Chapter 80
Chapter 80
remind her!. Sannan ya san ta inda zai b’ullo mata ta yarda dan yaga alamun ba lalle ta yarda cikin sauk’i ba gashi babu enough time!…. Ya jima a wajen kafin ya juya ya wuce sama da niyyar d’an bata time Kafin ya sake ganinta! Yana da full hope d’in zai yi nasara bi izinillahi. Mammy na sauk’a k’asan ta fara shan mamaki.. Kulolin abinci kala kala da su drinks ake ta shigowa da su! Bata ida fita daga wannan mamakin ba taga friends d’inta da sisters d’inta har da Mahaifiyarta suna ta shigowa har da ankon super d’in su da suka yi a jikinsu…. Da sauri ta k’arasa kusa da yayarta ta kamota tace “Me kenan? Wats the big idea?” Murmushi Haj Binta tayi kafin tace “Wunin d’an mu za muyi mana! Anjima kad’an kuma muje muga Amarya naji Dad yace za suyi traditional day d’insu suma daga nan mu bata kyaututtuka Naga ke baki son zancen shiyasa ma na zagayeki na kira Dad. Anko kuwa ni na fitar kuma gashi kowa yayi, ni da su Hajiya ( Mahaifiyar su) tun lokacin da aka sa rana dama muke ta shirye shiryen mu. Matsowa Mahaifiyar tasu tayi kusa da su ( ita da sister d’in tata ) kafin itama ta fara magana “Ki nutsu ki bari ayi komai a gama daga nan sai a san abun yi! Ni na hanasu su fad’a miki komai akan lamarin auren, gudun samun matsala dan na san halinki. In dai ni na haifeki to inaso ki kwantar da hankalinki kiyi hak’uri, ni kaina ba wai son had’in nake yi ba! Amman ki bar ni da su kawai ai in sun san wata basu san wata ba! Kuma kar ki bari kowa ya fahimci halin da ake ciki, ki nuna kina so inda hali ma ki shirya muje ki bawa ita Yarinyar kyauta da hannunki a gaban kowa…” Ganin friends d’in Mammyn sun tunkarosu ne yasa Mahaifiyar tata yin shiru ta fara yak’e.. Suna zuwa kuwa suka hau tayata murna kowa na farin ciki tare da yi mata ya jiki (dan ce musu aka yi ita da su Mom duk sun yi inhealing dangerous abu shine aka fitar da su k’asar waje suka yi jinya sai jiya suka dawo). Haka nan suka k’arasa tsakar falon aka zazzauna… Masu decoration suka shigo suka hau d’an gyaggyara parlourn Yayar tata ce tace “bara taje ta ajjiye abu daga nan ta cewa Arshaad ya shirya, su d’anyi hotuna a nan kafin a tafi event d’in su Hudan..” Sama ta nufa da niyyar ajjiye abu tukun ta je ta kira Arshaad d’in Tana shirin hawa suka had’u da Dad yana sauk’owa… Cikin mutunta juna da barkwanci suka gaisa daga nan yace mata “Ta kirawo masa Mammy, su sameshi su biyu a side d’in Arshaad.” Mammy na zaune a cikin friends da y’an uwanta amman kwata kwata hankalinta baya a garesu! K’ok’ari take taga ta tirsasa zuciyarta ta aminta da abinda Mamanta tace mata yanzun, amman furr ta kasa... A wannan yanayin sister d’in nata tazo ta rad’a mata sak’on Dad a kunne daga nan ta wuce ta nufi parlourn Arshaad. Da kyar Mammy ta iya mik’ewa tabi bayan ta.. Sauk’owar Arshaad kenan yaga sun nufi side d’inshi, A ranshi yace “perfect” Duk fa bai san me za suyi anan d’in ba. K’arasawa yayi ya gaggaisa da bak’in, kakarshi tana ta tsokanarshi, daga nan ya wuce shima. A parlourn suka tarar da Dad yanata faman kai kawo.. Suna shigowa ba tare da b’ata lokaci ba yace “Binta, ga y’ar uwarki nan, ki tayani tambayarta.. Akwai abunda suke b’oye min ita da Arshaad