Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 43

Chapter 43

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shaa Allah” yace sannan suka k’arasa….. Nan d’in ma abinci wajen kala hud’u akayi. Cikin nutsuwa da nishad’i sukayi serving kansu suka fara having breakfast d’in. Basu dad’e da fara cin abincin ba, Hudan taji yanayin bugun zuciyarta ya chanza! A hankali ta runtse idanunta tana k’ok’arin saita kanta, da kyar ta samu ta bud’e idanunta tana mai jin wata nutsuwa tana sauk’ar mata sakamokon k’amshin turaren da ya sakarmata da kasala lokaci guda! Basuma lura da shigowar tasa ba, sai da ya matsosu sosai da k’amshin turarenshi ya yi musu sallama, tukunna suka lura da shi. A hankali yace “AsSalama alaikom” “Wa’alaikassalam, d’an albarka!” Daddy yace yana mai ja mishi kujerar kusa dashi. Zama yayi, a lokaci guda kuma yana mai amsa gaisuwar su Shuraim sannan yace Daddy Ina kwana” Da kulawa Daddy ya amsa haka shima Abba bayan ya gaidashi. Sannan ya juya ya mik’awa Auwal hannu, sukayi musabaha. A hankali Hudan ta gaidashi ba tare da ta yarda sun had’a ido ba! Juyowa yayi ya kalli inda take, sai kuma da sauri ya kauda kanshi, a hankali yace “lafiya” Hira suka d’an fara sama sama, kusan rabin hirar akan maganan company d’in da Aslam da Abba za su bud’e ne. Ita dai Hudan kasa ci gaba da cin abincinta tayi, tun lokacin daya shigo! Bata san daliliba amma in dai yana waje to sai ta dinga jin kanta uncomfortable, ga yadda k’irjinta yake yi mata shima, wanda ta rasa dalili. Abba ne ya cewa Aslam “Ina Arshaad ne? Ban ganku tare ba.” “Ya tafi d’aurin auren wani Abokin su, and wai za su kai amarya Kaduna, around 2 haka.” Aslam d’in ya bashi amsa. “Ok” Abba yace kafin ya kalli Huda yace “Ko a bari sai gobe kuje park d’in ko? Tunda yau Arshaad d’in yana busy.” Kafin ya rufe bakin shi Auwal yace “Bani da aiki sosai yau, zan kaisu.” Hudan ta d’anji sauk’i saboda daman ba zata so su fita itada Arshaad ba, kuma ba zata so ace Aslam ya kaita ba! Amman kuma ba ita kad’ai ba hatta su Daddy sai da suka fahimci akwai wani abun da Auwal ya shirya duba da yadda baya son ta yanzu kuma lokaci guda yace ‘Zai kai ta’ Daddy wanda ya san halin kayanshine yace “a’a! Ka barshi goben Arshaad d’in ya kaisu” “Daddy i volunteered fa.” Auwal d’in ya fad’a yana kallonshi. Cikin d’an fad’a Daddyn yace “And i insist akan ka barshi Arshaad ya kaisu.” Murmushi Abba yayi kafin yace “Daddy tunda ya nuna zai kaisun a barshi mana ko? Please.” Baya son jan magana dan haka yace “ok” kawai ….dukda ya san Auwal bai Isa yayi mata komai ba tunda tare za su tafi ita da su Shuraim amma baya so suje Auwal d’in yayi mata wani kalar rashin mutuncin da zai ja yaji kunya ne. Murmushi Auwal d’in yayi ya kalli Hudan kafin yace “Ki shirya around 2:30pm haka” Yana gama fad’an haka ya mik’e yayi hanyar sama, da alama ma ko “to” d’in data ce mishi bai ji ba. Shuraim ne ya mik’e, yace “Abba zanje in yi assignment d’ina kafin mu fita” Da sauri itama ta mik’e daman hanya take nema saboda sam bata k’aunar zamanta waje d’aya da Aslam kwata kwata, gashi ta lura sai faman kallonta yake tayi, sannan anyi rashin sa a ya zauna a kujerar da take opposite d’in tata ne….a hankali cikin nutsuwarta tace “Abba nima bara inje” sannan ta juya ta yiwa Daddy sai anjima. Sudais shima binsu yayi, suka fice a tare…. Da