Chapter 49
Chapter 49
dan na sanki da taurin kai! Kar kije an kashe case but still kina zarginshi so just ki barshi su zo d’in.” A hankali tace “komai ya wuce, ki cire hijabin please haba mana”!Ta k’arashe maganar kamar zatayi kuka. Sai yanzu Sakina tayi murmushi kafin tace “Shikenan na faasa tafiya amman ki barsu kawai suzo d’in ayi a gama” D’aga mata kai Hudan tayi. A hankali Sakina ta koma ta zauna akan gado, bayan ta cire hijabin. Da kad’an kad’an Hudan ta dinga janta da hira har ta samu ta sake ta daina fushin.. Nan take bata labarin Ya Junaidu, amman the good news is that DNA d’in su Baba bai yi matching da gawarwakin ba Both wanda akayi a Lagos da wanda suka taho da sample d’in nan Kano aka yi. Hawaye Hudan ta share kafin tace Yanzu Ya Junaidu ya b’ata kenan?” A hankali Sakina tace “Mu yita addua kawai Allah ya baiyyana shi” “Ameen” tace. Ba abunyi dan haka daga kallo sai chatting da hira.. Yau su biyu tol suka yi lunch, su Shuraim suna school Abba kuma ya d’an fita wasu ayyuka, Arshaad bai lek’o ba Aslam ma haka. Sai bayan Magrib Arshaad ya kira Sakina yace mata “suna k’asa shi da Jalila, su sauk’o!”. Jalila tunda take bata tab’a jin farin ciki irin wannan ba!……. D’azun tana d’aki Gwaggo Asabe tazo tace mata “taje, inji Arshaad, yana kiran ta.” Kasa b’oye farin cikin ta tayi a gaban Gwaggwo Asaben har da su fesa turare da shafa jambaki, daman already idanunta da kwalli fuskarta kuma da powder! Ita dai Gwaggo Asabe tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, Allah yasa dai ba wannan Yarinyar Arshaad zai kwaso musu ba, ita tunda tazo gidan gaisuwa bata tab’a had’asu ba, gashi bata son aiki, hatta d’akin da take ciki sai dai tazo ta kira aje a gyara mata. Doguwar riga y’ar kanti mai kyau ce a jikinta, dan haka ta d’auko d’an k’aramin mayafi tayi d’auri sannan ta d’auko wani ta yafa shima d’an mitsitsi daga nan ta d’au wayarta tazo ta wuce ta fita ta bar Gwaggo Asabe da baki a sake. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauk’e, kafin ta lek’a da d’an k’arfi tace mata “yana chaan waje a bakin mota” Don har tayi nisa. “Ok” Kawai Jalila tace tayi gaba abunta. A bakin motarshi ta ganshi a tsaye. Bai yi wani kwalliya ba hasalima Jallabiya ce a jikinshi bak’a amman sai da numfashin Jalila ya kusan d’aukewa dan yayi mugun tafiya da imaninta! A k’asan ranta tace “Ma shaa Allah” Tanajin tsananin tsantsar k’aunarsa tana sake ratsa dukkannin ilahirin jikinta, itafa ko da ace Arshaad zai dinga yi mata dukan tsiya kullum! Muddin zai yarda ya aure ta su zama k’ark’ashin inuwa d’aya, ta na amsa sunan matarshi to wallahi zata iya zama da shi!. Tsabar kallon da take yi mishi har tuntub’e tayi ta kusan fad’uwa wanda hakan ne ya janyo hankalinshi gareta dan shi bai ma san ta fito ba!. Suna had’a ido ya tamke fuskar shi kamar bai tab’a dariya ba. A take taji gabanta ya fad’i amma sai ta dake ta k’arasa inda yake still tanata satan kallonshi…. Sai da ta d’an risssina tukunna tace mishi “Ina wuni” cikin wani kalan yauk’i da kissa. Sake had’e rai yayi, ya bud’e mata murfin motar tukun yace “lafiya, shiga mu je!” A take tsoro ya rufeta, D’an bata san mai ya shirya mata ba Tana shiga, ya rufe ya zagayo ya zauna mazaunin drivern. Sai da taji tashin motar tukun ta bud’e idanunta dan tun lokacin da ya rufe mata motar ta wani lumshe ido tana murmushi saboda ba k’aramin