wanda ban sani ba! Na san halinta da sanabe kala kala dan haka idan akwai wani abun gara tun farko ta fito ta fad’a kar taje ta yiwa mutane shirme!..” Hajiya Binta tana shirin yin magana Mammy tayi caraf ta amshe ta fara magana “Ai kai da kanka yanzu me kace? Muna b’oye maka, ko? To kuwa ai kaga tunda muka b’oye maka d’in to bai shafeka ba kenan! Infact babu abunda ma ya shafeka na daga rayuwar ni da y’ay’ana. Da kace kana kirana i thought welcoming d’ina zaka yi” Murmushin takaici tayi kafin ta juya ga Hajiya Binta tace mata “Ko kin san tun jiya dana dawo ban ga k’eyar bawan Allah n nan a kusa da ni ba balle ya tambayeni lafiyata ko ya nake? Ai ko ni kad’ai na aikata laifin b’oye y’ar gold d’inku wallahi ban chanchanci haka daga gareka ba ko dan darajar Arshaad da Aaima!” Ta fad’i haka tana takawa inda yake, daga nan taci gaba “Sannan yanzu ka wani kwaso k’afa kazo kana wani waye waye… Kai har kana da kunyar yi min wannan maganar? Bayan abunda ka yi? To bari kaji bai shafe ka ba! Ka zuba ido zaka gani tare da kowa idan Allah ya kaimu gobe.” Tana gama fad’in haka ta juya ta nufi hanyar fita. “Idan kika taka k’afarki kika bar min parlourn nan ba tare da kin fad’a min abunda nake son ji ba to a bakin auran ki.” Ba mammy ba hatta Hajiya Binta sai da gabanta ya yanke ya fad’i. Juyowa tayi tana kallonshi da idanuwanta da suka fara chanja launi, cikin tsananin takaici tace “Namiji k’anin ajali! Ai Aisha ta dawo dole ka yi min haka. To bari kaji in gaya maka wallah ko ka sakeni babu inda zanje sai dai in kai ka fita ka bar mana gidan nan ni da y’ay’ana!” Cikin katseta yace “Rukayya kar ki yi underestimating d’ina! Dan wallahi zan yi miki abunda ko me sunana aka kira sai kin ji kin tsani wanda ya kira sunan! Baki san a ya’ya nake ganin ki ba a halin yanzu, kar ki kaini bango! Wallahi ba dan darajar Aaiima da Arshaad ba da tuni na dad’e da sauya miki rayuwa.. Bana son dogon magana dan bana jin iya zama mai tsawo a inuwa d’aya da ke! Ki fad’amin abunda nake son ji in fita.” Ya fad’i haka cikin kakkausar muryar da take baiyyana tsanannin b’acin ran da yake ciki. Haj Binta ce tace “Kayi hak’uri dan Allah, Mammy ke kuma ba a haka! Ki bari wannan matsalarku ce daga baya za ku yi settling ke da shi Yanzu ki fad’i abunda yake son ji tunda ya nuna yana da buk’atar hakan” Cikin tsananin b’acin rai Mammy tace “Ba zan fad’a ba! Wallahi ba zan fad’a ba” Sannan ta juya gareshi tace “In kana buk’atar ji Yahaya ka zo ka shak’eni sai in fad’i maka ta k’arfin tsiya!! Da kake wani maganar sauya mini rayuwa, na nawa kuma? Bayan azabtar da mu d’in da ku kayi me ye kuma kuke tunanin za ku yi kuma wanda yafi wannan??. Ba dai rashin sanin ya kamata ka d’aurawa kanka ba, rana d’aya? To wallahi dede nake da k’ugunka! Maganace nace ba zan fad’a ba In kuma ka matsu to kazo ka shak’eni In fad’eta.” Cikin tsannnin fushi ya tunkarota kamar wanda zai rufe ta da duka! Dasauri Arshaad wanda shigowar shi kenan yanzun ya shiga gaban Mammy ya tsaya Hajiya Binta kuma taci gaba ta k’ok’arin hana Dad d’in k’arasawa inda Mammyn take! Dukkannin k’arfin da Allah yayi mata tayi amfani dashi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96