. Aslam shekara biyu kawai ya iya yi a Abuja ya d’agawa kowa hankali Akan shi fa ‘Mahaifiyarshi yake buk’ata’ Dan ba kad’an ba suna mugun k’aunar juna, kuma yana da k’ulafucin uwa ba kad’an ba, itama kuma haka, komai Aslam, shima komai Mommy. Saboda tsabar tsananin shak’uwar dake a tsakaninsu yasa har kusan zarewa tayi lokacin da aka kaishi Abuja, Idan nace zan tsaya fasalta miki kalar soyayyar da sukewa junansu sai mu kai jibi anan.......... Ba yadda Granpa ya iya haka ya tarkatoshi ya dawo dashi kano gurin Mahaifiyarshi, akan dai ya bari a tafi da ita d’in. Sai dai kuma daya dawo d’in abun bai yi dad’i ba sam! Dan k’iri k’iri Granpa ya dinga nuna banbanci k’arara ba tare da shakkar komai ba! Abun mamaki hatta driver

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});