dad’i taji ba. D’an juyowa tayi ta kalleshi fuskar shi yanda kasan wanda bai tab’a dariya ba! A hankali ta zaro wayarta ta turawa Auwal message saboda gaskiya in dai daga ita sai Arshaad ne a waje tou za a iya samun matsala dan tabbas tsaf! Zata Fallasa komai kuma ta san Auwal uban ta zai ci idan tayi hakan. Suna parking a cikin gidan dai dai message d’in Auwal ya shigo wayarta… Sai da su Hudan suka sauk’o tukun ta fahimci inda suka zo dan haka tayi mishi reply ta ajjiye wayar. Tunda ta sauk’o take maka mata harara!! A kujerun tsakiyar parlourn suke dan haka suma suka nufi wajen suka zauna. A hankali suka gaidashi ya amsa Sannan Huda ta kalli Jalilan tace “Ya Jalila ina wuni” Wani uban tsaki Sakina taja ta d’auke kai. “Hmm” Kawai Jalilan tace, wallahi ba don Arshaad yana wajen ba da sai ta tashi ta bugewa Sakina baki, dama a k’ule take dan ita kad’ai ta san tashin hankalin data shiga tun saukowarsu….. Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta kalli Hudan tace “lafiya” Kawai! Amman a k’asan zuciyarta ji take yi kamar ta mutu dan tsananin bak’in ciki! Wani irin tuk’uk’i ne yake taso mata saboda abunda idanunta suka yanzu nan ne gidan Mahaifin Huda?? Ba abunda yafi d’aga mata hankali daman tuntuni irin labarin da taji Gwaggo Asabe tanayi da wata mai aiki dattijuwa akan ‘Mahaifin nata ya bar gidan saboda Babansa yace ya zab’a ko shi ko ita!!’ Ita a tunaninta bashi da wani kud’i sosai dan tama d’auka gidan haya suka je suka kama suna zaune Ashe shima mugun mai kud’i ne. Ta tabbata Hudan y’ar masu kud’i ce kenan yanzu? Kuma Babanta yana matuk’ar sonta! Muryan Arshaad ce ta katse mata tunani jin yana cewa “Jalila ga Al Qurani, izu sittin.” yayi maganar yana nuna mata kan center table kafin yaci gaba “Idan baki da alwalla kije kiyi kizo yanzu! Zan rantse akan ‘cikin jikinki ba nawa bane ba! Sharri kika yi mini’ kema kuma zaki rantse akan ‘gaskiya kike fad’a (cikin nawa ne). Tsakanin ni da ke duk wanda yayi karya Al Qur’ani ya ci shi!.” Wata zazzafar zufa ce ta keto mata, tana shirin yin magana taji ance “Sannu Ya Sheik! Akaramakallahu.” Suka ji muryarshi yana takowa cikin parlour… Cikin gadara Auwal ya k’araso wajen, kafin one by one ya kalle su! Da kyar ya iya janye idanuwanshi daga kan Sakina! Sannan ya d’anyi murmushi yace “Ai ya kamata ni ma a gaiyyaceni meeting d’in ko?” Ya fad’i hakan yana mai neman kujera ya zauna kafin yace “Ya sheikh!! You were saying??” Banza Arshaad yayi da shi ya tashi ya matsa yana k’ok’arin d’aukar Qur’ani n Hudan tasa hannu ta d’auka a hankali tayi k’asa da kanta ta fara magana “Ya Arshaad dan Allah kayi hak’uri akan abunda nayi maka, na yarda da kai please ba sai ka rantse ba!” Wani farin ciki ne ya lullub’e Arshaad da Sakina a take. A hankali shima, yace “Thanks for trusting me Hudan, but i’ve to do this, please don’t stop me, okay?” Cikin katseshi tace “Nima please kar kayi haka, wallahi i trust you, in kuma kak’i yarda har kayi, to it means stilll baka hak’ura ba kenan da abunda nayi maka.” This time around murmushi yayi, kafin yace “Tou kawo, bani” Yayi maganan yana mik’a mata hannunshi Tana shirin yin magana, suka ji Auwal ya kwashe da dariya, cikin dariyar yace , “Yayi Romeo and Juliet!! Hey, look here” Yayi maganan referring to Hudan, kafin yace “Ki yarda da shi ko kar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96