murmushi Abban ya bisu da kallo yana jin wani tsananin farin ciki a ranshi.. Gyaran muryar da Daddy yayi ne ya juyo da hankalin su inda yake. Ganin yanayin shi yasa duk suka maida hankulansu a kanshi. Cikin rauni yace “Abba jiya da daddare naje wajen su Mammy, and thier situation is bad! Very bad!! Na san abunda suka yi was wrong but anyi saurin yanke hukunci cikin fushi gaskiya.. Thou they deserve it, but matsalan shine they can’t survive in there most especially ma Ummi, dan a yanzu inda zaka je ka kalla jikinta to ba zaka so ka k’ara kalloba sakamokon k’uraje da borin jinin da suka fito mata ta koina! Ka san dama ita tanada allergy tun tana y’ar k’arama tanada kyankyami sosai! Ko fa 1 week ba ai ba amman in kaje ba lalle ka iya gane ta ba! I don’t think zata iya kai 2 months a wajen nan gaskiya, jiya da naje ruwa ake k’ara mata, amai da gudawa take yi, gashi ko abinci mai kyau in mutum ya kai musu Granpa sai ya sab’a maka. Kar garin punishing d’insu kuma muje mu shiga hakkinsu, after all they are our wives..” Ajiyar zuciya Abba ya sauk’e kafin yace “Daddy inda case d’innan a hannu na yake, tou da zan iya sassauta musu, not because of wai na yafe musu ko na huce, NO! Only because of maganan da kayi min yanzun… Amman Granpa ke rik’e da case d’in, already ni da kai masu laifine a idanunsa a yanzu, Ina tunanin In muka yi interfering, za a iya samun matsala…” Cikin katseshi Daddy yace “Ba interfering za muyi ba! Gramma za muyi wa magana, na san ya san yanda za tayi ta d’an shawo kanshi, at least a d’an sassauta musu, ya bari a dinga kai mu su abinci daga nan, sannan a ajjiye su a tsaftataccen waje, dan gaskiya jikin Ummi ya bani tsoro jiya.” Numfashi Abba ya fesar, sannan yace “ba komai zan kira Gramma d’in a waya zuwa anjima in shaa Allah.” A hankali Aslam yayi k’asa da kanshi sannan yace. “Zan yiwa Granpa magana, in sha Allah zai sauk’o, zan lallab’ashi.” Shiruu, suka d’an yi, chan kuma Daddy yace “ok, hakan zai fi.” Abba yana shirin mik’ewa, Daddy yace “akwai wata maganar still fa. Jiya bayan mun rabu Arshaad ya kirani, wai yana son yin magana dani, i think kunyar ka yake ji shiyasa ya bari sai da na koma.” Da mamaki Abba yace “Arshaad? Kunya ta kuma? Ikon Allah!” Murmushi Daddy yayi, sannan yace “Bayan yace ‘yana son magana dani’ shine nace masa ‘ya zo tou muyi face to face’ Mun dad’e tare dan tare ma muka je station d’in da shi.” D’an kallonshi Abban yayi sosai ya bashi dukkanin hankalinsa alamun yana buk’atar k’arin bayani… Murmushi Daddy ya sake yi, kana ganinshi ka san yana cikin farin ciki da jin dad’in al’amarin, fuskarsa cike da annashuwa yace “Good news ne, Ashe wai ya san Huda, for the past 3 years, and suna dating ne, ita ce Yarinyar da muke da shirin zuwa nema masa aurenta! So yanzu ya same ni ne akan ko za a fara maganar tasu tund........” Kwarewar da Aslam yayi ne ya hanashi k’arasawa. Da sauri Abba ya mik’a mishi ruwa dan haka ya karb’a ya d’an kurb’a yana tarin kad’an kad’an still, su kuma sunata jera mishi “sannu!” D’aga kanshi kawai ya iya yi Idanunsa sun yi jaaaa! Alamun ba kad’an ba yaji azabar kwarewar… Sai da suka ga ya d’an nutsu tukunna Daddy ya kalli Abba yace “ya ake ciki?” Shiruu, Abba yayi, kamar mai nazari, kafin yace “all those years kuma bai gane ta

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});